A babban birnin Kigali jama'a sun yi rawa d rera wakokin goyon bayan jam'iyyar RFP mai mulkin Rwanda.. / Photo: AFP

Daga Grace Kuria Kanja (Kigali) da Emmanuel Onyango (Istanbul)

Bayan rantsar da Paul Kagame a karshen watan nan a karo na hudu a matsayin shugaban kasa bayan ya lashe zabe da kashi 99 na kuri'un da aka jefa, zai fuskanci bukatu da dama na jama'a, amma ba za a samu wani sauyi da yawa ba saboda ya kwashe sama da shekaru 20 yana kan mulki.

A yayin yakin neman zabe, ya dinga nuna irin zaman lafiya da nasara da habakar tattalin arzikin da kasar ta samu a karkashin mulkin RFP, bayan kisan kiyashin 1994 da aka yi wa Tutsi da Hutu.

Ya yi alkawarin yin karin ayyuka da yawa a shekaru biyar masu zuwa inda ya gargadi 'yan kasar Rwanda da kar su yanke kauna daga ayyukan sake gina kasar.

Tattalin arzikin Rwanda na habaka da kashi bakwai a cikin sama da shekaru 10 - yana daga mafiya habaka a Afirka. Amma masu jefa kuri'a sun nuna suna bukatar a kara inganta rayuwarsu.

Kagame ya amince da hakan bayan da mahukunta suka sanar da ya lashe zabe da kashi 99.15 na kuri'un da aka jefa.

Tun shekarar 2000 Paul Kagame yake shugabancin kasar Rwanda. Hoto: AFP

"Wadannan alkaluma masu yawa ba wai lambobi ne kawai ba, ko da a ce sun kai kashi 100, ba za su zama lambobi kawai ba. Wadannan lambobi na nufin amincewa, wanda shi ne abin da ya fi komai muhimmanci," in ji shi.

Shugaban mai shekara 66 ya samu karbuwa sosai a wajen 'yan kasar Rwanda, wadanda daga ciki suke masa kallon babban tubali ga kasar.

Tun shekarar 2000 Kagame yake kan mulki. A kowanne zabe tun daga 2003 zuwa 2017, Kagame ya sha samun sama da kashi 90 na kuri'un masu zabe, kuma a wannan karon ma haka abin yake. Hukumar zabe NEC ta bayyana cewa ya samu kashi 99.15.

Bukatu da yawa

Kagame ya ce lokaci ya yi da za a dawo bakin fama, a yayin da mutane ke da bukatu da yawa.

Kasar mai mutum miliyan 14 ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali na sama da shekaru 20, duk da masu suka na cewar babu 'yancin bayyana ra'ayi a kasar.

Har yanzu 'yan kasar Rwanda na fuskantar matsanancin talauci musamman a yankunan karkara.

Kamar kashi 49 na jama'ar kasar talakawa ne, inda kashi 23 kuma suke fama da talauci matsakaici, kamar yadda alkaluman UNDF na talaucin kasashe suka bayyana a 2023.

"A bangarena ina son Shugaban Ƙasar ya ƙara ayyukan da yake yi. Tun da ya yi kokari, a yanzu ina son ya kara wani kokarin - ayyukan yi ga jama'a da gina hanyoyi da makarantu da asibitoci da gina kasarmu ta zama mai karfi," in ji Sharles Mugunga, mazaunin babban birnin Kigali yayin tattaunawa da TRT Afirka.

Tsadar rayuwa na ci gaba da kasnacewa da rashin aikin yi a tsakanin matasa ya kai kashi 21, in ji alkaluman Hukumar Cigaba ta rwanda.

Bankin Duniya ya ce a shekaru goman da suka gabata yaki da talauci ya samu tsaiko "saboda kaura daga kauyuka zuwa birane".

Bankin ya kara da cewar kalubalen na bukatar inganta samar da ruwan sha da lantarki da tallafa wa masu kananan sana'o'i.

"Ka rage haraji da harajin shigo da kayayyaki daga kasashen waje," in ji Kalisa Innocent, wata mazauniyar Kigali.

Wani dan acaba kenan yayinda yake jiran fasinja a wata mahada mai cunkoson jama'a a Kigali. Hoto / Reuters

Kagame na kuma fuskantar batutuwan manufofin kasashen waje. Rikici da maƙwabciyarsa ta Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ya zama wata babbar matsala ga yankin na Babban Kogi.

Kusan dakarun Kagame 3,000 zuwa 4,000 ke yaƙi da 'yan tawayen M23 a gabashin Kongo, kamar yadda jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana.

Rikicin ya tsugunar da kusan mutum miliyan biyu tare da yin ajalin dubbai. Rwanda ta sha musanta zargin tana taimaka wa 'yan tawaye a Kongo.

Sai dai kuma, a garuruwan da ke kan iyaka ana ganin tasirin rikicin na DRC inda kauya wa ke neman mafaka a kauyukan Rwanda.

Burundi ma na zargin Rwanda ta goyon bayan 'yan tawaye da ke kai hare-hare a kan iyakarta, zargin da Rwandan ta musa. Kasashen biyu na da iyaka mai nisan kilomita 315.

Yadda Kagame ke fuskantar rikice-rikice da makotansa ya zama rikitaccen lamari da aka kasa fahimta.

Masu adawa da shugaban kasar Frank Habineza na Jam'iyyar DGP da Philip Mpayimane, dan takarar independa, sun amince da shan kaye a zaben, sun yarda da Kagame ne ya lashe zaben.

Hukumar Zabe ta Kasa za ta sanar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki nan da 27 ga watan Yuli.

A ranar Talata, 'yan kasar Rwanda sun zabi mata 24 'yan majalisar dokoki, da matasa biyu da mutum guda da ke da nakasa.

TRT Afrika