Daga Pauline Odhiambo
Idan ka bibiyi ayyukan fasahar Faithe Turner, za ka ga abubuwa uku sun bambanta da sauran- ƙoƙarin nuna kyawun mata baƙaƙen fata, da nuna jajircewar mata domin samun nasara ba tare da gajiyawa ba, da kuma amfani da zanen ƙwaron malam buɗe mana littafi a jikin zane-zanenta.
Yawancin abubuwan da Faithe take zanawa ba ta sanya musu ido. Wannan shi ma wani yunkuri ne a ayyukanta na isar da wani sakon, inda a sauran zane-zanen kuma da take saka musu idon, ake zana su a kusa da su domin nuna muhimmancin amincewa da yadda mutum yake, maimakon raina yanayin halitta, musamman launin fata.
"Na fi mayar da hankali a kan laɓɓa da hanci a zane-zanena saboda na fi sha'awar bayyana yanayin mata bakaken fata, kuma wadannan halittun ne ake kallo ana musu dariya cewa ko dai sun yi girma ki kuma fadi da yawa," in ji Faithe a tattaunawarta da TRT Afrika .
"Su mata farare suna iya nuna labbarsu a kalla gani, a yaba, amma mata bakaken fata ba haka abin yake ba, inda sukan yi fargabar bayyana yanayin jikinsu," in ji mai fasahar wadda mahaifiyarta 'yar Haiti ce.
"Ina so bakaken mata su gane cewa suna da matukar kyau suma."
'Gashin 'yan mata'
Mata bakaken fata sun yi fice wajen kitso daban-daban, sannan Faithe tana yin zane-zane da dama na na'ukan kitso masu kyau.
Kwarin gwiwarta na mayar da hankali kan bakaken fata ya samo asali ne daga abin da ya faru da 'yarta.
"Lokacin da yarinya ta take da shekara 5, tana karatu a wata makarantar da mafi yawan dalibanta kabilar Spain ne. Watarana ta dawo gida take fada min cewa ta tsani irin salon kitson da ne kanta, ta ce ta fi son gashinta ya tsaya a tsaye kamar yadda na sauran daliban makarantar yake."
"Sai muka zaunar da ita muka bayyana mata irin kyawun da take da shi, da irin yadda gashin ya mata kyau. Daga nan ne sai na fara tunanin yaya sauran mata bakaken fata yara da manya suke ji," inji mai fasahar mazauniyar birnin New York.
"Daga wannan tattaunawar ce na fara mayar da zane-zanen da nake yi a kan mata bakaken fata."
Nan da nan sai Faithe ta kware wajen zana na'ukan kitso ta kwamfuta ba tare da wani ya koya mata ba.
Hada launuka daban-daban
Tana amfani da launin ruwan kasa domin nuna na'ukan fatar mata bakaken fata da kuma irin kalar da suka fi so a gashi.
Amfanin zane-zanen nan shi ne domin a manna a shagunan kitso, domin mata sun rika zabar salon kitson da suke so.
Da fasahar kirkira irin ta dauri da wadda ake amfani da intanet duk suna bukatar kwarewa.
A amfani da fasahar dauri wajen kirkira, mutum na bukatar kwarewa a amfani da alburushin hannu da iya hada kaloli da sauransu, amma idan aka zo maganar fasahar kirkira ta zamani kuwa, ana bukatar kwarewa a amfani da wasu manhajoji ne wajen fitar da zanen da ake bukata.
Duk da cewa tun a shekarun 1960s ake amfani da fasahar intanet, mutane da dama suna taraddudi a kan salihahancinsa kamar yadda Kungiyar Artsper ta bayyana.
Amma wasu mutane suna ganin cewa kayayyakin zamani da ake amfani da su wajen fitar da zane-zanen suna saukaka aikin da yawa, sai ya zama tamkar cin banza kawai ake yi- amma ita Faithe ba ta amince da wannan fahimtar ba.
"Ina amfani da kwamfuta ce wajen kirkira ayyukana, amma suma dai zane ne kamar kowane irin zane. Amfani da kwamfutar ma wajen yin zanen ai yana bukatar kwarewa, kuma akwai wahala."
"Ina ta kara samun kwarewa saboda dadewa da na yi ina aikin, amma kuma yana da daukar lokaci musamman wajen fitar da na'ukan kitso saboda abubuwan da muke amfani da su kananan kai suke da su."
Nuna ƙwarewa
Faithe ta so ta zama kwararriyar mai hada kayayyakin kwalliya ce, amma ta koma bangaren zane-zane bayan wani malami ya ba ta shawara.
"Har na fara dinka kayan sawa, amma sai aka ban shawara cewa zan yi kyau da zane-zane," in ji ta, sannan ta kara da cewa, "bayan na kammala karatu, na fara aiki a matsayin mai zane-zanen sai na ga ba a yin ayyukan kirkira yadda nake so."
"Mu kuma masu aikin fasahar kirkira, muna bukatar samun damar kirkirar abin da zuciyarmu ta raya mana. Wannan ya sa na ajiye aikin, na koma aikin fasahar kirkira gadan-gadan," in ji ta.
Kamar sauran masu fasahohi, ita ma Faithe tun tana karama take da sha'awar ayyukan kirkira.
"Har yanzu ina da littattafai da na cika da zane-zane tun ina karama. Kuma a wancan lokacin na fi zana abubuwan da suka shafi kwalliya."
Sha'awar da take yi wa ayyukan kirkira na fasaha suna bayyana a duk wuraren da ta taba yin aiki, kafin ta ajiye aiki, ta koma harkar fasahar baki daya.
"Na taba karantarwa na wani dan lokaci, inda nakan zana duk wasu ayyukan da makarantar ta shirya za ta yi. Tun ina koyarwa abokan aikina suke fada min cewa me ya sa na zan rika yin zane na kudi ba? Ina tunanin tun asali ina da fasahar zane amma ban dauke ta da muhimmanci ba."
Sauyi daga Allah
Sai bayan da Faithe ta yi fama da wata jinyar mahaifinta ne, sai ta fara daukar fasaharta da muhimmanci.
"Mahaifina ya yi ciwon shanyewar gefen jiki sau biyar, wanda hakan ya sa ya rika zirya zuwa asibiti. Zama a asibiti da ganin yadda mahaifina yake wahala ne suka sa na fara zane,' inji ta, inda ta kara da cewa, "sai ya kasance mutane suna yaba duk abin da na yi a duk lokacin da na yada a kafofin sadarwa, wannan ne ya karfafa min gwiwa na fara mayar da shi kasuwanci."
A shekarar 2019 ce ta assasa kamfaninta mai suna Faithe with an E.
Yanzu kamfanin ya daukaka matuka, inda take hada riguna da jakukkuna da takalma da fastotci tare da buga suna ko wani sako a jiki.
Yawancin abubuwan da take hadawa suna kara nuna jajircewa, sannan suna dauke da tambarin malam bude mana littafi.
"Kwaron malam bude mana littafi yana alamta juriya da nasara," inji ta a tattaunawarta da TRT Afrika.
"Kamar kowane mutum, nima na sha fama, Wanda dole sai da na nuna juriya. Shi ya sa kamar yadda kwaron malam bude mana littafi ya samo asali daga kwaron katafila, hakan na nufin za a iya samun saukin bayan wuya."
Yanzu Faithe tana buga mujallar da rigunan da sauran kayayyaki ta hanyar fitar da zanen da za a daura musu a kwamfuta.