Daga Emmanuel Onyango
Yadda Paul Kagame da jam'iyyarsa ta Rwanda Patriotic Front suke tara dimbin jama'a a wuraren taron kamfe dinsu, na shan bamban da yadda manyan abokan hamayyarsa biyu suke tara tsirarun mutane.
Paul Kagame da jam'iyyarsa sun shiga zaben ne da yakinin cewa zai yi nasara a karo na hudu. Za a yi Babban Zaben Kasar ne a ranar 15 ga Yuli, inda za a zabi Shugaban Kasa da 'yan majalisa.
Hukumar Zaben Kasar wato National Electoral Commission ta tantance sama da 'yan takara 500 da za su fafata domin neman kujerun majalisar kasar guda 80.
Akwai masu kada kuri'a kusan miliyan 9.5 a kasar, kamar yadda alkaluman hukumar suka bayyana.
A wannan karon ma, Kagame zai sake fafatawa ne da sanannun abokan hamayyarsa, wadanda dukansu ba su samu kashi biyu na kuri'un wancan zaben na Shugaban Kasa ba. Amma a wannan zagayen, jam'iyyun adawa suna tunanin su tabuka sama da abin da suka yi a shekarar 2017.
'Yan takara takwas ne suka nemi takarar domin fafatawa da Kagame, amma Hukumar Zaben bayan ta tantance su, sai ta amince da biyu, ta yi watsi da sauran.
'Yan takarar da aka cire
An cire sauran 'yan takarar ne saboda dalibai daban-daban, cikinsu har da babbar abokiyar hamayyar Kagame mai suna Diane Rwigara, wadda hukumar ta ce ta gaza gamsar da ita cewa ba ta da wani laifi a hukumance.
Haka kuma an ce ta gaza wajen gamsar da hukumar cewa lallai ita 'yar asalin Rwanda ce.
Sauran 'yan takarar guda biyu da aka amince da takararsu su ne Frank Habineza da Philippe Mpayimana.
"'Yan takarar uku dukkansu suna da labarai na gwargwarmaya. Dukansu suna da ta cewa a game da gwargwarmayar gyara kasar bayan yakin kisan kiyashi," inji Eric Ndushabandi, farfesan kimiyyar siyasa a Jami'ar Rwanda.
Paul Kagame:
Kagame mai shekara 66 shi ne ya jagoranci fafutikar kawar da yakin kisan kiyashin da aka yi a kasar na shekarar 1994. A kisan kiyashin an kashe sama da mutum miliyan 1. Kagame ya kasance Shugaban Kasar tun daga shekarar 2000 zuwa yanzu.
Kasar mai mutum miliyan 14 ta samu cigaba a siyasance da abubuwan more rayuwa a cikin shekara 20 din nan, duk da cewa ana kushe yadda ake zargin gwamnatin da tauye hakkin abokan hamayyarta a siyasance.
A duk lokacin kamfe, Shugaban Kasar yana yawan nanata kira ga 'yan kasar da kada su kauce daga aikin da ake yi na sake gina kasar bayan yakin kisan kiyashin da aka yi, inda yake bayyana kansa a matsayin wanda ya fi cancanta da cigaba da gyara da ya faro.
Samun tabbacin nan yana da matukar muhimmanci a wajen masu kada kuri'a musamman ganin yadda suke fargabar makomar kasarsu wadda take yanki mafi fama da matsaloli a nahiyar.
"A fahimtar 'yan Rwanda da dama, muna tunanin wanda zai iya cigaba da sake gina kasar shi ne wanda ya faro aikin wato Kagame," inji Ndushabandi.
Ya kara da cewa, "Ba na shakkar zai lashe zaben. Ya faro wasu muhimman ayyuka ne da ya sa mutanen Rwanda da dama suke tunanin babu wanda zai iya cigaba da aikin sai shi."
Idan ya samu nasara, dokar kasar ta ba shi dama ya sake yin zango biyu ne bayan gyarar fuska da aka yi Kundin Tsarin Mulkin kasar a shekarar 2015. Amma gyarar ta takaita zangon Shugaban Kasa zuwa shekara biyar ne daga shekarar 2024.Babban abokin hamayyar Kagame, Frank Habineza yana kamfe a Gabashin kasar.
Frank Habineza:
Jagoran Jam'iyyar Green Party Frank Habineza ya kasance dan majalisa ne a kasar har zuwa watan Mayun da ya ajiye domin shiga zaben Shugaban Kasa. Tun yana dalibi a jami'a ne ya yi fice wajen tofa albarkaci bakinsa a kan adana muhalli da inganta halittun ruwa domin samun arziki ga kasar.
"Daga kasar waje ne ya samo irin wannan tunanin a lokacin da yake karatun a kasar Sweden," inji Ndushabandi.
Yana kamfe da alkawarin rage kudaden haraji da inganta ilimi da hadin kai.
"A wuraren kamfe, yana yawan daga manuniyarsa domin nuna cewa 'ni kadai za a zaba,'" inji masanin siyasa a kasar, Ismael Buchana.Philip Mpayimana:
Philip Mpayimana:
Philip Mpayimana dan takara ne mai zaman kan shi, wanda kuma tsohon malami ne, ya kuma yi aiki a Ma'aikatar Hadin Kai ta kasar kafin ya yi ritaya domin shiga takarar Shugaban Kasa.
Maganarsa cewa zai yi dokar da za ta takaita haihuwa a kasar ta haifar da muhawara mai zafi. "Yana so ya yi dokar da mutum ba zai samu sama da 'ya'ya uku ba,"inji Ismael Buchanan.
Abin da ya sa ya kuduri aniyar yin dokar shi ne domin gwamnati za ta yi gamsar da mutanenta idan "ana tsara" iyali.
"Ya zauna a kasar Faransa, a can ya samu wannan tunanin. Amma yawan maimaita kudurinsa da alakantawa da zamansa a Turai na nuna lallai yana da burin cika muradinsa," inji Ndushabandi.
Za a kammala yakin neman zabe ne a ranar Asabar, sannan ana sa ran samun sakamakon zaben a ranar 20 ga Yuli.