Cyril Ramaphosa ya kasance jigo a siyasar Afirka ta Kudu tun zamanin yakin da ake yi da wariyar launin fata. / Hotuna: Getty 

Daga Sylvia Chebet

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa mai shekaru 71 da haihuwa, mutum ne da ya tsinci kansa cikin mawuyancin yanayi na siyasa a daidai lokacin da yake neman wa'adi na biyu a mulkin kasar tare da ci gaba da riƙe madafun ikon jam'iyyarsa ta ANC tun bayan zaben farko ma jam'iyyu da dama da aka gudanar a shekarar 1994 a kasar.

Hasashen kuri'un jin ra'ayin jama'a na nuna cewa akwai yiwuwar jam'iyyar ANC ta rasa kujerun rinjayenta majalisar dokokin kasar, lamarin da ke zama babban ƙalubale ga shugaban kasar wanda samun nasararsa ta ta'allaka kan farin jinin jam'iyyar.

Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin Ramaphosa ya haɗa nasarori da kuma gazawar jam'iyyar ANC mai fafutukar kwato 'yanci a kansa.

David Monyae, mataimakin farfesa a fannin kimiyyar siyasa a Jami'ar Johannesburg, ya shaida wa TRT Afrika cewa nasarorin da ANC ta samu na dabaibaye da tarin ƙalubale da ke addabar mafi yawan masu kada kuri'a a Afirka ta Kudu.

"ANC ta samu nasarori da yawa ta kowane ma'auni, kama da daga gidaje idan aka yi la'akari da tsarin tattalin arzikin wariyar launin fata da samar da wutar lantarki duk da cewa kamfanin makamashi a Afirka ta Kudu Eskom yana fama da tarin matsaloli ta fuskar rarraba wutar," a cewar Monyae.

Yana mai ƙari da cewa, ita kanta jam’iyyar ta amince da cewa ba ta yi wani abun a zo a gani ba a wasu muhimman wurare.

"Kan batun raba ƙasa wanda shi ne tushen gwagwarmayar neman 'yanci a Afirka ta Kudu, babu wani abun faɗa da za a iya cewa akai, dangane da batun 'yantar da tattalin arzikin yawancin baƙaƙen fata, shi ma babu wani abu da aka yi," in ji shi.

“Kazalika, har yanzu akwai tarin matsaloli a wasu bangarori da dama da suka hada da fannin kiwon lafiya da ilimi kuma dukkan waɗanda haƙƙonkin sun rataya ne a wuyansa (Ramaphosa) a matsayinsa na shugaban wannan jam’iyya mai mulki kuma yana cikin abubuwan da ya gada daga jam’iyyar ANC tsawon shekaru 30 tana mulkin kasar.''

Ramaphosa na ƙoƙarin tunatar da masu kada kuri'a cewa jam'iyyar ANC ita ce wacce ta fi dacewa a zaba a zaben kasar da ke tafe.

Ko da yake ba za'a danganta wasu daga cikin rashin nasarar da ke rage martabar ANC da Ramaphosa kai tsaye ba, amma akwai yiwuwar a danganta su da shugabannin da ya gada.

Sai dia ana yawan yi masa kakkausar suka kan gazawar jam’iyyar a tsawon shekaru biyar da suka wuce bayan ya dare kan karagar mulki.

“Musamman babu wani uzuri da za a yi idan ana maganar cin hanci da rashawa. Annoba ce… kuma duk hakan ya faru ne a ƙarƙashin ikonsa,'' in ji Monyae.

Yana mai kari da cewa, ''Tattalin arzikin bai bunkasa ba, duk da cewa an yi fama da annobar covid-19 da kuma rikicin hada-hadar kudi na duniya, duk da haka da zai iya taɓuka abin da ya fi haka kyau".

Matsalar rashin aikin yi da ya kai kashi 32 cikin 100, ya zama jan aiki ga jam'iyyar ANC ta Ramaphosa, sai dai shugaban ya yi imanin cewa jam'iyyarsa ta samu nasarorin da za su kai ta ga sake samun nasararsa.

Yanzu haka 'yan Afirka ta Kudu suna samun kashi 93 cikin 100 na wutar lantarki, sama da kashi 36 cikin 100 a zamanin mulkin wariyar launin fata lokacin da ake fifita 'yan tsirarrun fararen fata.

