Daga Pauline Odhiambo
Akwai bidiyoyi da dama a shafin YouTube waɗanda ke bayani dangane da dalilin da ya sa zanen da Leonardo da Vinci ya yi na Mona Lisa ya fita daban. Ta hanyar amfani da tsarin binciken na Google, shafin na Google ɗin na fito da kusan shafuka 20.
Mai zanen nan na Nijeriya Ibrahim Bamidele ya yanke shawarar gudanar da bincike domin gano dalilin da ya sa matar da aka zana wadda ba ta da girar ido ke jawo miliyoyin masu yawon buɗe ido na zuwa gidan tarihi na Louvre a duk shekara.
Ta haka ne aka samu "Black Lisa", inda Bamidele ya kwaikwayi zane mafi shahara a tarihi.
Ga idon da ba a horar da shi ba, zanen da matashin mai shekara 32 ya kwaikwaya na da Vinci idan mutum ya kalla da farko zai iya zame masa bambaraƙwai a ido. Idan mutum ya ƙara mayar da hankali ya kalla da kyau zai ga ya fito da wani abu da mutum ya sani - tamkar irin "murmushin Mona Lisa".
"Ina daga cikin mutanen da ba su taɓa fahimtar wani abu na daban da Mona Lisa ba, inda na yi tunanin hanya ɗaya ta yin hakan shi ne na zana ta," kamar yadda Bamidele ya shaida wa TRT Afrika.
"A lokacin da nake zanata, daga nan ne na fahimci wane irin zane ne aka yi. Da Vinci ya yi ƙoƙarin fitar da abubuwa a zanen ba tare da ya yi amfani da kayan fentin da ake amfani da su sosai ba a yau.
Tabbas, 'Black Lisa' ta Bamidele ta wuce batun sha'awar mai zane kawai. Haka kuma ba wai batun zaɓar launi bane ko kuma wakiltar wani ɓangaren mutanen duniya.
"Ana mu'amula da mutane daban-daban dangane da launin fatarsu. Wannan ba wani lamari bane na wariyar launin fata, amma wani abu da ya shafi launin fatar 'yan Afirka," kamar yadda mai zanen mazaunin Legas ya bayyana.
Ɗaya daga cikin abokan Bamidele na kusa ne suka ja ra'ayinsa - wanda wani ɗan Afirka ne wanda ake saka ayar tambaya dangane da launin fatarsa sakamakon zabaya ne.
"Idan launin fatarka ya sha bamban da wanda kake da shi yau fa? kamar yadda ya tambaya.
"Za ka yi rayuwa kamar yadda kake yin ta a yau, ko kuma za ka yi ta daban?
"Za a kula da kai da kyau ko kuma nuna maka tsananin bambanci?"
A matsayinsa na wanda yake yi wa duniya magana ta hanyar zane, burin Bamidele shi ne ya yi wani zane wanda zai "bayar da ƙwarin gwiwa ga mutane domin su so juna duk da bambance-bambancen da ke tsakani".
A wurin da matasa da yawa suke gwagwarmaya domin sanin amfaninsu a rayuwa, Bamidele tun daga farko ya san cewa duniya na so ya zama mai zane.
Ayyukan zane-zanensa masu ban sha'awa, waɗanda ke nuna abubuwa na ruhaniya sun bambanta da yanayin yadudduka na Afirka, waɗanda ake nuna su a wurare a Nijeriya da Birtaniya da Amurka.
An sayar da zanensa da dama kan dubban daloli kowane ɗaya, sai dai Bamidele yana sane da cewa tafiyar zama shahararren mai zane na da ƙalubale iri daban-daban.
"Zama mai zane ba abin alfahari bane a lokacin da nake tasowa, ko sayen kayan zanen abu ne mai wahaka. Ana kallonsa a matsayin wani abu mara amfani maimakon wata abu da ya kamata a ƙware a kai," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika. " Sai dai ina da yaƙinin kullum zan yi abin da nake so."
Tufafin Afirka
Sakamakon zaburarwa da al'ardarsa ta Yarabawa ta yi masa, Bamidele ya zaɓi ya nuna kyawawan al'adun Nijeriya a cikin fasaharsa, wanda ya fara da amfanin da tufafin Afirka
Yayin da yake karatun jami'a, ya yi zane ta hanyar gauraya tufafin Afirka daban-daban a kan zanen, a lokacin yin hakan, sai ya gano basirarsa.
"Na samu kayayyakin zane-zane iri-iri a lokacin da nake makaranta, sai dai na samu Ankara (Tufafin Afirka), wanda ya fi burge ni saboda ina son ganin abubuwa iri-iri a kusa da zanena," kamar yadda mai zanen ya bayyana.
Pablo Picasso da Georges Braque su ne aka sani soma irin wannan nau'in zanen a 1912.
"Amfani da Ankara a al'adata na da matuƙar amfani. Waɗannan tufafin na al'ada ne kuma suna da kyau ta ma'anar cewa iyali ɗaya za su iya sanya kayan da aka yi daga yadi iri ɗaya inda za su iya saka su yayin wani biki domin bambanta kansu da sauran baƙi," in ji Bamidele.
Yawancin zanen da Bamidele yake yi, yana zana mutane waɗanda a saman kansu akwai wani zagayayyen abu wanda zai nuna wata alama ta ruhanai.
Wasu daga cikin ayyukansa waɗanda suka haɗa da "Divinity da "Madonna in Thought" na magana ne kan muhimmancin kasancewa tare da duniyar ruhanai.