Burodin pide na daga cikin abubuwan da Turkawa ke ci a lokacin buɗa-baki. / Hoto: TRT World

"Za ku iya samun burodin pide ba lallai sai a watan Ramadana ba," in ji Ercan Bayraktar.

Bayraktar shi ne mamallakin gidan burodin Bayraktar Firini da ke Beyoglu. "Sai dai pide ɗin da ake samu a watan Ramadana, na musamman ne, fulawar da ake amfani da ita ta fi kyau," in ji shi. "Fulawa ce ta alkama wadda ta fi jan ruwa. Tana ƙamshi daban idan ana gashi da ita."

Bayraktar ya ce ɗan ƙaramin gidan burodin nasu wanda ke a Balik Pazari (kasuwar kifi) ya shafe aƙalla shekara 100 a birnin Santambul. "Ba mu san yaushe ne takamaimai lokacin da aka kafa shi ba," kamar yadda ya bayyana.

Gidan burodin na Bayraktar Firini an kafa shi fiye da shekara 100

Rahmi Burman wanda ke aiki a wurin gasa burodi na Bayraktar ya bayyana cewa burodin na pide na mannewa idan ba su yi amfani da kwanson alkamar ba domin raba burodin da katakon da suke amfani da shi wurin ajiye burodin a cikin wurin gashin.

Izzet Boz wanda shi ma ma'aikaci ne ya ce ana sarrafa Ramadan pide a gidan sama a ƙarƙashin farar fitila mai haske a kan tiles farare inda ake rufe shi da fulawa. Ya taƙaita dalilin da ya sa burodin yake zama na musamman "Shifa [waraka]."

Aydin Ozleyen, wanda abokin sana'arsa ne ya bayyana cewa ya ce fulawar da ake amfani da ita tana da kyau sosai.

Nau'in fulawar da ake amfani da ita wurin yin burodin pide ta musamman ce.

Wata mai nazarin tarihin abinci Nazli Piskin ta tabbatar da cewa a birnin Santambul, an fi ganin pide a lokacin Ramadana, sai dai duk da haka ana ganinsa bayan watan. "Idan za mu kalli Anatolia, ana cin pide a kusan kullum."

"Pide wani nau'in burodi ne a shimfide. Mun ce masa burodi a shimfide saboda shi ma yana ɗauke da yeast," in ji ta.

"Ba ya kama da yufka [kwaɓin da ake yin borek da shi], wanda ba a saka masa yeast." Kamar yadda Piskin ta bayyana, ana gane ƙwarewar mai yin pide ne sakamakon shi ba a mulmula shi sai dai "ana kwantar da shi da hannu ne".

"Shi ya sa," Piskin ta ce, "ko wane mai gasa burodi da irin pide ɗinsa," Ta kuma bayyana cewa zafin da wurin gashin ko wane gidan burodi ke ɗauka ya bambanta, sai dai babban bambancin kawai shi ne shi kansa pide ɗin.

"Za a iya haɗa pide ba tare da ƙwai ba," kamar yadda Piskin ta bayyana. "Ba ina nufin haɗa shi da kwaɓin ba. Ina nufin shafa shi a saman pide ɗin bayan an kammala siffanta shi da hannu kafin a saka shi cikin wurin gashi."

Pide ɗin da aka gasa da ƙwai samansa ya fi zama ɗorowa da ruwan ƙasa, wanda kuma ba a gasa shi da ƙwai ba ya fi haske. "Babu wani batun ɗaya ya fi ɗaya," in ji Piskin. "Kawai ya danganta ne da abin da iyalai suke so."

Ana watsa riɗi a saman Ramadan pide ɗin sannan a saka shi a cikin wurin gashi.

Piskin ta bayyana cewa Evliya Celebi wanda matafiye ne na Daular Usmaniyya a ƙarni na 17 ya yi rubutu dangane da Ramadan pide.

"Ya yi rubutu game da al'adar Santambul ta Ramadan pide kuma ya bayyana cewa ana shafa ruwan saffron a saman wurin da ake gasa Ramadan pide."

Ta bayyana cewa saffron ɗin na bayar da ƙamshi mai daɗi ga Ramadan pide ɗin.

Dangane da abin da ake watsawa a saman pide ɗin, Evliya Celebi ya bayyana cewa masu gidajen burodi kan gaurayawa "poppy seeds" da kuma "anise seeds" sai a watsa a kan pide ɗin, ba kamar yadda yadda ake gauraya riɗi da cumin a yanzu ba. Piskin ta bayyana cewa babu tabbaci ko an yi amfani da riɗi da kuma "cuming seeds" ba a zamanin Evliya Celebi, sai dai bai ambace su ba.

Piskin ta ce akwai wata al'ada ta cin Ramadan pide. "Kamar yadda kuka sani, an fi son cin Ramadan pide da zafinsa idan an fito da shi daga wurin gashi," in ji ta. "A tsawon shekaru, iyalai kan tura ƙananan ƴayansu domin bin layi don su samu Ramadan pide mai zafi domin cin sa da ɗumi a lokacin buɗa-baki".

Kamar yadda Piskin ta bayyana, Ramadan pide na da muhimmanci sakamakon ƙamshin gashin na zagaye unguwa, da kuma yadda mutane ke taruwa a gaban gidan burodi kafin buɗa-baki domin ɗaukar pide ɗin a kai gida.

Piskin ta ce Ramadan pide na saurin bushewa. " Babu wanda ke son cin busashen pide," kamar yadda ta yi bayani. "Shi ya sa iyalai ke siyan wanda za su yi amfani da shi kaɗai, shi ya sa ba a samun kwantansa washe gari."

Ta shaida wa TRT World cewa ta tsani ganin burodi ya lalace, inda Piskin ta ce "Bari a ce akwai sauran Ramadan pide wanda ya rage. Za a iya turara shi a cikin tukunya mai tafasa." Ta kuma bayar da shawara kan cewa za a iya yanka shi ƙanana a gasa shi ya zama kamar cin-cin. " Za kuma a iya niƙa shi ya zama busashn garin burodi," kamar yadda ta bayyana.

Ta ce kowane gida suna da gidan burodin da suka fi so don siyan pide. “Misali, ni da mijina muna zuwa wani gidan burodin da minti goma ne daga gidanmu duk da cewa akwai wanda ya fi kusa da mu, wanda ba mu cika son shi ba," in ji ta.

TRT World