Daga
Pauline Odhiambo
Clara Ndinda ta taso ne a zamanin da ake yayin saƙar kwarashi a shekarun 1990, sana’r da manyan mata ke shafe awanni a zaune tare suna saƙa abin yi wa kujera da teburi ado don ƙawata gidajensu.
Amma Clara ba ta fara tsantsar sha’awar saƙar kwarashin ba sai a shekarar 2018 a lokacin da ta ga wata abokiyar wasanta da ta girme tana saƙa kaya masu ban sha’awa da kwarashi.
“Kallon yadda take saƙar na da ban sha’awa saboda da tsinken tsintsiyar kwakwa take saƙar!” kamar yadda matashiyar mai shekara 26 ta shaida wa TRT Afrika.
“Abin ya dinga birge ni da ba ni sha’awa, kuma yana da kyau ƙwarai,” ta ce.
Sha’awarta ta ci gaba da ƙaruwa a lokacin da ta ga mahaifiyarta tana warware saƙar wata tsohuwar rigar sanyi da kuma amfani da kwarashin wajen saƙa tsumman goge-goge da ulun.
“Mahaifiyata ta koya min matakan, amma sai na ga da akwai wahala. Washe gari sai ta saya min ulu, sai na yanke shawarar kallon yadda ake saƙar a shafin Youtube don fahimta kan abin sosai,” in ji Claea, wacce a lokacin matashiya ce mai tsananin jin kunya kuma ɗalibar jami’a.
Takura da cin zali
Duk da cewa daga farko nau'ukan da take saƙawa ba wasu tsala-tsala ba ne, harkar saƙar kwarashi ta matuƙar ɗauke wa Clara hankali a lokacin da take karantar fannin fina-finai a jami'a.
"Wasu daga cikin ƴan ajinmu na tsokana ta. Sukan kira ni da 'Kaka Clara', suna zana wani hoto na na wata yarinya da ke cikin takura tana irin ayyukan tsofaffin mata."
Clara ba ta bari maganganunsu sun ɗauke mata hankali ba, sai ta mayar da hankali wajen saƙa kaya masu sauƙi. "Na saƙa wa kaina ɗankwali. Bai yi kyau ba sam, amma dai na yi alfahari da kaina sosai," ta faɗa.
Bayan da ta kammala jami'a a 2019, Clara ta yi ta fafutukar neman aiki duk da cewa kuwa da zarar ta ga damar aiki take nema. Kwarashi ya zame mata mafita.
"Daga nan sai na yi shawarar sayen kayan saƙar kwarashi da ƴan kuɗaɗen da aka ba ni kyauta a lokacin bikin kammala karatuna," ta ce.
"A cikin sati ɗaya na saƙa wata hula na wallafa ta a shafin sada zumunta. Sai mutane da dama suka nuna sha'awar son sayenta, suna ƙarfafa min gwiwar cewa na fara kasuwancin saƙa hulunan sanyi."
Komawa sana'ar saƙar kwarashi
Clara ta fara wannan hoɓɓasa ne da jarin dala 50, inda ta fara sayar da hulunan sanyin cikin sassauƙan farashi. A yayyin da aka fara sayen kayan nata, sai ƙwarewarta da farashin suka ƙaru.
"Akwai sauran mutanen da ke sana'ar saƙar kwarashi a lokacin suna sayar da hulunan sanyin a kan shilling 100 duk ɗaya, amma sai na yanke shawararsayar da nawa a kan 800 (dala 6). Na san irin ƙwarewar da na saka a yin kayana da kuma tsaftarsu. Kuma sai ga shi masu saye suna saya a kan haka din," in ji Clara.
Wani abokin ciniki ya taɓa yin odar huluna bakwai a lokaci ɗaya kuma ya biya kuɗin gaba ɗaya. "Na ɗauki kimanin mako guda kafin in yi duk nau'in hulunan bakwai saboda a lokacin ina saurin yin saƙar," in ji ta.
