Donald Itsoga ya zabi aiki a waje inda yake jin dadin mu'amala da dazuka. Hoto / Courtesy

Daga Firmain Eric Mbadinga

Madalla ga ƙwarewar hannayensa, kayan ado masu kyawun mu'amala da Donald Itsoga ke samarwa na da yawa sosai da kuma jan hankali. SUn hada da kwanduna, huluna. tebura da ma dardumai na ciyawa - duk yana saka su da ganyen kwakwar manja.

Kuma Donald na yin ayyukansu na fasaha a fili. Ya zabi gabar tekun babban birnin Gabon, Libreville, wajen da aka sani da kayatarwa a lokacin faduwar rana da kuma iska mai dadin shaka.

Ga wannan ƙwararren mai kera kayan ado, wannan waje na ba shi damar ganin alakar da adam, gabar teku da tekun kanta, baya ga kasancewa tare da tsantsar duniya.

"Mafi yawan su a nan Gabon, idan akwai wani yanayi na murna ko bakin ciki, muna amfani da ganyen kwakwa don yin ado," in ji shi yayin tattaunawa da TRT Afirka.

"A wajena, shekaru shida da suka wuce na yanke shawarar ba zan sake amfani da ganyen kwakwar manja ba, sai dai na bishiyar kwakwa manya, kuma don kawata su sai na ke kitsa su," in Donald a yayin da ya sunkuwa yana shirya ayyukansa da sanyin safiya.

Ana yawan neman kayan da Itsoga ke samarwa a wajen tarukan jama'a. Hoto / Courtesy

Donald ya samu tunanin aiki da ganyen kwakwa ne bayan haduwa da wasu abokai biyu, daya daga Martinique, dayan kuma daga Togo.

Bayan doguwar muhawara, su ukun sun amince da muhimmancin tsantsar tsirrai da yadda kowanne bangare nasu yake zama ginshiki a rayuwa.

Amfani da ganyen kwakwa, wani bangare ne na daidaituwar tsarin rayuwa, duk sun amince da hakan.

Mai son sauraren wakoki, Donald ya yi tunanin yadda sana'arsa za ta kai shi sassan duniya, a ce yana dauke da lasifika a hannu, maimakon kitso wanda mafi aksari mata ne ke yi.

"Ban taba tunanin zan yi wannan aikin ba," in ji Donald. Sai dai kuma, sunansa na tsakiya, Daji, na iya bayyana yadda ya mika wuya ga kiran da dazuka suka yi masa.

Farashin adon da yake yi ya ta'allaka da irin taron da za a yi. Hoto / Courtesy

A lokacin auren gwaggonsa ne Donald Itsoga ya fara bayyana basirarsa ta ado daga ciyayi.

Ya bayyana cewa "Na yi niyyar yin wani abu a lokacin aurenta. Hakan ya fara ne a lokacinda na je yi wa wajen taron auren ado. Sai na saka ganyayyaki.

A lokacin da na ke yin hakan, na lura cewa mutane na kallon aiki tare da kayatuwa da shi. Wani abun ne ke kaiwa ga wani, kuma an yada hotunan adon a shafukan sada zumunta, bayan nan sai kawai na fara karbar bukatar mutane ta su ma a yi musu."

A yayin da ake ta samun yawaitar neman kayan adon, sai Donald ya yanke shawarar horar da wasu matasa wannan sana'a.

Shekaru uku bayan fara wannan sana'a, sai ya karbi bakuncin Jean-Paul Manga "Pablo", wanda tuni ya zama abokin hadin kansa.

Tare da sama da kashi 88 na dazuka da suka yi mata iyaka, Gabon na da dimbin bishiyu wadanda ake amfani da ganyensu wajen samar da abubuwa da dama, har ma magunguna ake yi da wasu.

Ana samun bishiyun kwakwa a yanki mai tsayin kilomita 950 na gabar teku.

Madalla ga ayyukansu na tsara wa da samar da kayan ado a cikin gidaje, abokan biyu sun bayyana cewa sun kubutar da kawunansu daga bukata.

"Game da wadannan ayyuka, ya ta'allaka. Ga bikin aure na gargajiya, misali, kana iya neman a biya ka saifa dubu dari takwas, (daidai da dalar Amurka 1,300) ko, dubu dari bakwai ko miliyan daya ko ma fiye da haka. Ya ta'allaka ga irin aikin da za a yi da kuma yawansa," in ji Donald, yana bayani kan kudin da suke karba.

Donald da abokin aikinsa Pablo suna nuna daya daga cikin ayyukansu. Hoto / Courtesy

Domin kasancewa mai gogayya da kuma aiki tukuru, DOnald da Pablo na da manufar cakuda al'adun gabon masu yawa a waje guda a cikin sana'arsu.

"Yau, iyali na murna, abokanmu, iyayenmu, kowa na alfahari. Tabbas Gabon ta samu ci gaban amfani da ganyen kwakwa. Yau, muna yin abubuwa da yawa, muna yin abubuwa masu muhimmanci sosai," in ji mai yin ado, yana murmushi.

TRT Afrika