Wasu daga cikin mawakan ana musu kallon gwaraza wadanda suka nuna bajinta a masana'antar wakokin na Afirka.

Daga Pauline Odhiambo

Babu shakka Allah Ya albarkaci Afirka da zaratan mawaka. Sai dai duk da haka, yana da kyau a fahimci cewa komai kyawun abu, yana da lokacin da tausaronsa zai dusashe.

Akwai kungiyoyin mawaka ko daidaikun mawaka da suka yi tashe, amma saboda wasu dalilan aka daina jin duriyarsu a lokacin da suke tsaka da ganiyarsu, amma har yanzu ana cigaba da maganarsu a nahiyar.

Bari mu fara da Nijeriya.

P-Square

P-Square

P-Square: Tagwayen sun yi tashe matuka. Sautin wakokinsu ya yi amo sosai tare da cewa suna da fasahar kirkira da iya rawa da kuma kima a wajen mutane. Sun fitar da wakokin da suka yi shuhura kamar "No One Like You", "Ifunanya", "Alingo", "Chop My Money", da sauransu.

Lokacin da suke ganiyarsu, babu wata kungiyar mawaka a Afirka da ta yi kusa da su. Amma sabani tsakaninsu ya jawo rugujewar hadakar.

Duk da cewa sun fitar da wasu wakokin a baya-bayan nan, lallai da alama ana cigaba da tuna lokacin da suke ganiyarsu.

Haka kuma wakokin Bracket na "Yori Yori" da "Mama Africa" suma sun yi tashe sosai a nahiyar.

J-Martins

J. Martins

Shi ma J. Martins dan Nijeriya ne da ya kasance fitaccen mawaki a fadin Afirka. Daga cikin fitattun wakokinsa akwai "Good or Bad" da "Oyoyo" da wadanda dukansu sun yi tashe a nahiyar Afirka baki daya. A tattaunawarsa da jaridar Punch a shekarar 2021, mawakin ya bayyana cewa ya daina harkar waka, ya koma noma da siyasa.

A Afirka ta Kudu, kungiyar mawakan Mafikizolo sun shigo harkar da zafinsu da fitattun wakokinsu "Khona", "Love Potion" da "Tchelete". Sai dai daga baya an rage jin wakokinsu.

Mafikizolo

Fitaccen mawakin Ghana Fuse ODG ya nishadantar da mu da wakarsa ta "Million Pound Girl" da kuma wadda ya yi daga baya ta "Dangerous Love". Shi ma dai yanzu ba a cika ji daga gare shi ba.

A Kenya, mawaki Redsan ya fitar da wakoki da dama a shekarun 2000s, inda ya kasance daya daga cikin fitattun mawakan Kenya. Amma shi ma din yanzu shiru muke ji daga wajensa.

Kungiyar mawaka ta Elani band wadda hadakar mawakanta ta fitar da wakoki irin su "Jana Usiku" da "Kookoo" sun raba gari kowa ya kama gabansa.

Obsession

A kasar Uganda, kungiyar mawaka ta Blu 3, wadda ta kunshi mawaka Jackie Chandiru, Lilian Mbabazi da Cindy Sanyu, ne aka fi ji a yankin Gabashin Afirka a shekarun 2000s. Wakokinsu irin su "Hitaji", "Burn" da "Where You Are" sun yi shuhura, amma suma a shekarar 2008 suka watse bayan shekara hudu suna wakoki tare.

Obsession

Obsessions wata kungiyar mawaka ce ta mata zalla a Uganda da ta yi tashe. Daga cikin fitattun wakokinsu da suka yi tashe akwai "Jangu" da "I'll Do".

A Tanzania an daina jin duriyar fitattun mawaka. Daga cikinsu akwai Lady Jaydee, Mr Nice, MB Dogman, Ray C da Kungiyar mawaka ta TMK Wanaume Family da suka yi wakar "Dar Mpaka Moro" da ta ta yi tashe sosai. Wasu daga cikin fitattun wadanda suka fara waka a kasar da suka hada da Farfesa Jay da Mwana FA a kasar ta Tanzania sun koma siyasa.

Ray C

Mawakin Bobi Wine na Uganda ma ya gwada kwanjinsa a siyasa.

Bayan ambaton wadannan zaratan mawakan, wane ne ba ya ji kamar a dawo da hannun agogo baya a harkar waka?

TRT Afrika