Sai dai tsawaita matsalar makamashi wanda ke janyo katsewar wutar lantarki a kullun zuwa sa'o'i 12 a rana na matukar kawo cikas ga ayyukan tattalin arzikin kasar lamarin da ke ƙara rage martabar jam'iyyar.

"Babbar nasara ce amma har yanzu akwai sauran aiki a gaba," kamar yadda Ramaphosa ya bayyana a kwanan nan, yana mai jan hankali da cewa "sabuntawa ba abu ba ne na yini guda ba."

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a na hasashen jam'iyyar ANC za ta rasa rinjayen da take da shi a majalisar dokokin kasar a zaben da za a yi a cikin wannan watan.

Kazalika shugaban ya amince da cewa da yawa daga cikin masu kada kuri'u suna ''sukar ANC,'' amma yana da yakinin cewa har yanzu jam'iyyar ce za ta lashe zabe kuma shi ne ɗan takarar da ya fi cancanta.

"Mafi yawan mutanen da suka taba zabar jam'iyyar ANC har yanzu suna kallon jam'iyyar a matsayin wadda ita kadai ce za ta kawo sauyi a kasar, wajen karfafa ta da kuma inganta ta," a cewar Ramaphosa, inda ya kara da cewa " mutane da yawa ba sa ganin wani ya taɓuka wani abu."

"Duk da haka, wannan na iya zama dama ta ƙarshe da aka bai wa ANC," in ji Monyae.

''Har yanzu akwai sauran mutane Irina waɗanda suke tunawa da abubuwan da suka faru a baya, kuma har gobe suna tafe da tabon gwamnatin da ta shuɗe, kazalika har yanzu ba mu kai ga matakin da al'ummar za su yi saurin mantawa ba, mutane suna kallon ANC a matsayin jam'iyyar 'yantar da jama'a da kuma ba ta dama ta biyu da ta uku.''

Baya ga jam'iyyar, har yanzu akwai masu alfahari da halayen Ramaphosa a cewa masana.

Monyae ya kafa hujja da cewa duk da tarin koma bayan da suka dabaibaye shi, "har yanzu akwai mutanen da za su ce san barka, muna sane da kurakuran, mun fahimci duk wannan amma shi ne wanda yafi cancanta akan sauran."

A ko da yaushe Ramaphosa kan fito cikin kwanciyar hankali a cikin taron jama'a da rangadin yakin neman zabe

Biyo bayan zamanin gwagwarmayar ‘yantar da kasar da kuma sauyin da aka samu daga mulkin wariyar launin fata zuwa kasar Afirka ta Kudu mai bin tafarkin dimokradiyya, Ramaphosa wanda ya kasance lauya yana daga cikin waɗanda amince da cewa sun ba da gudunmawa sosai.

''A zahiri, idan za'a yi mishi adalci, ya matukar taka rawar gani a tsarin demokradiyyar da muke morewa yanzu.

"Ya kasance babban mai shiga tsakani na jam'iyyar ANC a duk lokacin da ake tattaunawa da gwamnatin wariyar launin fata kuma ya kasance jagora a rubuce-rubucen kundin tsarin mulkin da muke amfani da shi," in ji Monyae.

A matsayinsa na tsohon ɗan kungiyar kwadago wanda ya wakilci ma'aikatan ma'adinai, Ramaphosa ya kasance yana da burin zama shugaban kasa tun ranar samun 'yancin kai amma sai da ya tsaya takara na tsawon shekaru 25 kafin ya kai ga wannan matsayi.

An tilastawa Jacob Zuma wanda ya gada daga kujerar mulki yin murabus bayan da ya fuskanci tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa kuma Ramaphosa - a lokacin mataimakin shugaban kasa ne - ya rike igiyar adawa da Zuma kana ya mamaye fadar gwamnatin kasar.

Sai dai a zaben kasar da za'a gudanar cikin wannan wata, akwai yiwuwar tafiyar ta yi matukar yin wuya ga jam'iyyar ANC, la'akari da kuri'ar jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan da kamfanin zabe na Ipsos ya tattaro wanda ya nuna nasarar da jam'iyyar ta samu na sama da kashi 57 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben kasar na shekarar 2019, ya ragu yanzu zuwa sama da kashi 40 cikin dari.

TRT Afrika