Tufafi a hukumance da tawagar Kenya suka sanya a yayin wasannin Olympics na Paris.      

Daga Kevin Momanyi

Hukumomi a Kenya sun sake bijiro da wani yunƙuri a karo na biyu don neman a samar da kalar tufafinta na ƙasa.

Jami’ai sun ce an yi kasafin kuɗin Kenya shilling miliyan 100, kwatankwacin dalar Amurka 775,000 domin samar da irin tufafinta na ƙasa.

Ana sa ran za a bayyana ire-iren tufafin da suka yi nasara a watan Oktoba, a cewar ma'aikatar al'adu ta kasar.

"Tufafin Ƙasa wani kaya ne da 'yan kasa suka amince da shi a matsayin sutura da ta haɗa duk wani bambance-bambance na al'adu, da asali, wanda ke ƙara martaba da kuma ƙimar ƙasa a idon duniya '' a cewar Kiprop Lagat daraktan ma'aikatar.

Rashin nasarar yunkurin farko na samar da tufafin ƙasar da aka shirya yi a shekarar 2004 ya biyo bayan rashin samun gudummawar jama'a sosai wanda ya kai ga daukar shawarar karshe daga mambobin kwamitin da aka zaba, a cewar jami'ai.

Muhimmiyar tambaya

An shigar da ‘yan Kenya domin a dama da su a wannan tsari, a cewar babbar sakatariyar ma'aikatar Ummi Bashir.

Jami'ai sun shaida wa 'yan majalisar doƙoki ta kasar cewa, idan aka yi la'akari da bambancin al'adu da ake da su a Kenya, za a iya gabatar da tutafi iri daban-daban sabanin guda ɗaya kawai.

''Ba lallai ba ne, mu iya samun tufafi guda ɗaya na ƙasa, amma muna iya samun iri daban- daban da za su iya wakiltar bambance-bambancen da muke da shi na al'adu a ƙasar nan,'' in ji Lagat.

Ra'ayoyi sun bambanta game da wanna shirin. Wasu dai na nuna shakku kan ko shi ne muhimmin abu da ya kamata a mayar da hankali akai a daidai lokacin da al'ummar Kenya ke ci gaba da kokawa kan matsalar tsadar rayuwa.

''Shilling ɗin Kenya miliyan 100 aka ware don samar da kalar tufafi na Kasar bayan rashin nasarar da aka samu a baya.

Shin, wa zai iya min karin bayani tare da bayyana min alfanun da wannan yunƙuri zai yi wan talakan Kenya?

Muna da manyan batutuwan da ke bukatar a magance su," kamar yadda Martin Wachira, wani mazaunin babban birnin Nairobi, ya shaida wa TRT Afrika.

Arzikin Al'adu

"Wannan tunani da gwamnati ta yi yana da ƙyau. Muna buƙatar tufafi da zai nuna irin arzikin al'adunmu a Kenya,'' in ji Wilson Sampeua mazaunin gundumar Nakuru.

Kazalika maƙwabciyar kasar Tanzaniya ita ma ta yi ta ƙoƙarin samar da wani tsari na suturar al'adun kasa, inda har yanzu yunƙurin gwamnati ya gaza samun sakamako mai ƙyau.

Wannan yunƙuri dai ya samu shawarwari daga kusan masu ruwa da tsaki 2,450 da mazauna daga sassa daban-daban a kasar zuwa ga kwamitin da aka kafa don sa ido kan samar da suturar al'adu na kasa.

Sauran kasashen yankin gabashin Afirka da suka haɗa da Ruwanda da Burundi da kuma Uganda, ba su da wata sutura ko tufafin ƙasa a hukumance ba.

Duk da haka, ana sanya wasu tufafin gargajiya na ƙabilu daban-daban a matsayin tufafi na ƙasa a manyan taruka na al'adu da na ƙasa baki ɗaya.

TRT Afrika