Daga Abdulwasiu Hassan
A wannan mako ne jihar Legas da ke yankin Kudu maso Yammacin Nijeriya ke karɓar baƙuncin gwanayen mawaƙan baka da marubuta da sauran masu harkar nishaɗantarwa a taron bikin wakoƙin baka na ƙasa da ƙasa na Legas na shekara-shekara.
Bikin na kwanaki huɗu, wanda aka soma daga ranar Laraba, ya haɗa shirye-shirye na karatuttuka da wasannin kwaikwayo, da kuma baje kolin kayayyakin fasaha da dai sauransu.
Ana gudanar da taron ne a Cibiyar Mike Adenuga da ke Ikoyi a jihar ta Legas, sannan taken bana ya mayar da hankali ne kan ''bin kwakwafi da gano sabbin abubuwa,'' a cewar wanda ya shirya taron Efe Paul-Azino.
"Bikin na sake tabbatar da 'yancinmu na neman ilimi ba tare da tasirin ƙasalandan ɗin siyasa ko addini da kuɗi ba," in ji Efe a cikin wata sanarwa da ya fitar.
"Yana sake tabbatar da sadaukarwarmu a duniyar da fasaha da kimiyya suke taka rawa zuwa ga makomar da za karfafa mana hanyoyin bincike da tambayoyi da kuma fahimtarmu.''
Kawar da duk wani tarnaƙi
Bakin da masu nishaɗantarwa sun fito ne daga yankuna daban-daban wanda ke nuna an kawar da duk wani tarnaƙi, ba kawai a tsakanin fannonin ilimi ba har ma a tsakanin al'adu da mutane, in ji Paul-Azino.
Wasu daga cikin manyan bakin da ake sa rai a wajen bikin sun haɗa da Wana Udobang, da Mahogany Browne, da Obii Ifejika, da Zaynab Iliyasu Bobi, da Ameerah Shabzz-Bilal, da Kamnelechukwu Susan da kuma Helena Lewis.
An shirya haska wasu shirin binciken ƙwaƙwaf na bidiyo guda biyu a taron. Masu suna David Odiase’s Benin Did Not Die da kuma Kola Tubosun’s Ebrohimie Road: Na gidan adana kayan tarihi game da rayuwar wanda ya lashe kyautar Nobel na farko na Afirka a fannin fasaha.
Kazalika wani marubuci mai suna Umar abubakar Sidi zai karantawani littafinsa mai suna The Incredible Dreams of Garba Dakaskus, inda zai hada kai tare da Elizabeth Johnson don tattauna wa akan littafin.
Kimiyyar yanayi
Haka kuma, za a kuma gudanar da zaman tattaunawa a bikin da Niyi Osundare, tare da Amy Shimson-Santo, da Nninmo Bassey da kuma Deji Toye kan maudu'in: Shin kimiyyar yanayi tana buƙatar sabon harshe?
Za a kuma karrama marubuciyar Nijeriya, Jumoke Verissimo, wacce ke koyar da fasahar rubuce-rubuce a Jami'ar Metropolitan da ke ƙasar Toronto da lambar yabo ta musamman.
An kirkiro bikin wakokin baka na kasa da kasa na Legas a shekarar 2015 kuma ana kan gudanar da shi a duk shekara.