Julian yana son zana fuskokin mutane a allo. / Hoto: Julian

Pablo Picasso, wanda shahararren mai zane ne ɗan ƙasar Sifaniya, ya taɓa cewa "duk wani abin da za ka iya tunani da gaske ne".

Mai zanen nan na ƙasar Ghana Julian Selby ya soma zane shekaru takwas da suka wuce, amma karfin tunanin da ya sanya a cikin fasaharsa ta zane, da sauran abubuwan da ke cikin duniya sun tafi da shekarunsa da ƙwarewarsa.

Mutane da yawa masu sha'awar suna da wuya su yarda cewa wannan matashin da ke amfani da sunan sa na Pimpin, wanda ake kira "Prosperity is My Pride in Nature", ya koyar da kansa kuma sabon salo ne ga wannan sana'a.

Ana yaba masa sosai a cikin tafiyarsa kamar yadda yake shan suka, yana tunatar da kansa cewa shi ɗalibi ne mai ƙoƙarin samun lafiya kowace rana.

"Na soma zane bayan kammala jami'a," kamar yadda Julian ya bayyana wanda ya yi karatu kan tashoshin jiragen ruwa da jigilar kayayyaki ta ruwa a Accra, kamar yadda TRT Afrika ya shaida wa TRT Afrika.

“A ko yaushe ni na kasance wanda ba ni son fita, ina shafe awowi a cikin ɗakina inda zane ko a lokacin da nake neman aiki."

Julian na amfani da fensiri domin yin zane. / Hoto: Julian

Yayin da yake jiran ya samu aiki, Julian ya gano cewa zai iya samun kuɗi daga fasaharsa. A lokacin, ya yi hidimar ƙasa ta shekara ɗaya ta wajibi da ake buƙata ga duk wani ɗan Ghana ya yi.

"Na kirkiro dabaru da yawa kuma na fara wallafa wasu daga cikinsu kan shafukan sada zumunta," kamar yadda mai zanen ya bayyana, wanda ya smau ƙarfin gwiwa daga wasu masu zane a shafin YouTube.

"Zanen da na soma yi na farko na sayar da shi ga wani wanda ban sani ba. Mai sayen ya ga abubuwan da nake sayarwa a intanet," kamar yadda ya tuna.

Neman suna

Zanen da ya fara a cikin ɗakinsa ya haɓaka zuwa wani babban kasuwanci, inda aka yi ta aiko masa da odar yin hotuna na allo daga ƴan ƙasa da wasu manyan ƴan Afirka ta Kudu.

Julian ya yi zane da dama waɗanda suka haɗa da na tsohon Shugaban Ghana John Kufour da shugaban Liberia George Weah da wasu manyan mutane.

"Na gane da wuri cewa kuna buƙatar salon sa hannu don yin tasiri. Yawancin masu fasaha suna zane da gawayin graphite. Na ɗauki gawayin kuma na canza sautin saboda ina so in zama na musamman," in ji Julian, wanda ya kira aikinsa "Artwork by Pimpin ".

"Na ci gaba da koyon dabaru kuma na haɗa salo da yawa don ƙirƙirar nawa."

Duk da hotunansa da ake buƙata, ra'ayin yin zane ya kasance ainihin abin da Juilan ke sha'awa. Hoto: Julian

Bayan ya rungumi aiki na cikakken lokaci a matsayin mai zanen fensir ƙwararre a haƙiƙanin gaskiya, horon Maritime na Julian abin tunawa sosai.

"Watsuwar da aikin ya yi tamkar wutar daji ya sa hatta da tsoffin abokan karatuna na jami'a sun gani sun neme ni don na yi musu. Wasu daga cikinsu suna sha'awar sauya shekata daga masana'antar jigilar kayayyaki zuwa fasahar zane," in ji shi.

Ubangidana

Duk da hotunansa da ake buƙata, ra'ayin yin zane ya kasance ainihin abin da Juilan ke sha'awa.

"Har cikin zuciyata nake son zane. Ni da kaina na kirkiro yawancin salon, sannan in dauki hotunan zanen da na yi," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

An yabi Julian da kawo salon zanen fensir a Ghana kuma ya ƙirƙiri salo 150 akan jigogi daban-daban. Ya fi alfahari da wani aiki mai taken "The Struggle", inda zanen ke nuna yadda ake kokarin tserewa wani mawuyacin hali.

“Gwagwarmaya ta shafi rayuwa ne da kalubalen da ke cikinta, idan ka kalli hoton, za ka ga an ja batun ta bangarori daban-daban ta hanyar sarka da aka daure a wuya, na yi amfani da wannan ra’ayi ne wajen bayyana yadda mutane za dinga jan ka daga nan zuwa can a rayuwa, amma dole ne ku ci gaba da fafutuka," in ji Julian.

Zanen hoto na sanya Juilan farin ciki. Photo: Julian 

"Wasu mutanen sun nuna shakku kan lamarina da farko. Na sami maganganu marasa kyau, wasu ma suka ce karya nake yi cewa ni ne makirkirin fasaha ne," in ji shi.

"Na yi watsi da su saboda na san dole ne in ci gaba da mai da hankali kuma in ci gaba da wanzar da burina na zama mai zane."

Kwaikwayon zahiri

Ɗaya daga cikin alamun kasuwancin Julian shi ne ikon kwaikwayon halaye na tunanin batutuwansa - yana sa su zama kamar da gaske.

Yana ɗaukar kimanin kwanaki biyar don kammala hoto, aiki mai ɗaukar lokaci idan aka yi la'akari da yawan karbar ayyukna daga mutane da kuma mayar da hankalinsa ga samun cikakkun bayanai.

Abokan cinikinsa sun haɗa da mutanen da suke so su ba 'yan uwansu mamaki tare da hotuna a matsayin kyauta a ranar haihuwa, ranar tunawa ko a bukukuwan ritaya.

Lokaci-lokaci, yabo ya fi saka Julian farin ciki fiye da yadda yake samun ladan aikinsa. Hoto: Julian 

"Ina samun kusan odar yin kamar hoto goma a mako, wanda hakan ke sa ni kasancewa cikin aiki sosai," in ji shi.

To, mene ne a cikin zanen hoto ne da ke sa Julian farin ciki?

"Ina son ɗaukar motsin yanayin da mutum ke ciki da kuma daidaita shi zuwa cikakken bayani. Wannan yana ɗaukar lokaci mai yawa amma shi ne ɓangaren nishaɗi na aikina," in ji shi.

"Idan abokin ciniki bai gamsu da sakamakon ba, zan ci gaba da hakan har sai mutumin ya yi farin ciki."

Daga cikin fitattun ayyukan Julian akwai hoton da aka ba wa tsohon shugaban Ghana John Kufuor. Hoto: Julian

Lokaci-lokaci, yabo ya fi saka Julian farin ciki fiye da yadda yake samun ladan aikinsa.

TRT Afrika