Daga Pauline Odhiambo
Bisa ga dukkan alamu, burin samun zubin halitta mai ɗaukar hankali abu ne da ya game duniya, ya sanya bil adama ya ɗauki batun dirin mutum da matuƙar tasiri tsawon lokaci.
Misirawan dauri, Romawa da Girkawa an san su da yin amfani da sinadaran asali kamar zuma da aka kwaɓa da man zaitun don haskaka fata. Wasu sun yi gwaji da gaurayen Ma'u Kal da sinadarin farar dalma - ta Cerussa _ domin samun irin launin da suke buƙata.
A China, an fara al'adar ƙara wa fata haske fiye da shekaru 2,200 da suka gabata, da ya haɗa da dabaru kamar yin amfani da alli. Abin da ya sa yin bilicin ya zama batun da ke jawo ce-ce-ku-ce, musamman a Afrika, shi ne matsayin hakan a al'adance.
"Whitewashing", kalmar da ke nufin sauya sura ta yin amfani da na'ura mai ƙwaƙwalwa ko sauya launin fata ta ƙara haske, mutane da dama na masa kallon hakan na ƙasƙantar da mutanen da ba farar fata ba.
Hasalawa ba da gangan ba
Wani ra'ayi shi ne cewa Turawan Mulkin Mallaka sun kawo illolinsu ga mutanen da suka bautar,suna yayata ra'ayin cewa fata mai haske ita ce maɗaukakiya.
Hakan ya haddasa bazuwar yin amfani da abubuwan ƙara hasken fata a yankunan da aka yi wa mulkin mallaka.
Ra'ayin nan na samun gamsuwa da fatar da Allah ya halicci mutum da ita tun asali har yanzu bai gushe ba.
"Ba zan taɓa sayen kayan kwalliya daga kamfanin da wakilinsa ke tallata ƙarawa fata haske ba," wata mai sha'awar kula da fata, mazauniyar Rwanda ta sheda wa TRT Afrika.
Yayin da muhawarar ke ci gaba da kankama, wani ra'ayi a ɗaya ɓangaren shi ne, yadda mutum ya gabatar da kansa a idon duniya, ya kamata gabaɗaya ya zama zaɓi ne na ƙashin kansa.
"Akwai buƙatar mutane su kwantar da hankalinsu kuma su shafa wa mutanen da ke yin bilicin lafiya...Har wa yau, masu yini a cikin rana, su kan ƙara haske idan suka ɗan ɗauki lokaci a cikin ɗaki," inji wata mai amfani da dandalin sada zumunta.
Harkar Ƙara wa fata haske
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), fata mai haske ta riga ta karɓu a wajen mutane kuma al'ummomi da dama na mata kallon ita ce ƙoƙoluwar kyau.
A wasu al'ummomn, yadda zubin mutum ke ɗauke hankali, yiwuwar auruwar mutum, damarmakin samun aiki da kuma matsayin mutum ta fuskar zamantakewa da tattalin arziƙi, suna da dangantaka kai tsaye da launin fatar mutum.
A galibin lokaci hakan na shafar kimar matan da ba fararen fata ba a faɗin duniya, waɗanda su kuma saboda haka, sai su karkata ga amfani da sunadarai wajen ƙara wa fatarsu haske.
A watan Nuwambar shekarar 2023, Haɗaɗɗun Alƙaluma Sa Idon Kan Kiwon Lafiya a Afrika na Hukumar WHO sun nuna cewa yawan yin bilicin ya bambanta sosai, kama daga kashi 25% a Mali zuwa kashi 77% a Nijeriya. Zimbabwe (31.15%), Afrika ta Kudu (32%), Ghana (39%), Senegal (50%)da kuma Congo Brazzaville (66%) sune sauran ƙasashen da suke yawan yin bilicin.
Hakan, ya samar da harkar kasuwancin mai da allurar bilicin da ke bunƙasa a duniya wadda darajarta ta kai dalar Amurka biliyan $9.22 a shekarar 2023.
An yi hasashen kasuwar za ta bunƙasa zuwa dala biliyan $16.42 zuwa shekarar 2032.
Yanayin ƙwayoyin halittar gado
Ƙwararru na cewa ba abin mamaki ba ne fatar mutum ta yi haske haka kawai saboda dalilai da dama.
"A wajen wasu, cuta mai shafar launin fatar mutum za ta iya jirkita duhu ko hasken fata, inda adadin jirkitar ya danganta da shiga ranar mutum da kuma ƙwayoyin halittarsa na gado," Ayanda Masemola, wata likitar fata a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu ta sheda wa TRT Afrika.
" Wani lokaci, ƙwayoyin halittar da ke samar da abin da ke jirkita fatar sukan samu lahani ko kuma su ci karo da wani ƙwayar halittar gado da ba a saba ganin irinta ba, wacce za ta iya zamar da fata mai duhu ko kuma ta zamar da ita mai haske."
A wannan cuta, ana iya rasa launin fata a duka jiki ko kuma ya shafi ƙanana da manyan wasu sassan na musamman.
"Akan fi iya gano cutar a mutanen da ke da fata mai duhu saboda da bambancin haske da ke tsakanin fatarsu ta asali da kuma sassan da suka yi hasken," Masemola ya bayyana.
Tasirin magunguna
Wasu magungunan suma za su iya sauya launin fatar mutum.
"Magunguna za su iya jirkita yanayin fatar mutum, musamman tsakanin mutanen wasu ƙabilu. Mata sun fi saurin tasirantuwa da sauye sauyen da sinadarin homon ke haifarwa, haka kuma su ma mutane da ke da jinsin Asia da Afrika," Wandia Karige, mai sayar da kayan kwalliya a Kenya ta faɗa.
"Komai ya danganta ne da magungunan da ake sha,adadinsa da kuma wa'adinnsa."
Ƙwayoyin Steroids da hydroquinone da aka san suna jirkita launin fatar mutum, wani ɓangare ne na kayayyakin da kamfanonin sarrafa magunguna mafiya girma a duniya ke sarrafawa.
Karige ya bayyana cewa duk da dai ana amfani dawaɗannan magungunan ta halattacciyar hanya kuma dole sai da takardar sahalewar likita kafin a bai wa mutum su a ƙasashe da dama, a galibin lokaci, ana samun su ta ɓarauniyar hanya kuma a yi amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba.
Hakan gaskiya ne musamman a ƙasashen da yin bilicin ya samu gindin zama. Karige ta bayar da shawarar a dinga amfani da tabarau da kuma sanya tufafin da ke lulluɓe fata domin ba ta kariya daga hasken rana mai cutarwa.
Wasu magungunan da ke jirkita fata suna buƙatar sahalewar masana kiwon lafiya.
"Sauyi a launin fatar mutum zai iya taɓa ƙima da kuma ma ingancin rayuwar mutum gabaɗaya. Akwai buƙatar neman shawarwarin masana kafin yin wani gagarumin sauyi a kan fatar mutum, ta shaida wa TRT Afrika.