African Yuva ya kera kaya ga jarumar Hollywood Lupita Nyong'o da ma wasu masu sanannu a Afirka: Hoto: African Yuva

Daga Pauline Odhiambo

A kasuwancin ɗinka tufafi, abin da kake saya sau da yawa ba shi ake kawo maka ba, amma idan ana batun tufafin Afirka, babu wanda ya isa ya jarraba haƙurinka kamar tela.

Waje ne da ake samun tsaiko sosai wajen baiwa mutane kayayyakinsu na gargajiya, mai kasuwanci 'yar kasar Kenya Beverlyn Mawia Muthengi ta ga babbar damar amfana da wannan matsala tare da samar da kayan Afirka ɗinkakku da za a iya saka su a wajen kowanne irin taro ko sha'ani kuma a kowanne lokaci.

Kayanta ɗinkakku da sai dai a ɗauka a saka kawai, sun kawata jarumar Hollywood Lupita Nyongo'o da wasu mashahurai da dama da ke da mabiya da yawa, waɗanda suka sanya kayan nata tare da ba ta dama yin fice.

"Na gano cewa mafi yawan mutane na da matsalar yarda da tela. Mutane a Nairobi za su iya faɗa maka nasu labarin na yadda tela ya kunya ta su. Babbar matsala ce a a ƙsashen Afirka da dama," Beverlyn ta shaida wa TRT Afirka,

Ta kara da cewa "'Yan Kenya da dama na sayen kayayyaki a ƙurarren lokaci. Za mu iya sanin labarin za a yi biki tun watanni huɗu baya, amma sai mu fara sayen kayan da za mu saka kwanaki kaɗan kafin ranar bikin, wanda hakan ke sanya da yawa daga cikin mutane ke samun matsala da teloli."

Da yawan masu sayar da tufafi ta yanar gizo na yin alƙawarin kai kaya masu kyau da ƙayatarwa, amma masu saye sai su ƙarƙare da karɓar kayan da ba su suka tsammaci karɓa ba.

Kayan masu babban jiki na da jerin tufafin African Yuva. Hoto: African Yuva

Salon Afirka

Kafin ta fara kasuwancinta, beverlyn ta kasance tana ajje hotunan nau'ikan kayan sawar Afirka ta shafin Pinterest, ta dinga adana bayanai na nau'ikan tufafi da dabaru a shafin na sada zumunta inda take kuma neman telan da zai iya ɗinka irin wannan kayan.

"Kamfanin African Yuva ya fara aiki da saƙar ƙwarashi da ake kira Yarn Yuva. Yuva na nufin gida a yaren Turkanci, yarn a yaren Indiya," in jita. "Na fita sayen zaren saƙa wata rana sai na haɗu da wani tela wanda ke ɗinka kaya da yadikan Afirka. Na nemi ya ɗinka min buje manya-manya da yadikan Afirka ta yadda zan haɗa su da rigunan da na ke hada wa. ta haka ne aka kafa Yuva a 2017."

Beverlyn ta yada hotunan rigunan da ta kammala a shafukanta na sa da zumunta inda ta wayi gari tana da mabiya 8000 bayan wasu 'yan makonni.

"A wannan lokacin ne na fahimci cewa na fara wani abu, ganin cewa mutane 800 sun yanke shawarar bibiyata na nuni da cewa akwai bukatar tufafin Afirka masu ƙayatarwa, tabbas wannan ya taimaka min wajen bunƙasa kasuwancina,' in ji ta.

Ta fara tsara tufafi ta hanyar amfani da ƙwaƙwalwarta, inda a 2018 ta fitar da jerin kayayyakinta a karon farko duk da ta fuskanci ƙarancin kuɗaɗe. Abokiyar Beverlyn ta tsara dukkan kayan, wata kawar tata kuma ta ɗauki hotunan kayayyakin tare da yaɗa su a shafukan sada zumunta na African Yuva.

