Wata irin rawa da mutanen kabilar Luguru suke yi a Tanzania tana ta yaduwa a shafukan sada zumunta inda masu amfani da TikTok da dama suka rinka yin bidiyo suna yin rawar ta Chunda.
Ana iya yin rawar a kowane lokaci amma an fi yin ta ne a lokacin girbe amfanin gona da kuma bukukuwan karshen shekara.
Ana yin wakoki daban-daban a kowane biki amma rawar iri daya ce - inda ake buga kafafu da karfi sai kuma matasa maza suna waka.
Chunda na nufin "wurin da ka tsaya" a harshen Luguru saboda masu rawar suna tsayawa ne a wurin da suke tsaye idan suna rawar
Matasa maza ne ke jagorantar rawar inda wasu daban ma za su iya shiga, kamar yadda Rajab Almasi ya bayyana, shugaban kungiyar masu rawa ta Twarikadiria.
"Muna kiran Allah sosai a cikin bidiyon kuma ba a shan giya," kamar yadda ya yi bayani.
Rawa ce da ake yi ba tare da wata ganga ba ko wani kayan kida ba, sai dai buga kafafuwa da kuma magana da muryoyi masu karfi wadanda suke fitar da wani sautin waka.
Masu rawar akasari na yin da'ira, sai dai ana kara barin sarari ko da za a samu adadi mai yawa na masu rawar. Jagoran rawar a ko da yaushe yana a tsakiyar da'irar da ake yi.
Rawar Chunda na hada matasa da dattawa wuri guda, kamar yadda Chedieli Senzige ya bayyana, wani malamin fasaha.
"Wannan rawar ta Chunda ba wai dari bisa dari ta al'ada ba ce, amma an hada ta da zamani da tsohuwar al'ada," kamar yadda ya yi bayani.
Masu rawar za su iya saka ko wadanne irin kaya, inda buga kafar da suke yi ita ce wani abu daya da ke hada kan masu rawar.
Yankin na Morogoro wanda aka fi sani da "Mji kasoro bahari", na alfahari da wasu raye-rayen da suka hada da Mangaka da Ngokwa wadanda su ma ake yin su a lokutan bukukuwa daban-daban.