Baje kolin al'adun Afirka a wajen Taron Diflomasiyya na Antalya. Hoto: TRT Afrika

Daga Coletta Wanjohi

Taron Diflomasiyya na Antalya ya samu halartar shugabannin ƙasashe da na gwamnatoci da ministoci da jami'an diflomasiyya da shugabannin kasuwanci da malaman jami'o'i da masu nazari da bincike, inda aka gabatar da ƙananan taruka da dama da baje koli kan abubuwan da suka shafi siyasa da tattalin arziki da ilimi da kuma musayar al'adu.

Baje kolin al'adun Afirka a wajen Taron Diflomasiyya na Antalya. Hoto: TRT Afrika

Taron wanda aka yi a birnin Antalya da ke gaɓar Tekun Bahar Rum ya samu halartar wakilai daga ƙasashe fiye da 140 - mafi yawansu daga Afirka.

An yi baje kolin kayayyakin al'adu da suka shafi na sassaƙa da saƙam tare kuma da yin taron ƙasa da ƙasa.

Baje kolin al'adun Afirka a wajen Taron Diflomasiyya na Antalya. Hoto: TRT Afrika

Taron Diflomasiyya na Antalya ya samar da damar da aka yi musayar al'adu a tsakanin mutane daga sassan duniya daban-daban, ta hanyar nunin kayayakkin yankuna.

Baje kolin al'adun Afirka a wajen Taron Diflomasiyya na Antalya. Hoto: TRT Afrika

An nuna kayayyaki da suka shafi tukwanen ƙasa da gumaka da saƙaƙƙun tufafi da sauran su na ƙasashen Afirka daban-daban.

Baje kolin al'adun Afirka a wajen Taron Diflomasiyya na Antalya. Hoto: TRT Afrika

Kayayyakin al'adu da dama da aka nuna sun taimaka wajen fayyace kyakkyawan tsari na al'adu da nahiyar ke da shi.

Baje kolin al'adun Afirka a wajen Taron Diflomasiyya na Antalya. Hoto: TRT Afrika

Baƙi da dama sun ɗauki lokaci wajen kallon baje kolin Taron Diflomasiyya na Antalya.

Baje kolin al'adun Afirka a wajen Taron Diflomasiyya na Antalya. Hoto: TRT Afrika

An gudanar da ƙananan taruka da tattaunawa da dama da kuma baje kolin kayan al'adu da na fasaha a wajen Taron Diflomasiyyar na bana.

TRT Afrika