Matan Maasai na neman sabbin hanyoyin samun kudade baya ga kiwon dabbobi. Hoto / TRT Afrika

Daga Ronald Sonyo

Makiyayan kabilar Maasai da ke arewacin Tanzania na rungumar kiwon zuma bayan shekaru suna fuskantar fari da ya kassara dabbobin da suke kiwo.

Jama'ar da mafi yawansu makiyaya ne sun bayar da muhimmanci ga al'adar mallakar garken shanu, akuyoyi da tumaki da suka gada kaka da kakanni.

Amma kuma munin da yanayi ya yi wanda ba a taba tsammata ba ya janyo rabuwarsu da tsarin rayuwar da suka saba da shi, inda fari ya janyo ba sa iya ciyar da dabbobin.

Kauyen Esilalei da ke yankin Arusha ne ya fi rungumar kiwon kudan zuma, inda kwangirin kiwon zuma da dama suke makale a jikin bishiyoyi.

Yadda aka rataye kwangiri a jikin bishiyu suna reto a yankin. Hoto / TRT Afrika

Rukunin matan Maasai kusan 30 a nan, na daga wani bangare ne na wata karamar kungiyar noman zuma, inda suka samar da zumar. suke kunshe ta tare da sayar da ita. Maza ma sun shiga wannan kasuwanci mai albarka na noman zuma.

Paulo Michael ya shaida wa TRT Afrika cewa yana daya daga cikin wadanda suka tsinci noman zuma kuma tuntuni ya samu kwastomomi, wasu ma a wajen kasar.

"Na koya wa yarana irin dabaru da kwarewata, saboda ta hanyar wannan aiki muna samun abinci. Duk da akwai wasu 'yan kalubale kamar samun kayan kiwon na zamani, amma a hankali muna lallaba wa," in ji Paulo.

Masu kiwon zumar na bayyana cewa aikin da suke yi a matsayin kungiyar sayar da zumar na taimaka musu wajen bunkasa kasuwancin, da kuma kara fahimtar kasuwancin ta yadda za su samu karin kasuwa sosai.

Har yanzu mafi yawan manoman zuma na amfani da hanyar gargajiya wajen tattara zumar. Hoto / TRT Afrika

Maria Shinini, wata mai kiwon zuma a yankin daga wannan kauye, ta bayyana yadda sana'ar ta sauya rayuwarta da ta iyalinta.

Ta ce iyalinta na amfani da kudaden da ake samu daga sayar da zumar wajen biyan kudin makarantar yaransu, gina gidaje da kuma kara yawan shanun da suke da su.

Shigar mata sana'ar kiwon zuma

A al'adance, da wahala matan Maasai su shiga wani aiki na neman kudi. Ba su da wani karfin fada a ji a al'umarsu da maza suka zama su ne jagorori. Amma a yanzu wasu daga cikin matan, na taka rawa a fannin tattalin arziki ta hanyar kiwon zuma.

"A yanzu, muna taimaka wa mazajenmu don kula da iyalanmu. Ana girmama mu saboda noman zumar da muke yi. Yanzu ina iya ciyar da kaina da iyalina."

Shinini da ke da kwangirin zuma 85 ta bayyana cewa "Da farko, babu masu sayen zumar da muke samarwa. Muna sayar da ita ga iyalai, abokai da garuruwan da ke kusa da mu. Amma a yanzu mun fadada kasuwarmu."

A yayin da suka bayyana nasararsu, masu noman zumar sun bayyana cewa wannan tafiya tasu na da wahala. Da fari ba su da wani ilimi na kiwon zuma, inda suka rika asara tsawon shekaru.

Shinini ta ce "A baya ba mu da wani cigaba, ba ma iya zuwa kasuwa mu sayi kaya da kan mu. Amma a yanzu muna da kudin saya, muna iya biyan kudin makarantar yaranmu tare da taimakawa jama'armu. A baya ina tambayar mijina ya ba ni komai."

Ta ce "Muna farin ciki, saboda mun fara ganin sakamako mai kyau. Amma dabbobin dawa irin su giwaye a wasu lokutan suna karya bishiyun da muka rataye kwangirin zumar."

Samar da zuma ta tallafawa rayuwar matan Maasai a Arusha. Hoto / TRT Afrika

Karin daraja

Masu kiwon zumar sun fara kara daraja ga kayayyakinsu ta hanyar samar da zumar da take gauraye da magani ga jama'ar yankin.

"Mun san darajar maganin gargajiya, shi ya sa muke gauraya su da zuma kuma ana sayar da su kan kudi da yawa a kasuwanninmu. Kwalbar zumar mai hade da magani na kaiwa har dala $15," in ji Shinini.

Amma babban kalubalen da suke fuskanta shi ne yadda dabbobin dawa ke rusa inda suke kiwon zumar. Akwai babban daji da ke makotaka da kauyensu, wanda hakan ke kawo musu barazana inda dabbobi irin su giwaye ke lalata musu gonakin zumar.

Rashin ingantattun kayan aiki na ba su wahalar kai zumar da suke nomawa zuwa kasuwanni na kusa.

TRT Afrika