Akwai kayan Afirka da dama da aka samar a yanayi mai kyau. Hoto: African Yuva

A rukunin kayyakinta na 2019, Beverlyn ta samu kuɗaɗen da suka ishe ta har ta ɗauki hayar mai ɗaukar hoto kwararre, har ma da mai yin kwalliya. Tana iya tuna yadda kabot ɗin ajiye kayanta ta karye saboda nauyin kayan da aka ɗora mata na tufafin Afirka da suke jiran a ɗinka su. Kayan da aka gama ɗinka wa na samun karɓuwa nan da nan, kuma mutane na aiko da buƙatar za su saye su don saka wa.

Hada wa da kayan masu manyan jiki

Ta ce "Rukunin kayayyakinta na 2019 na da salo a nau'ika da yawa ciki har da kayan da muna ci gaba da sayar da su. Mun ɗauki hotunan dukkan kayan da muke da su ta yadda masu saya za su tabbatar da abinda suka saya ne aka kai musu gida, kuma ba a yaudare su da tallan ƙarya ba a yanar gizo."

Haka zalika kayan da aka samar na 2019 sun ja hankalin sabbin kwastomomi sosai daga Amurka da faransa, wasun su ma kamfanoni ne da suka sayi kayan beverlyn tare da ajiye su.

"Babban matakin da na ɗauka zuwa yau shi ne kafin na saki sabon salo na ɗinki, sai na duba ko akwai waɗanda za su dace da mata masu ƙiba ko kuwa a'a," in ji ta. "Akwai iyalin da suka taimaka min saboda sun gamsu da inganci da kai musu kaya a kan lokaci, kuma hakan ya taimaka min wajen riƙe aboka hulaɗata."

Beverlyn na kokarin ganin ta saki sabbin rukunin kayayyaki sau uku a kowacce shekara tun bayan fara kasuwancin, amma a 2020, annobar Covid-19 ta kawo cikas ga nasararta.

Lokacin annobar covid-19 kayan African Yuva sun yi tasiri sosai. Hoto: African Yuva

"Na yi bincikena tare da gano cewa mutane na son sayen kayan sawa da za su dinga saka wa a lokacin da suke tsare a wuraren kula da masu corona, sai na mayar da hankali wajen dinka dogayen kaya, takunkumin rufe fuska da sauran tufafi," in ji ta.

"A watan Oktoban 2020 na dauki ma'aikacina cikakke na farko. na ji dadi kuma abin albarka ne ka dauki ma'aikaci a lokacin covid-19 lokacin da ya rasa aikin yi."

A yanzu Beverlyn na yin takama da ma'aikata 14 ciki har da teloli da manajan dinki da ke gudanar da kamfanin.

Matsayin shiga Hollywood

“Dinkina ya samu kwarin gwiwa ne daga yadda mutane suke so su yi kayu su kuma ji dadi a koyaushe, don haka babban burina shi ne kirkirar wani tufafi da zai ringa yi wa mata kyau a kowane irin biki,” a cewarta.

African Yuva sun mayar da hankali ga kayan da ke jan hankali a jikin mata.' Hoto: African Yuva

A 2021, Lupita Nyong’o ta sanya daya daga wata falmaran da Beverlyn ta dinka a lokacin da aka yi hira da ita a wani fitaccen shirin talabijin a Amurka. Da dama daga taurarin dake fitowa a wasan kwaikwayo da manyan kamfanoni suke nunawa a duniya, sun saka kayan da Beverlyn ta dinka.

“Da farko na so in dinka wa Lupita wasu fitinannun kaya, amma sai ta zabi wata riga da aka riga aka dinka wacce ta dace da irin abin da ta ke so. Shaidar da muka samu daga taurarin duniya da ke saka kayan da muka dinka ya taimaka mana wajen kasancewa fitattu.”

“Mafi yawan kamfanoni suna yi wa mata dinkin da za su burge maza, amma a matsayinmu na ‘yan Afirka, muna dinky ne don adon mata,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika. “Batu ne na samar da wani tufafi da zai bai wa mata damar su burge juna kuma su yaba wa zabin juna yayin da ake gina kowa ta hanyar dinki da kawa.”

TRT Afrika