Daga Charles Mgbolu
Mutanen kasar Afirka ta Kudu za su kada kuri’a a ranar 29 ga Mayu a zaben da ake ganin Jam’iyyar African National Congress (ANC) mai mulki a kasar na fuskantar kalubale mafi girma a shekara 30 da suka gabata.
Hukumar Zaben Kasar Mai Zaman Kanta ta sanar a watan Maris cewa akwai masu kada kuri’a a zaben na Shugaban Kasa da na wakilan larduna guda miliyan 27.79, wanda shi ne mafi yawan masu kada kuri’a tun bayan da kasar ta koma dimokuradiyya.
“Babban abin lura a zaben shi ne karuwar matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 39 a cikin masu zaben. Masu shekaru a wannan tsakanin su ne kashi 42 (wato miliyan 11.7),” inji Babban Jami’in Zaben kasar, Sy Mamabolo.
Masu sharhi a kan harkokin yau da kullum a kasar suna ganin wannan alkaluman a matsayin abin da zai iya sauya fasalin kasar.
Matasa da dama sun bayyana rashin aikin yi a matsayin babban kalubalen da ke ci musu tuwo a kwarya.
Yawan marasa aikin yi a kasar abin damuwa ne kasancewar alkaluman kafar kididdiga ta yanar gizo ta Statista ta bayyana Afirka ta Kudu a matsayin kasar da ta fi yawan marasa aikin yi a nahiyar Afirka.
La’akari da zabukan baya
Jam’iyyar ANC ce ta lashe dukkan zabukan shekarar 2019, inda ta yi kamfe da kundin manufofin “Hada hannu domin ciyar da Afirka ta Kudu gaba,” inda kudurin farko a cikin kundin shi ne, “Samar da ayyukan yi masu nagarta.”
A cikin kundin manufofin jam’iyyar mai mulki, akwai inda aka bayyana cewa, “Sauya yanayin tattalin arzikin kasar domin mutane su amfana ta hanyar bayar da tallafin da zai samar da hanyoyin cigaban mutanen kasar da samar da ayyukan yi masu inganci,” kamar yadda yake rubuce a cikin kundin manufofin jam’iyyar mai mulki.
A cikin shekara biyar da suka gabata, rashin aikin yi ya karu matuka a Afirka ta Kudu. Alkaluman da Hukumar Kididdiga ta Afirka ta Kudu, wato Statistics South Africa (Stats SA) ta fitar a watan Mayu ya nuna cewa akwai mutum miliyan 8.2 da ba su da aikin yi a kasar a rubu’in farko na shekarar 2024.
Rashin aikin yin ya karu da kashi 32.9 ke nan idan aka kwatanta da rubu’i na hudu na shekarar 2023, wanda shi ne mafi girma tun daga lokacin da aka fara tattara alkaluman a shekarar 2008.
Irin wadannan alkaluman ne suke fusata mutanen kasar. “Duk wanda ya samu nasara a zaben dole ya dage wajen yaki da rashin aikin yi, musamman a tsakanin matasa.
Muna son ganin matasa sun shiga harkokin tattalin arzikin kasar, suna samun damar gudanar da rayuwarsu cikin walwala, sannan su rika biyan haraji,” inji Tebogo Makubung, wani dan wasan tsere kuma dan jarida mai gabatar da shirye-shiryen wasanni a tattaunawarsa da TRT Afrika.
Hukumar Kididdigar kasar wato Stats SA ma ta tabbatar da hakan, inda ta bayyana cewa matasan kasar, “suna fama da rashin aikin yi,” inda matasa masu shekara tsakanin 15 zuwa 34 suka fi fuskantar matsalar.
“Sakamakon alkaluman farko na shekarar 2024 ya nuna an samu karin marasa aikin yi guda 236,000, inda jimillar ta koma miliyan 4.9. Wannan ya nuna karin marasa aikin yi da kashi 1.3 daga kashi 44.3 da yake a rubu’in karshe na shekarar 2023 zuwa kashi 24.5 a rubu’in farko na bana,” kamar yadda rahoton hukumar na watan Mayu ya nuna.
Wani mazaunin birnin Johannesburg mai suna Nhlanganiso Sabelo ya ce ya kamata a bunkasa bangaren koyar da sana’o’in hannu domin samar da damarmakin ayyukan yi ga matasan kasar.
“Ina so gwamnati mai zuwa kada ta mayar da hankali a kan samar da ayyukan yi kawai, akwai bukatar ta inganta bangaren koyar da sana’o’in matasa. Idan matasa ba su da kwarewar da ake bukata, ta yaya za su samu aikin su ko kuma su fara wani kasuwancin da za su dauki wasu aiki?” in ji Sabelo.
Shi ma Jaji Abolore wanda yake da wajen shakatawa na dare haka yake tunani, inda ya ce, “Zuba kudi domin samar da ilimi kyauta da koyar da sana’o’in hannun da ake bukata za su taimaka wa matasa wajen inganta harkokinsu. Misali fasahar AI da ta shigo yanzu, akwai bukatar a koyar da matasa amfaninta da wayar musu kai domin su daina fargabar rasa ayyukansu,” inji Jaji a tattaunawarsa da TRT Afrika.
Bukatu masu yawa
Shugaban Kasa Cyril Ramaphosa, wanda yake takarar domin mulki a zango na biyu ya san cewa nasararsa ta ta’allaka ne da yadda ya gamsar da mutanen kasar hanyoyin magance rashin aikin yi.
“Mutane da dama sun shiga makaranta, sun samu shaidar difloma, amma ba su samu aikin yi ba, sannan ba su da jarin da za su fara kasuwanci. Duk da cewa bunkasa tattalin arziki yana da muhimmanci wajen samar da ayyukan yi, ba za mu jira har sai ya zama mu din ne kawai muka samar da ayyukan da ake bukata ba,” inji Shugaba Ramaphosa a watan Fabarailu.
Mutanen kasar irin su Jaji suna kara nanata cewa gwamnati kada ta takaita tunaninta a kan masu neman aiki kawai, ya kamata a rika tunawa da irinsu masu samar da ayyukan yi ga wasu.
“Ya kamata a rika bayar da tallafin bunkasa kasuwanci. Ya kasance an saukaka hanyoyin samun tallafin kamar tallafin kudi ko rage kudaden haraji, wadanda za su taimaka wajen kara habaka harkokin wuraren shakatawa na dare. Shekara uku ken an da wucewar annobar covid, amma har yanzu ba mu warware daga illar da kullen ya mana ba,” in ji Jaji.
A ranar 29 ga Mayu, masu kada zabe za su zabi wakilansu na Majalisar Dattawa mai mutum 400, wanda kuma su ne za su zaba Shugaban Kasa.
Tuni kowane bangare ya shirya tsafa domin zaben, wanda zaben ne kuma zai nuna tafarkin da kasar za ta dauka wajen yin sallama da farkon goman shekara na hudunta. Matasa suna fata sabon Shugaban Kasar, ko ma wane ne, zai sanya su a cikin tsare-tsarensu.