Daga Mazhun Idris
Daya daga cikin manyan abubuwan da suka ja hankali a ziyarar Uwargidan Shugaban Kasar Turkiye Emine Erdogan zuwa Nijeriya shi ne baje-kolin wasu kayatattun ayyukan fasaha na wasu matan kasar da Cibiyar Yunus Emre ta yi.
Daga cikin masu fasahar da suka baje-kolin kayayyakinsu a wajen akwai Halima Abubakar, wadda take amfani al’adu daban-daban wajen fitar zane mai kyau, wadanda suka matukar birge Uwargidan Shugaban Kasar.
“Na zabi salon zanen Mandala ne da Tezhip da Dotisim,” inji Halima a tattaunawarta da TRT Afrika.
A harshen Turkiye, Kalmar Tezhip na nufin ‘kayan adon da aka hada da zinare.” A kasar, ana amfani da fasahar wajen kawata zane-zane da rubuce-rubuce ta hanyar amfani da kaloli daban-daban da alburushi.
Ana amfani da Tezhip wajen kwata Masallatai da wuraren ibada da zane-zanen masu na’uka daban-daban ko dai a tsaye, ko a da’ira ko kuma a hade su domi su fitar da wata siffa mai nuna al’aduna yankin Larabawa.
Ita kuma fasahar zanen Mandala ta samo asali ne daga kalmar “da’ira”. Salon fasahar zane ne da ake amfani da layuka da da’irori wanda asali yake nufin yanayin zanen duniya a addinin Hindu da Budda, wanda yake nuna da tafarkin samun natsuwa da maslaha.
Dotism kuma na nufin amfani da digo-digo wajen fitar da zane kafin a bi shi da kala.
Ana bin kan digo-digon ne da kaloli domin su baje, sannan su fitar da zane mai kyau. Ana amfani da manhajar canva wajen fitar da zanen dot.
Ayyukan sha’awa
Halima ta shiga harkokin zane-zane ne shekara goma da suka gabata, bayan ta ci karo da wasu zane-zanen Mandala a kafar Instagram. A lokacin tana da shekara 18 ne, kuma tana karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano a Arewa maso Yammacin Nijeriya, inda take karanta biochemistry.
“Sai na tuntubi kwararrun masu fasahar daga Dubai da India da wasu kasashen yankin Asia domin samun karin bayani. Amma babu wanda ya amsa min,” inji Halima a lokacin da take bayyana ta faro.
A lokacin ne sai ta fara neman wanda ya iya amfani da fasahar Mandala a Nijeriya da zai iya kowa mata, amma shi ma ba ta samu ba.
Duk da haka Halima ba ta yi kasa a gwiwa ba, sai ta fara binciken yadda za ta koya wa kanta zanen ta hanyar kallon bidiyoyi da karatu a intanet, wanda ta dauki kusan shekara uku tana yi. Domin kirkirar zanen Mandala, sai ta fara amfani da alkamin fensir mai kala da takardar magani da tsinsiya.
“Na sha fama wajen koya da gwadawa har na kai ga kwarewa,” in ji ta.
Halima ta zama kwararriyar mai fasahar ce a shekarar 2017, lokacin tana da shekara 21.
Halima tana hada al’adun yankin Afirka wajen fitar da zanenta wadanda suka kara kawata aikin tare da kara masa kasuwa a nahiyar.
Halima ta bayyana cewa halinta na bin diddigin abubuwa da sannu a hankali ya taimaka mata wajen kwarewa. Ta ce ra’ayinta na tabbatar duk abin da take yi, ta yi shi da kyau ya taimaka mata wajen samun nasara.
Fasahar ’yan Afirka
Kasancewar fasahar Mandala na da alaka ne da yankin Gabashi, sai Halima ta fara tunanin yadda za ta kara al’adun Afirka a ciki, amma ba tare da ta bata asalin fasahar ba.
“Sai na yanke shawarar fara kara wasu abubuwa da suke nuna al’adun Afirka ta hanyar amfani da wasu salo domin bayyana ci gaban da aka samu a bangaren fasaha a nahiyar. Babu iyakancewa a abubuwan da mutum zai iya kirkira,” in ji ta.
Yadda take hada fasahar da al’adun nahiyar Afirka a cikin ayyukanta din ne ya jawo mata kwastomomi daga manyan mutane da ofisoshi da dama.
Zanen jikin bangon da take yi yana bayyana al’adu da abubuwan da aka sani. Yanzu haka ana amfani ayyukanta a Masallatai da dama a Nijeriya, har ma da Fadar Shugaban Kasa.
Lokacin tunani
Shin yaya Halima take yi wajen fitar da zane-zanen Mandala?, “Kwarera a wannan fasahar na bukatar juriya da hakurin tabbatar da komai ya fita da kyau. Sannan kana bukatar kayayyakin aiki,” in ji Halima.
Ana fitar da zanen Mandala ko dai kai-tsaye a jikin bango, ko a yi amfani da manhajar canva wajen zanawa kafin a daura a bango, sannan a bi shi da fenti. Abin da Halima ke fara yi idan an ba ta aiki shi ne ta ziyarci wajen, ta duba irin ginin ko wajen da ake bukatar zanen, sannan ta tantance irin zane da kalolin da za ta yi amfani da su.
A duk lokacin da za ta yi aiki, tana zuwa ne tare da ma’aikatanta, sannan su share wajen da su yi aikin, sannan su shafa wasu na’ukan man da ake shafawa kafin a fara fenti, wadanda suke taimakawa wajen fitar da zanen fes.
Sai bangaren kirkira a cikin ma’aikatan nata su fitar da zanen farko da hannu.
“Sai ni kuma in bi zanen da suka fitar da fenti ba tare da kaucewa daga asalin zanen ba. Amma wasu lokutan nakan kara wasu abubuwa da suka zo min a lokacin da nake fitar da zanen domin kara kawata aikin,” in ji Halima.
Tana aiki ko dai a zaune ko a tsaye, ko kuma ta hau saman matakala, ya danganta ne da yanayin wajen. Hankalinta ya koma kacokam kan aikinta ne idan ta fara ta hanyar tunane-tunane da zancen zuci.
“Fasahar Dotilism wajen zane yana cikin lokaci sosai, wanda hakan ya sa yake bukatar hakuri, juriya da natsuwa, sannan ya kasance kana da sha’awa,” in ji ta.
A cikin Birnin Tarayya Abuja da wasu jihohin Nijeriya, ayyukan Halima na nan birjik suna kawata wurare, inda har ake tattaunawa yadda kyawun ayyukan suke samar da kwanciyar hankali.