Daga Mazhun Idris
"Akwai buƙatar mu naƙalci gilas," kamar yadda shugaban Apple, marigayi Steve Jobs ya shaida wa jagoran tsara na'ura na kamfaninsa, Jony Ive, a shekearar 2006.
Steve Jobs ya yi suna wajen mayar da hankali kan gilas, wanda abu ne da yake da ƙayatar da idanu, kuma ake iya amfani da shi a fannoni da dama, tun shekarun da suka kai 4,000 da suka wuce.
Ya taɓa faɗa wa shugaban kamfanin Corning Inc, cewa "Ka da ka ji tsoro, za ka iya wannan aikin." Martanin Steve ya zo ne bayan da Wendell ya ce ba zai yiwu ba a samar da gilas mai ƙarfi samfurin 'Gorilla Glass' cikin wata shida, domin a ƙere da kuma fitar da sabuwar iPhone.
Ƙasa da shekaru ashirin daga lokacin can, fasaha ta yi gaba matuƙa, kuma duniya ta koma wani sabon zamani da ake damuwa da muhalli, inda gilashi ya zamo abin-so don maye gurbin roba a duk lokacin da aka samu dama.
Wannan sauyi ba wai don ƙawa ake yin sa ba, saboda yana da tushe mai zurfi kan yadda ake iya amfani da gilas a fannonin rayuwa, kamar gine-gine, abubuwan ƙunshe kaya, kayan lantarki, motoci, sadarwa, da kayan masarufi.
Wannan yunƙuri na neman alkinta muhalli ya haifar da bincike don samo sabbin kayayyakin da ake iya sabuntawa. Ɗaya cikin waɗannan abubuwan zamani shi ne nau'in gilas da ke rage cin makamashi, wanda ake gini da shi, kuma wanda yake rage datti da ke cutar da muhalli.
Dr Hadi Ibrahim Bello, ƙwararre ne kan fasahar gilas da sinadarin silica, wanda ke Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria, a Nijeriya. Ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "Girman tattalin arziƙin masana'antar gilas yana ƙaruwa da sauri sakamakon yadda ake ƙara son karatu dangane da ilimin gilas, da kuma neman kayayyaki masu kare muhalli."
Shu'umin abu
A matsayinsa na mamban babbar cibiyar bincike kan fasahar gilas ta Nijeriya, kuma wanda ya kwashe sama da shekaru 20 yana harkar, Dr Bello yana kira gilas abu mafi karɓar sauyi don amfani a sassan rayuwar ɗan-adam.
Wani misali shi ne masana'antar ƙera motoci tana samun gagarumin ƙaruwar buƙatar gilashin mota na zamani, wanda ke zuwa da shimfiɗar kariya, wadda ke sauƙaƙa zafi da hasken da ke shiga cikin mota.
Dr Bello ya ce, "A masana'antar maƙunshin kayayyakin masarufi da masana'antar lafiya, tuni gilas ya maye gurbin roba a kayayyakin amfani, sakamakon sauƙinsa da rashin gurɓata muhalli".
Annobar da duniya ta fuskanta ta ƙara yawan buƙatar kayayyakin gilas a fannin masana'antar haɗa magunguna da kiwon lafiya.
Haka nan gilas, yana da farin jini a sauran sassan rayuwa, kamar bangon gini, da kayan kicin, da kayan ɗakin binciken kiwon lafiya.
Yayin da duniya ke nuna damuwa kan cutar da muhalli da roba ke yi saboda jinkirinta na narkewa a cikin ƙasa, kamfanoni suna juya akala zuwa ƙera kayayyakin da ba su laharta muhalli da yanayi.
"Cigaban da aka samu baya-bayan nan a ƙera gilas kamar gilas nau'in fiberglass, ya janyo samuwar kayayyaki masu inganci sosai kamar shahararren gilas ɗin 'Gorilla Glass' na wayar zamani, da kuma samfurin kwanan nan mai suna 'Tiger Glass'," in ji Dr Bello.
Masana'antar gilas
A kasuwannin duniya, abubuwan da ke shafar hada-hadar nau'in gilas da ake manyan ayyuka da shi, da wanda ake ayyukan gida, sun haɗa da inganci da farashin kaya. Duka waɗannan suna dogara ne kan fasahar ƙera gilas, da yanayin ƙerawar, da kyawun kasuwa.
