Zanen Olaniyi Omatayo yana yana fitar da abin da ake zanawa a yanayi na tuna baya da suke nuni da tarihi da al'adu. Hoto: OIaniyi Omotayo      

Daga Pauline Odhiambo

Da a ce tuna baya zai yi amfani wajen dawo da hannun agogo baya, to lallai da zane-zanen Olaniyi Omatayo sun taimaka wajen tuna bara. Olaniyi Yana fitar da zane-zane ne da suke fitowa tamkar wasu sofaffin hotuna.

Zanen Olaniyi Omatoyo yana fitar da abin da ake zanawa a yanayi na tuna baya da suke nuni da tarihi da al'adu.

"Na yanke shawarar amfani da wannan tsarin ne domin bayyana kyawawan al'adun Afirka," inji mai fasahar dan Najeriya a tattaunawarsa da TRT Afrika.

"A farkon lokacin da na fara zane, na kasance ina yin kowane irin zane, amma daga bisani sai na yanke shawarar fara zana abubuwa da za su dade suna ba da ma'ana sannan su kasance wakilan bakaken fata a duniya."

Mai fasahar wanda shi da kan shi ya koyar da kan shi fasahar zane-zanen, Olaniyi ko kuma 'Niyi' kamar yadda aka fi saninsa, ya kawo wasu sababbin salon a harkar domin bayyana fasaharsa.

Niyi's technique is textured and naturalistic. Photo: Niyi

Hada fasahohin 'Impastorealism’

"'Impastorealism' kalma ce da na hada domin bayyana yadda nake iya hada fasahar realms da impasto," inji matashin mai shekara 28, sannan ya kara da cewa, "ban karanci bangaren fasaha ba a makaranta, amma na samu kwarewa a harkar ce ta hanyar bincike a kafofin sadarwa, inda na koya abubuwa da dama da salon zane-zane masu yawa.

Impasto wani salo ne na zane da ake yi a jikin bango da yake fita tamkar fasahar 3D kamar yadda Artists & Illustration suka bayyana. A irin wannan salon zanen, bayan an kammala ana ganin alamar alburushimn fentin.

A fasahar realism kuwa, ana fitar da zane ne kamar asalin yadda yake a zahiri. Haka kuma ana amfani da kalmar wajen bayyana zanen da aka yi, amma suka fito kamar hotunan kati.

"Yanzu ina aiki ne a kan fitar da wasu zane-zanen da suka nuna muhimmancin hadin kai a tsakanin bakaken fata a duniya.

"Daya daga cikin abubuwan da nake aiki a kai shi ne zanen wasu mutane da suke kama da ’yan’uwa da suke tafiya a cikin jirgin ruwa zuwa wani wuri."

Fasahar karfin gwiwa

"Za a iya kallon zane-zanen da nake yi ta fuskoki da yawa, amma ni manufata ita ce in karfafa gwiwar mutane domin su san kansu sannan su fahimci abubuwan da za su iya yi," inji shi.

Zane-zanen Niyi suna nuna muhimmancin hadin kan mutane a kasashen Afirka. Hoto Niyi

Sai dai matashin mazaunin Legas ya sha fama da kalubale, duk da ya kasance yana dan rage zafi daga sayar da wasu daga cikin aikace-aikacensa.

"Wasu lokutan nakan samu kasuwa sosai, amma wasu lokutan kuma kasuwar takan ja baya," inji Niyi.

"Amma rashin kasuwar kan taimaka min wajen inganta fasahata ta hanyar kirkiro wasu sabbin abubuwan da suka fi na baya."

Da alama wannan tunanin ne ya sa ya sanya wa wani zanen da ya yi sunan “The Rhythm of Self-Assurance, wato amon yarda da kai, wanda ya samo daga wata waka.

Zanen The Rhythm of Self-Assurance an yi shi ne a sanadiyar wakokin Jimi Hendrix. Hoto: Niyi

"A kwanakin baya ne na saurara wasu wakokin Jimi Hendrix, inda amon kidan ya dauke min hankali.

"Wakokinsa sun kwashe sama da shekara 50, amma har yanzu ana sauraronsu kuma suna karfafa gwiwar mutane.

Wannan ya sa na yanke shawarar zana wani abu domin karrama wannan gwarzo.

Zane-zanen ban dariya

Karrama gwaraza mazan jiya na cikin abubuwan da Niyi ya sanya a gaba.

A lokacin da yake karami, yakan dauki tsawon awanni yana zana littafan wasan yara, duk da iyayensa sukan yi masa fada a kan yin zane a jikin littafansa.

"Lokacin da na fara makarantar sakandare, sai na fara zana littafan wasan yara da suke dauke da irin su Superman da Spiderman da sauransu.

"Na kasance ina boye abubuwan da na zana ne, amma sai watarana mahaifiyata ta binkado su, inda a wannan lokacin maimakon ta min fada kawai, sai ra kone su baki daya."

Bayan wannan lokacin ne sai da Niyi ya yi kusan wata shida bai zana komai ba saboda fushi.

"Na shiga damuwa sosai a wannan dan lokacin saboda ji na yi kamar na rasa komai," inji shi a tattaunawarsa da TRT Afrika, sannan ya kara da cewa, "amma sai na koma na cigaba da zane-zanen da nake yi, inda a wannan lokacin mahaifiyata ta kyale ni."

An sayar da wasu aikace-aikacensa a kan farashin dubban daloli a kasuwannin duniya. Hoto: Niyi

Niyi ya kara da cewa yanzu mahaifiyarsa ce ta fi karfafa masa gwiwa- inda take kasancewa a wajen tarukan da ha halarta tana karfafa masa gwiwa kamar a Mujallar Alexis a Legas, da Mitochondria Gallery da ke Texas, a Amurka.

An sayar da wasu aikace-aikacensa a kan farashin dubban daloli.

Yadda ya taso

Niyi ya fara gane yana da fasahar zane ne a lokacin da yake karanta business administration a Jami'ar Adekunle Ajashin da ke Jihar Ondo, inda ya kammala da digiri mai mataki na farko.

"A jami'a na kaddamar da zanen da na yi na farko, inda daga lokacin ne na gane ashe zan iya samun kudi daga fasahata.

"Wannan ne ya kara karfafa min gwiwa, sannan ya sa na yanke shawarar cigaba da amfani da fasahar a matsayin sana'a."

Bayan ya kammala jami'a a 2018, sai Niyi ya koma Legas domin cigaban aikasa.

"A Jihar Legas ce ake samun damar fadada duk wata sana'a ta fasaha. Komawa Legas na cikin muhimman matakan da na dauka saboda akwai mujallu, wanda hakan ya taimaka min wajen kara kwarewa da sanin makamar aiki."

Kasuwar ayyukan fasaha ta Nijeriya tana da hannun jarin sama da Dala bilu1.8 a Disamba 2023 kamar yadda rahoton arzikin Afirka na 2023 ya bayyana.

Shawarar da Niyi yake ba masu ayyukan fasaha maso tasowa ita ce, "idan kana sha'awar abu, ka fara gwadawa kawai. Zai fi kyau a ce ka fara ka gaza maimakon nan gaba da rika da-na-sanin rashin gwadawa."

TRT Afrika