Firayim Minista Rishi Sunak ya ce yarjejeniyar ba da mafaka da Rwanda za ta hana ta bin ka'i'oji.  

Daga Milicent Akeyo

Gwamnatin Biritaniya na kokarin ganin ta aiwatar da manufarta wanda ka iya mayar da dubban masu neman mafaka zuwa kasar Rwanda duk da hukuncin da Kotun Ƙolin kasar ta yi na haramta wannan shiri.

Kazalika 'yan siyasa masu adawa da masu fafutukar kare hakkin bil'adama musamman wadanda ke kallon matakin a matsayin take hakkin dan' adam sun yi ta sukar manufar.

Sai dai Firayim Minista Rishi Sunak ya ce gwamnatinsa na son dakile kwararan yawan bakin haure da ke shigowa kasar ba bisa ka'ida ba.

''Babu yadda za a yi a hana mutane zuwa nan sai dai idan an dauki wani mataki da zai sa a tura su wani waje, kuma abu mafi sauki shi ne yin hakan, '' a cewar Mista Sunak a yayin jawabinsa da ya gabatar wa 'yan majalisar dokokin kasar a farkon wannan watan.

"Wannan ce matsayar mu na hana kwararan bakin haure kuma za mu yi iya kokarinmu wajen shigar da wannan mataki cikin dokokinmu tare da tabbatar da an aiwatar da shi,'' in ji shi.

A ranar 11 ga watan Disamba ne 'yan majalisar dokokin Birtaniya suka amince da shirin inda 'yan majalisa 313 suka kada kuri'ar amincewa da kudirin da ke goyon bayan manufar yayin da 269 suka ki amincewa da shi.

Damuwa kan tsaro

Matakin hakan na zuwa ne kasa da mako guda bayan rattaba hannun Birtaniya da Rwanda kan wata sabuwar yarjejeniya da ta wajabta wa Rwanda karbar mutanen da za a dawo da su daga Birtaniya bayan soke yarjejeniyar farko da Kotun Ƙolin kasar ta yi.

Gwamnatin Birtaniya ta ce an samu adadin masu neman mafaka sama da mutum 600,000da suka shigo kasar a shekarar 2022./ Hoto: AFP

"Muna son tabbatar da cewa mutane za su iya rayuwa cikin aminci da wadata," in ji sakataren harkokin cikin gida ina Birtaniya James Cleverly yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar a Kigali.

Yarjejeniyar za ta daura ne kan aikin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu wanda zai tafi da ''amintaccen yanayin kwarewar'' Rwanda da kuma aikin da Birtaniya ke yi wajen tabbatar da cewa an dakile tsarin kasuwancin miyagun mutane masu bin hanyoyin da suka saba ka'ida,"in ji shi.

Sabuwar yarjejeniyar da kuma amincewar majalisar dokokin Birtaniya na zuwa ne bayan hukuncin kotun kolin kasar a watan Nuwamba inda ta nuna damuwarta kan lafiyar mutanen da za a mayar.

Sai dai kasar Rwanda ta ce babu wata fargaba kan shigo da masu neman mafakar, tare da alkawarin aiwatar da yarjejeniyarta da Birtaniya.

''Ina son na sake jaddada batun cewa, za mu yi maraba da mutanen da aka ware wa Rwanda kuma za a ba su kulawa da kariya da suke bukata don su samu damar gina sabuwar rayuwa," a cewar Ministan Harkokin Wajen Rwanda Vincent Birutsa.

Tun a watan Afrilun 2022 ne Firayim Minista na lokacin Boris Johnson ya fara sanar da wannan tsari bayan kulla wata yarjejeniya tsakanin Birtaniya da Rwanda wanda aka yi wa lakabi da ''shirin masu neman mafaka da ci gaban tattalin Arzikin Birtaniya da Rwanda.''

Hakkoki

Gwamnati ta ce za ta kori duk wanda ya shiga Biritaniya bayan 1 ga watan Janairun, 2022 a karkashin tsarin, tana mai cewa matakin yin hakan zai zama izina ga sauran mutanen dake kokarin bin ''haramtattun hanyoyi masu hadari.''

Za a dauki tsawon shekara biyar ana aiwatar da shirin, inda za a mayar da mutane da ke tsallaka tashar ruwan kasar mai nisan kilomita 33 ta kananan kwale-kwale zuwa Rwanda, inda za a duba cancantarsu ta samu mafaka idan sun yi nasara sai a ba su wuri zama.

Biritaniya na fatan rage yawan masu shigowa kasar neman mafaka zuwa kasa da mutum 100,000 a duk shekara – lamarin da gwamnatin kasar ta ce zai taimaka mata wajen tara biliyoyin fam.

A shekarar 2022 kadai, an samu adadin sama da mutane 600,000 da suka shigo kasar neman mafaka, a cewar gwamnatin Birtaniya.

