Daga Charles Mgbolu
Masaniyar fasahar gine-gine kuma malamar jami'a 'yar kasar Ghana mai shekara 60 Lesley Lokko, ta kara yin shuhura bayan an sanar da ta lashe kambin kwarewa a gine-gine na 'Royal Institute of British Architects'.
Ita ce mace 'yar Afirka da ta samu wannan kambi, kuma bakar fata ta biyu a duniya da aka karrama a tarihin RIBA.
Kwamitin bayar da kambin 2024 ya bayyana cewa an zabe ta ne saboda "Shugabanci na misali, kauna da jajircewar ta ga fannin fasahar gine-gine da binciken ilimi a fannin, musamman yadda take mayar da hankali wajen bayar da darasi kan launin fata, asalin al'umma da fasahar gine-gine."
Kwamitin ya kuma yabe ta kan kayan da ta baje-koli a wajen Venice Biennale, Baje-Kolin Kasa da Kasa Kan Fasahar Gine-Gine daga kasashe daban-daban, da aka gudanar a Venice, Italiya kowacce shekara.
Kwamitin ya kira aikinta da "matakin assasa tushen fasahar gine-ginen hadaddiyar Afirka da masu alaka da Afirka."
'Lamarin dimauta'
Lokko da ta dimauta saboda farin ciki ta kira sanarwar da cewa "mafarki ne" a wani sako ta hsafin sada zumunta.
"Wannan abu ya dimauta ni sosai. Ina godiya ga kowa wanda suka bayar da gudunmowa ga nasarorina a shekaru 30 da suka gabata. Sama da komai, na yi fatan a ce muna tare da dukkan ku yau a nan."
A shafinta na Instagram ta bayyana cewa "Na sadaukar da wannan ga mutane da dama - abokan aiki, wadanda muka nhada kai, al'ummu, kamfanoni, da musamman malamai - da suka sauya rayuwata ta hanyar da ba zan iya bayyana wa ba."
An haifi Lokko, wadda malamar makaranta, marubiciya da kula da mutane ce, a Dundee, Scotland. Mahaifinta dan Ghana ne, mahaifiyarta kuma 'yar Scotland.
Ta sadaukar da rayuwar aikinta ga bangaren da aka manta da shi na alakar da ke tsakanin fasahar gine-gine, asalin al'umma da launin fatarsu.
Fasahar gine-gine don gobe
Lokko ta ce kayan da ta baje-koli a Venice Biennale wata dama ce ta gano gibin da ake da shi a Afirka bayan mulkin mallaka, sannan a samar da yanayin da matasa masu zuwa za su kware a fannin fasahar gine-gine.
A wata tattaunawa da aka yi da ita, ta ce tana fatan za a mayar da hankali sosai wajen kafa makarantun horar da matasan Afirka kan fasahar gine-gine.
"Afirka na da dimbin matasa da suke fama da yunwa kuma suke da burin nasara a rayuwa. Amma ilimi shi ne babban kalubale: akwa makarantu da dama da ba su da inganci a nahiyar da ke mutane kusan biliyan guda.
"Kuma mafi yawanci, tsarin koyarwar da ake amfani da shi wanda aka gada daga 'yan mulkin mallaka ne. Hanzarin da ake samu wajen sauyi na da matukar muhimmanci, kuma ba mu da fasalin koyo da koyarwa da za mu tunkari wannan abu."
Lokko ta ci gaba da koyarwa a makarantu a duniya, kuma ta samar da makarantun koyar da fasahar gine-gine - a Johannesburg, Afirka ta Kudu da Accra babban birnin Ghana.