"Yan kasashen Afirka ba sa bukatar Visa don shiga kasashen  Kenya, Rwanda, Benin, Seychelles da Gambia. Hoto: Reuters

Daga Sylvia Chebet

A ranar 1 ga watan Nuwamba ne shgaban ƙasar Kenya William Ruto ya yi wata sanarwa da ta faranta zuƙatan mutanen da ke yawan yin bulaguro irin su Wangari Muikia, wacce ke yawan yi tafiye-tafiye tsakanin ƙasashen Afirka don yin kasuwanci.

"A ƙarshen shekarar nan, babu wani ɗan Afirka da zai buƙaci biza kafin ya zo Kenya," kamar yadda Ruto ya bayyana wa wani taron ƙasa da ƙasa da aka yi a Congo-Brazzaville.

"Bai kamata a hana ƴaƴanmu ƴan Afirka damar watayawa a cikin nahiyarsu ba kamar yadda ake saka musu iyakoki na shiga Turai."

A wajen Taron Ƙasa da Ƙasa na Tafiye-Tafiye da da Yawon Bude Ido Karo na 23 a Kigali, Shugaban Ƙasar Rwanda Paul Kagame ya jaddada wannan batu na takwaransa na Kenya.

"Duk wani dan Afirka na iya shiga jirgi zuwa kasar Rwanda a duk lokacin da ya ga dama, kuma ba za su biya komai ba don shiga kasarmu,” in ji shi.

Matakin da kasashen Kenya da Rwanda suka dauka na bude kofofinsu ga 'yan Afirka, ya sa burin Ƙungiyar Tarayyar Afirka na ba da damar tafiya ba tare da biza ba a nahiyar na neman cika.

Afirka babu iyaka

Ga mutane irin su Muikia, manajan darakta ta kamfanin ba da shawarwari a kan ƙwarewa a tattalin arziki, jin daɗin tafiye-tafiye ba tare da matsala ko damuwa ba game da takunkumin tafiye-tafiye tsakanin ƙasashen yana 'yantar da hanyoyi fiye da ɗaya.

Muikia ta fadawa TRT Afirka cewa "Saukaka hanyar shiga kasashen abu ne mai kyau matuka," ta ci gaba da cewa "Na san wahalar d aake sha idan ana neman Visa din zuwa wtaa kasa. Yanzu mutane ba sa bukatar su nema ko su bi ta bayan fage don shiga kasarka ko wasu kasashen."

Nahiya mara iyakoki za ta bunkasa tattalin arzikin Afirka da rayuwar mutane biliyan 1.3. Hoto: Reuters

Nan ce gabar da ta hade hanyyoyin Afirka waje guda ga Yarjejeniyar Kasuwanci Ba Tare da tsangwama ba ta Afirka (AFCTA), hadaddiyar kasuwar hada-hada ta mutane biliyan 1.3 da take da jarin da ya kai kimanin dala biliyan $3.4.

Kamar yadda shugaban Kenya Ruto ya bayyana "Saka Visa ga 'yan kasashenmu na Afirka na cutar da kawunanmu ne. A yayin da mutane ba za su iya tafiya ba, 'yan kasuwa ba za su iya zuwa wata kas aba, masu sana'o'i ba za su iya tafiya ba, gaba daya sai mu zama masu tafka asara."

Shugaba Kagame ma, na da ra'ayin hakan wannan matakin zai taimakawa Afirka wajen kulla alakar cude ni in cude ka, kuma duk kasashen nahiyar na da ra'ayin cire wannan shinge.

"Kar mu gaza kallon kasuwar nahiyarmu," in ji Kagame. Ya kara da cewa "'Yan Afirka ne makomar yawon bude ido a duniya, kuma masu matsakaicin smaun kudade z asu ninninka a shekaru masu zuwa."

Muikia, masaniyar tattalin arziki da kamfaninta ke bayar da shawarwari kan tattalin arziki, na da ra'ayin cewa idan ana son nahiyar ta habaka sosai, ana bukatar jama'arta su dinga haduwa da juna.

Tana fatan matakin da Kenya da Rwanda suka dauka zai sanya sauran kasashe ma su yi haka, wnada zai sanya a samu tsari irin na Schengen da kasashen Turai ke amfani da shi.

Muikia ta ce "Abu ne mai kyau dan kwadago ya je wajen da ake bukatarsa. Yana d aamfani mutane su tafi wajen da suke tunanin zai fi amfanar su kuma za su samu tsaro. Yana da amfani ga gwamnatoci su samu matasa da za a dama da su wajen cigaba a kowanne fanni."

Sauran kasashen da suka cire Visa ga dukkan 'yan Afirka su ne Gambia, Benin da Seychelles.

A ra'ayin Wangari, za a ji dadin tsarin a lokacin da manyan kasashen Afirka masu karfin tattalin arziki suka janye visa ga 'yan Afirka baki daya.

A 2016, Tarayyar Afirka ta kaddamar da "Fasfo din Afirka", tana mai cewa zai zama kishiyar na Tarayyar Turai wajen "amfana da arzikin nahiyar". Sai dai kuma, jami'an diplomasiyya da ma'aikatan Tarayyar Turai ne kawai aka baiwa wannan fasfo.

Fasfon Afirka da baiwa 'yan kashen nahiyar damar shiga kowacce kasa ba tare da tsangwama ba, na da manufar janye duk wani kalubale da ake fuskanta wajen tafiya, aiki da rayuwa a nahiyar, kamar yadda aka bayyana a shafin yanar gizon Tarayyar Afirka.

Cire visa ga dukkan 'yan kasashen Afirka a nahiyar zai amfani samar da ayyuka sosai. Hoto: AP

Matsalolin da za a iya samu

A yayin da ake kusantar tabbatar da Afirka mara bukatar Visa ga 'yan Afirka, Wangari ta yi gargadi da cewa "Kar mu cuci kawunanmu da cewa hakan ba zai zo da kalubale da yawa ba."

Ta tambayi cewa "Misali, ta yaya za mu tabbatar ba wata barazana ce muke marabta a kasarmu ba?

Wata tambayar kuma ita ce ta kwarorowar 'yan kwadago, masana tattalin arziki na cewa a yayin da hakan kan iya zama abun ban sha'awa, amma kuma rashin kwararrun ma'aikata ba shi da amfani da yawa ga tattalin arziki.

A yayin da kasashe da dama suke cikin matsin rayuwa da gwagwarmaya, kwararar ma'aikata zuwa wasu kasashen na Afirka na iya ta'azzara rashin aikin yi.

Ta shaida wa TRT Afirka cewa "Irin wannan yanayi na nufin gogayya mai tsauri a kasuwar neman ayyuka da aka yi wa yawa. Idan ba a kula sosai ba, wannan zai haifar da rikici a wata kasar.

Akwai mutane da yawa a kasashen da ke neman ayyukan yi, so za ka iya fuskantar barazana idan aka dauke ka, su ba a dauke su ba."

A yayin da ake da jerin amfani da rashin amfanin janye biza tsakanin kasashen Afirka, masana tattalin arziki na tunatarwa kan damarmaki da kalubalen da ya kamata a kalla a auna domin samun kyakkayawan sabon tsarin.

TRT Afrika