Birtaniya ta ce sabuwar yarjejeniyar da aka sanya wa hannu za ta tabbatar da cewa Rwanda ba za ta kori masu neman mafaka zuwa wata kasa da za a yi barazana ga rayuwarsu ko 'yancinsu ba.

A shekarar 2022 aka sanar da tsarin mayar da masu neman mafaka a Birtaniya zuwa kasashensu. Hoto: AFP

"Abu wani sabo da yarjejeniyar ta zo da shi, shi ne tabbatar da hakkokin da suka wajaba a kan Rwanda a lokacin da ta karbi mutanen, wanda (yarjejeniyar baya) ba ta zo da hakan ba " a cewar wani malami a jami'ar Rwanda Dakta Alphonse Muleefu a yayin hirarsa da TRT Afirka.

Za a iya dora alhaki kan Kasar wacce ke yankin gabashin Afirka ''idan har ta keta wadannan hakkokin da aka dora mata karkashin dokokin kasa da kasa.''

Rwanda dai ta sha yin watsi da ikirarin da ke cewa ba za ta iya samar da tsaro ga masu neman mafaka ba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da kasar za ta karbi bakuncin masu neman mafaka ba. Tun daga shekarar 1996 take karbar bakin haure da 'yan gudun hijira.

Daukar Nauyi

A cewar Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), tun daga watan Satumban 2023 Rwanda take karbar 'yan gudun hijira sama da mutum 135,000 da masu neman mafaka - galibi daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC) da Burundi da kuma kasar Libiya.

Kazalika kasar ta ba da mafaka ga wasu 'yan gudun hijirar Afghanistan musamman dalibai.

Gwamnatin Birtaniya ta ce a duk shekara tana kashe Fam biliyan uku a tsarin ba da mafaka na kasar, inda a ko wacce rana ake kashe fam miliyan takwas wajen biyan kudaden wuraren zama na 'yan gudun hijira da masu neman mafaka.

lamarin da a yanzu ta ce take kokarin rage yawan kashe wadannan kudade.

Gwamnatin dai ta yi alkawarin ba da kulawarta ga mutanen da za a tasa keyarsu zuwa kasar Rwanda, ciki har da samar musu da wuraren zama da kudaden tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum har na tsawon shekara biyar.

Ya zuwa yanzu kasar Birtaniya ta bai wa Rwanda fam miliyan 240 a matsayin taimakon raya tattalin arzikin kasar, inda rahotanni suka yi nuni da cewa za a kara wasu kudaden da suka kai kimanin fam miliyan 100 a tsakanin shekarar 2024 zuwa 2026.

Wannan kasafin na kan sama da kusan fam 170,000 da gwamnatin Birtaniya ke shirin kashewa kowane mutum dake neman mafaka karkashin sabuwar yarjejeniyar.

Rasa Kasa

Masu sharhi sun bayyana cewa, yayin da ake kara samun kyamar baki a Turai, masu neman mafaka da dama za su iya fuskantar wannan mataki sannan zai yi wuya a iya samu wata mafita iingantacciya.

“Kididdiga ta yi nuni da cewa kusan kashi 50 cikin 100 na mutanen da ke neman mafaka a Turai ba su samu, a karshe sai dai a yi watsi da su,” in ji Muleefu.

"Mutanen da aka yi watsi da su, sukan kasance ba su da wata kasa ko kuma su fada cikin wani mawuyacin yanayi,'' in ji shi.

"Abin da nake ganin ya kamata mutane su mayar da hankali akai shi ne, mumunar hanyar da ake bi wajen kwarara zuwa Turai yana dake da matukar hadari kana yana dada samar da riba ga miyagun ayyuka,'' in ji shi.

A karkashin shirin na rufe kofa ga masu neman mafaka, za a tsugunar da wadanda aka kora a wani wurin da aka gyara a Kigali.

Ginin mai daki 50 ya tsugunar da mutanen da suka tsira daga kisan kiyashin Rwanda na 1994.

Ya zuwa yanzu dai, ba'a kai wani neman mafaka a zahiri zuwa Rwanda daga Birtaniya ba.

A watan Yunin shekarar 2022 ne aka shirya tashin jirgin farko na jigilar masu neman mafakar, amma aka dakatar da shi saboda kalubale na doka.

A yanzu dai, ba za a soma aikin kwasar mutanen ba sakamakon zaben Birtaniya da ke tafe a shekara mai zuwa, la'akari da cewa batun ka iya zama kan gaba a yakin neman zaben kasar.

Masana sun ce sakamakon tsarin shirin masu neman mafaka ta Birtaniya da Rwanda ka iya shafar fannin siyasa da shari'a da hakkokin bil'adama da kuma tasirin tattalin arziki.

TRT Afrika