Amma abin da ya fara a matsayin kasuwanci mai suna Beanie Hub daga ƙarshe ya koma asali zuwa wanda ke samar da kayayyaki masu yawa. A yanzu ita ma tana saƙar suwaitu na sanyi masu yawa.
"Na ɗauki kwanaki uku don yin rigar sanyi ta farko. Ba ta yi kyau ba, amma ta yi ban sha'awa," in ji ta. "Na yanke shawarar yin riga ta biyu kuma na yi bidiyon TikTok na yadda na saƙata daki-daki kuma an kalli bidiyon sasu sama da miliyan ɗaya kuma an yi ɗaruruwan mutanen da ke sha'awar saye sun yi tsokaci."
A ƙarshen wannan ranar, Clara ta samu sabbin mabiya 10,000 inda suka ƙaru a kan 200 da suke bin ta kafin wallafa wannan bidiyon. "Mutane sun cika akwatin saƙonta da yin oda. Saƙonnin sun yi yawan da har ta gaji da amsa su, duk da cewa ba ni da ƙwarin gwiwa game da ƙwarewar yin suwaita sosai."
Sauyawar ƙaddara
Da Clara ta ga ta gaza amsa yawan buƙatun mutane sai ta rufe shafinta na sada zumunta, inda ta saka saƙo a saman shafin cewa suwaitunta ba na sayarwa ba ne.
A wannan lokacin sai ta tsaya ta ƙware a kan saƙarta, inda ta ci gaba da yin hulunan sanyi kawai don sayarwa.
Zuwa ƙarshen shekarar 2022, sai Clara ta sake ƙwarewa da saƙa rigunan sanyi, amma har a lokacin ba ta da tabbas kan ko za ta sayar da su.
Ta ɗauke wan kanta hankali ta wajen ƙoƙarin neman aiki a gidan talabijin, amma sai ta yi rashin sa'ar haɗuwa da ƴan damfara da sunan za su ba ta aiki.
Ƙoƙarinta na ƙrshe na faɗaɗa kasuwancinta ya zo ne bayan da ta sha da ƙyar a wani mummunan hatsrin babur da ya kusa ritsawa da ita.
"Na karye a ƙafata da kuma jin ciwo a hannuna. A lokacin mahaifiyata ke min wanka saboda ba zan iya ko da motsi da ƴan yatsuna ba balle har na iya riƙ kwarashi," in ji Clara.
"A lokacin ban sani ba ko zan warke. A sannan ne na yi tunanin cewa lallai fa rayuwata ta ta'allaƙa ne a kan fasahata."
Haɗaka
"A lokacin da ta fara samun sauƙi, sai Clara ta fara karɓar aikin saƙa suwaita daga masu saye. "Na koma kan tsofaffin saƙonnina na shafukan sada zumunta inda na amsa buƙatun masu son sayen suwaita daga mutanen da a baya suka tuntuɓe ni," ta ce.
"Har a lokacin mutane da dama suna sha'awar abin, har ma wani mutum ya yi odar cewa a saƙa wa iyalansa riguna da hulunan sanyi iri ɗaya!" A lokacin da ake ci gaba da saka odar sayen, sai Clara ta fara koya wa ƴan mata masu sha'awar sana'ar yadda ake saƙar kwarashi.
"Mafi wahala shi ne darasi na farko - rike ƙugiya da zaren don yin zubin farko," in ji ta. Da yawa daga cikin ɗalibanta sun samu sauƙin zuciya daga ɗumbin matsalolin da suke ciki a da bayan da suka fara ɗaukar darasi, gwagwarmayar da ta tuna tun farkon darasinta tare da mahaifiyarta.
"Za mu iya shafe kusan makonni biyu a kan wannan taƙamaiman abu, amma da zarar ɗalibaina sun riƙe wannan, to babu kuma wata matsala. Wannan yana faranta min rai," in ji Clara.