Janar Muhoozi ya sanar a ranar Juma'a, 10 ga Janairu, cewa ya bar amfani da shafin X. /Hoto: Reuters

Babban hafsan sojin Uganda, Janar Muhoozi Kainerugaba, ya rufe shafin sada zumuntarsa na X.

Janar Muhoozi ya sanar a ranar Juma'a, 10 ga watan Janairu, cewa ya daina amfani da shafin sadarwa na X don "mai da hankali kan rundunar tsaron jama'ar Uganda," wato (Uganda People's Defence Force) wanda shi ne sunan hukuma na sojojin Uganda.

Babban hafsan sojan, ya gaya wa masu bin sa har miliyan daya a shafin X cewa za su "sake haduwa" da shi "a lokacin da ya dace a nan gaba."

Ya kara da cewa "ya san" mabiyansa "suna sonsa" kuma za su ci gaba da binsa "kamar iska."

'Babu shafin'

Idan aka gwada neman shafin Janar Muhoozi a X mai sunan @mkainerugaba, sai a ga an rubuta cewa: "Wannan asusun babu shi, gwada neman wani."

Matakin da babban hafsan sojan ya yanke na barin amfani da shafin X — wani dandali da ya yi fice a kai - ya zo ne bayan da ya haifar da takaddamar diflomasiyya a kwanan nan tsakanin Uganda da kasashe makwabtanta, wato Sudan da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC).

Har ila yau shawarar ta zo ne bayan da ya aike da sako a ranar 5 ga watan Janairu ga madugun 'yan adawar Uganda Robert Kyagulanyi, wanda aka fi sani da Bobi Wine.

Muhoozi ya ce mahaifinsa, Shugaba Yoweri Museveni ne ke hana shi daukar mataki kan Bobi Wine, dan siyasar adawa da ke ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a watan Janairun 2021 da ya yi nasara a kan Shugaba Museveni.

Saƙonni masu cike da ce-ce-ku-ce

Museveni, wanda ya kwashe kusan shekaru 39 a kan karagar mulki, an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ya samu fiye da kashi 58% na kuri’un da aka kada a kan na Wine mai kashi 35 cikin 100.

A tsakiyar watan Disambar 2024, Janar Muhoozi mai shekaru 50 ya wallafa wasu rubuce-rubucen da suka jawo cece-ku- ce — daya daga cikinsu a game da Sudan da kuma na DRC.

A ranar 16 ga Disamba, Muhoozi ya wallafa a shafinsa na X cewa zai "kai hari" kan fararen fata dauke da makamai da ke aiki a gabashin DRC.

Da yake bayyana su a matsayin "sojojin haya fararen fata", babban hafsan sojan ya ce zai kai musu hari "daga ranar 2 ga watan Janairu, 2025," inda ya kara da cewa aikinsa zai kawo karshe a watan Disamba 2025.

Akwai fararen hula da dama da ke aikin wanzar da zaman lafiya a gabashin DRC mai fama da rikici a karkashin Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyi masu zaman kansu.

Akwai kuma wasu fararen fata masu dauke da makamai da DRC ta ce "masu horar da sojoji ne da ke taimakawa wajen zamanantar da ayyukan sojojin Kongo a yankunan Goma da Sake."

An kira jakadan Uganda

Bayan da Muhoozi ya wallafa a shafinsa na X, DRC ta gayyaci wakilin Uganda a Kinshasa, Matata Twaha Magara, domin ya yi bayanin kalaman da Janar Muhoozi ya yi.

A ranar 17 ga Disamba, babban hafsan sojan Uganda ya wallafa a shafinsa na X cewa zai "kama" babban birnin Sudan Khartoum.

Muhoozi ya ce zai nemi taimakon zababben shugaban Amurka Donald Trump don cim ma wannan shiri da zarar Ba'amurken ya hau karagar mulki a ranar 20 ga watan Janairu.

A ranar 18 ga Disamba, Sudan ta shigar da martani ga Uganda, tana mai cewa tana neman gafara "saboda munanan kalamai masu hatsarin gaske na kwamandan sojojin."

Jim kadan bayan wallafa wadannan sakonni guda biyu a kan Sudan da DRC, Muhoozi ya goge su.

Kakakin gwamnatin Uganda, Ofwono Opondo, ya caccaki Janar Muhoozi da laifin lalata alakar kasar da makwabtanta.

Opondo ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da gidan rediyon Capital FM na Uganda a ranar 21 ga watan Disamba inda ya ce: "Babu ko ina a duniya da muka taba ganin babban hafsan hafsoshin tsaron kasar yana aikata irin abin da Janar Muhoozi ke yi."

Opondo ya kara da cewa lokaci ya yi da aka fuskanci halin hafsan sojojin.

A cikin Afrilu 2022, Janar Muhoozi ya rufe shafinsa na X, wanda ke da mabiya 500,000, amma bayan mako guda, ya koma dandalin.

TRT Afrika