Cewar Dr Bello, "A taƙaice, shi gilas wani abu ne mai garai-garai wanda ake iya malƙwayawa. Ana yin sa daga narkakken yashin silica wanda ake sanyayawa cikin sauri don ya yi ƙarfi. Amma kimiyyar ƙera gilas tana da tsauri".
Kimiyyar sinadari da fasahar ƙera gilas tana duba yanayi, da ƙarfin da ake buƙatar gilashin da za a ƙera ya yi, don tabbatar da dacewar kayan da za a haɗa gilas ɗin da shi, kafin ma a fara narkar da yashin.
Sauran muhimman abubuwan da ake lura da su wajen ƙera gilas sun haɗa da, shirya tanderun wuta, da iza wuta, da ririta makamashi, da kayan aiki, da kula da aikin, wanda duka suke buƙatar wuri da kayan aiki na musamman.
Duk da ƙarfin gogayyar kayayyakin gilas na ƙasashen waje, saboda bambancin farashi da inganci, gilas ɗin da ake samarwa a gida a kasuwannin Afirka suna da daraja a fannin fasali da tasiri ga al'adu.
Damarmaki a Nijeriya
Mafi girman masana'antar gilas a duniya tana manyan cibiyoyin masana'antu da ke Amurka, da Turai da Asiya.
Musamman nahiyar Asiya, inda nan ne ake samun ƙwararrun ma'aikata cikin kuɗi ƙalilan, wanda hakan ke haifar da samuwar tarin masana'antun ƙera gilas a yankin.
Dr Bello ya yi amanna cewa Afirka na buƙatar shawo kan ƙalubale, musamman na samuwar fasaha, da ƙwararrun ma'aikata, kafin nahiyar ta iya cin moriyar inganta tattalin arziƙi ta fannin samar da gilas.
A cewar wani rahoto a 2021 wanda shafin https://www.reportlinker.com/ ya wallafa, "Ƙarfin Afirka wajen samar da kwalabe da mazubin gilas ana sa ran zai haɓaka ya samu ƙaruwa da ninkin da ya kai kashi 5.67% tsakanin 2021 da 2026".
Ana ta'allaƙa wannan kan gagarumin zuba jarin da ake a fannin ƙera kayayyakin haɗa magani, kamar mazubin gilas, da maƙunshin gilas, musamman wajen yaƙi da annobar Covid-19.
Bincike a Nijeriya ya nuna cewa sassa da yawa na ƙasar suna da tarin kayayyakin haɗa gilas kamar yashin silica, da dutsen quartz, da limestone, da feldspars, kaolin, da ɓurɓushin gilas.
Wani yanki a jihar Ondo ta Nijeriya, yana da ƙiyasin tan biliyan uku na yashin silica. Duk da wannan, ƙasar ta dogara ne kusan kacokan kan gilas da ma yashin silica da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje.
Jami'ar Ahmadu Bello Zaria ta kasance tana gudanar da kwas kan fasahar ƙera gilas, tun shekarun 1970, kuma tana ƙoƙarin cike gurbin ƙarancin ƙwararru kan fasahar. Wasu 'yan tsirarun jami'o'i su ma suna saka ƙaimi wajen shiga harkar.
Dr Bello ya ce, "Ya ɗauke mu shekaru 40 kafin mu kafa sashe mai zaman kansa don nazarin fasahar gilas da silica a matakin digiri. Wannan ya faru ne a 2017. A yanzu muna da tanderu na zamani mai aiki da gas, da mai aiki da lantarki wanda ake iya ɗauka."
"Duk da ƙarancin ikonmu, ɗalibanmu suna samun horo kan ƙera gilas, da samar da kayan cin abinci na gilas, da kayan ɗakin binciken kimiyya, da kayayyakin zane. Amma muna ƙoƙari sosai don haɓaka fannin ilimin zamani, da aikin ƙirar gilas."
Ɗalibai a jami'ar suna samar da kofunan gilas, da mazubi, da kayayyakin binciken kimiyya. Kuma suna nazartar salon sarrafa gilas da sinadaran yin gilas, inda suke naƙaltar salon zamani da na al'ada.