Oluwatobiloba Fasalejo yana amfani da bayyana yanayin zamantakewar al'umma a cikin salon zayyana na zamani/ Hoto: Fasalejo

Daga Pauline Odhiambo

A harshen Yarbanci, Fasalejo na nufin mutumin da yake nuna kulawa ko karamci.

Kuma a zahiri, haka lamarin yake ga ɗan Nijeriya mai aikin zane Oluwatobiloba Fasalejo wanda ke amfani da irin wannan halayya wajen zanen al'ummar da ya ke ciki.

''Muna da abubuwa marasa kyau da yawa da ke faruwa a Nijeriya da ma duniya baki daya, dalilin da ya sa na ke son zane-zane na su kasance irin waɗanda za su samarwa mutane kwanciyar hankali,'' kamar yadda mai salon zayyana na "expressionism" na zamani ya shaida wa TRT Afirka.

''Ina son mutanen da na zana su samu kwanciyar hankali a cikin al'ummar da suke ciki tare da zaman lafiya da soyayya da na ke nunawa a zane-zane na.''

A cewar Mujallar Artland, salon zayyana na "expressionism", abu ne da masu fasahar yin sa ke kokarin fayyace abubuwan da mutane kan ji a zukatansu ta salon zane.

Salon zayyana na "expressionism", abu ne da masu fasahar yin sa ke kokarin fayyace abubuwan da mutane kan ji a zukatansu ta salon zane./ Hoto: Fasalejo

Sananniyar Fasaha

Mai fasahar zayyanar ma shekaru 24 daga jihar Ondo, a ko wane lokaci yana sane da yanayin mutane.

Tun yana yaro, Fasalejo ya ke tallafawa danginsa ta hanyar sayar da zanensa.

“Wannan ita ce hanyar da na ke bi wajen ƙokarin samun abinci amma mahaifiyata ta hana ni, tana mai cewa hakkin iyaye ne, ba na Yara ba,'' in ji shi.

Sai dai duk da haka, matashin mai zanen yana da matuƙar sha'awar sakawa al'ummar da ya fito inda ya sake komawa ga fasahar zayyana don nuna gadiyarsa.

Fasalejo yana da matuƙar jin daɗin sakawa al'ummar da ya fito ta hanyar fasahar zane-zanensa/ Hoto: Fasalejo  

''Na soma ne da yiun zane-zane a kyauta ga mutane a cikin al'ummat. ina yinsu ne a kan takardar rubutu kuma idan na nuna musu, irin kallon farin ciki da godiyar da ke kan fuskokinsu ya fi min kuɗi,'' in ji matashin.

''Na gane cewa, hanya ce mai kyau da za ta iya nuna musu ka na tare da su da kuma yaba musu. Sirrin labarinsu har 'ya zuwa yanzu shi ne ya ke ƙara min karsashi a yin zane na.”

''Zuwa ga Cancanta''

Jerin zayyanarsa mai suna 'More than This' na ɗaya daga cikin salon ayyukansa da suka nuna kyawun al'ummar.

“Akwai zane-zane guda shida a cikin jerin ayyukan da na saɗaukar wa duka al'ummarta da suke ji kamar ba su cancanta ba ko kuma ba su yi koƙari,'' in ji Fasalejo.

''Wannan tunatarwa ce kan mun fi ƙarfin matsalolinmu, kuma a tare za mu iya shawo kan komai.''

Faselojo ya ƙware ne a zayyana da acrylic da oil mediums/ Hoto: Faselejo

Kamar sauran masu fasahar zane-zane, Fasalejo ya fara aikin zane ne ta hanyar ra'ayi da ya ƙarfafa sha'awarsa waɗanda ke tafiyar da tsarin zayyanarsa daga farko har zuwa ƙarshe. Amma a wasu lokutan, ya kan samu jinkiri wajen samun abun da zai ta da sha'awarsa.

“Cim ma wannan na buƙatar jimiri matuƙa. Wani lokacin kawai ina ci gaba da zanen ina kuma mayar da hankali wajen yin aikin saboda a ƙarshe na samu zane cikakke,” in ji mai zanen da ya ƙware a zane da acrylic da kuma mai.

Wani jerin zane-zanen mai taken ‘'Yan uwa mata Albarka ne’ wata shaida ce kan sabon salon basirararsa yayin zane-zane.

“Taken 'yan uwa mata ya fara ne da zane guda, amma daga baya na fitar da zane-zane uku,” in ji Fasalejo, wanda yake da 'yar uwa guda.

'‘'Yan uwa mata Albarka ne’ wani take ne da ke nuna 'yan-uwantaka. / Hoto: Fasalejo

Gado da al'ada

A ƙarshe aikin zanen yana ƙayatarwa da ke nuna ƙarfin tarihin Yorabawa, inda yake cakuɗa tunanin ƙashin-kai da alfahari da al'adu.

Bisa la'akari da mai kallo, salon zanen Fasalejo suna bayyana kamar hoton allon kwamfuta kamar an saka a kwamfuta – wannan shi ne babbam tambarin mai zanen, inda yake bayar da labarai da nasarori a al'ummarsa.

Ya bayyana cewa, “Duka zane-zanena haka salonsu yake (tamkar kwamfuta). Ina gama salo daban-daban na haske da duhu don ƙirƙirar wani salon”.

“Wannan na nuna yanayi mabambanta da ƙalubale da mutane ke fuskanta da matakan jimirinsu.”

Yawancin zane-zanen Fasalejo suna kama da sikirin ɗn kwamfuta. / Hoto: Fasalejo

Yanayi mai canjawa

Fasalejo ya ce ƙwarewarsa na da alaƙa da shekarun da ya shafe yana nazartar abin da kuma atisaye, hadi da fasahar da Allah Ya hore masa.

'Abin bajinta'

An nuna zane-zanen Faselejo a gidajen nune-nune da dama a Nijeriya da Kenya.

TRT Afrika