Daga
Sylvia Chebet
Yadda duniyar take kara fuskantar yake-yake, kananan yara ne suka fara fuskantar matsalolin da hakan ke zuwa da shi, inda sukan sha fama da damuwa da raunuka a sanadiyar yake-yaken da babu ruwansu.
Watakila ranar 11 ga Yuni, wadda ranar ce Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana da Ranar Wasanni ta Duniya, ita ma ta zama tamkar sauran ranaku irinta domin tuna rayuwar miliyoyin yara da suka makale a kasashen duniya da ake yaki irin su Falasdinu da Sudan da Dimokuradiyyar Jamhuriyar Congo da Ukraine da Myanmar.
Babban Daraktan Asusun UNICEF, Catherine Russel, ta ce an ware ranar ce domin yara su fahimci cewa, "za su iya gudanar da rayuwarsu komai wahalar da suka tsinci kansu a ciki."
Kididdiga ta nuna girman lamarin. Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya a kan kuncin da yara suke rayuwa a ciki a garuruwan da ake yaki ya nuna yadda suka fuskanci matsananciyar damuwa a shekarar 2023, inda aka samu mace-macen yara da dama, wasu suka jikkata a yankunan Falasdinu da Sudan da Myanmar.
Kungiyoyin Ba da Agajin Gaggawa sun ruwaito yadda yara da dama suka mutu a yake-yaken da babu hannunsu a ciki. Wadanda kuma suka tsira, suna rayuwa ce ta kunci da damuwa da ba za su taba mantawa da ita ba har abada.
Alamun yaki - Yaran da suka samu raunuka a Gaza
A Gaza, Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa sama da yara 15,00 ne aka kashe tun bayan da Isra'ila ta fara hare-harenta a kasar a ranar 8 ga Oktoban 2023.
Wakiliyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ta musamman a kan harkokin yara da yake-yake, Virginia Gamba ta ce sun saka jan fenti a kan sojin Isra'ila bisa samunsu da laifin kashe dalibai 'yan makaranta da marasa lafiya a asibitoci.
Bayan barazanar harin bama-bamai da suke fuskanta, fararen hula a Gaza suna kuma fama da rashin ababen bukata irin su ruwan sha da na girki da wanki da sauransu.
Yanzu haka sama da yara 3,500 da suka tsira da ransu, amma suke fuskantar barazanar mutuwa saboda rashin abinci mai gina jiki.
A Sudan, an kashe kusan yara 500, sannan sama da 700 sun samu raunuka duk da an tsagaita wuta tsakanin sojojin Sudan da jami'an tsaron Rapid Support Forces masu tada kayar baya. Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kai hari a makarantu da asibitoci guda 85 tun farkon fara yakin a Khartoum a ranar 15 ga Afrilun 2023.
Asusun UNICEF ya sa Sudan a cikin daya daga cikin kasashen da suke da matukar wahalar rayuwa ga yara. Wani rahoto ya nuna cewa akalla yara miliyan 19 ne suke fuskantar barazanar daina zuwa makaranta, wanda hakan zai shafi ci gaban rayuwarsu.
Makarantu da dama a Sudan sun zama matsugunin 'yan gudun hijira akalla miliyan 8.
Warakar tunani
Amal Adam Hassan, wadda ta tsere daga Khartoum zuwa Kosti, yanzu koyarwa take yi a daya daga cikin irin wadannan makarantu da suka zama matsugunin 'yan gudun hijira, inda take rayuwa tare da sauran daruruwan masu gudun hijira.
Yaran da aka kwaso daga Sudan domin tseratar da su daga yakin a lokacin da suke isa Abu Dhabi
"Koyar da yaran ba abu ba ne mai sauki ko kadan," inji ta a tattaunawarta da TRT Afrika, inda ta kara da cewa, "yanzu babu ruwanmu da manhajin karatu, mun fi mayar da hankali a kan gyara tunaninsu."
Da taimakon Hukumar 'Yan gudun hijira ta Norway, Amal ta samu damar halartar kwas domin kwarewa a kan koyar da yara da suke fuskantar yaki. Wannan horon zai taimaka mata wajen sanin makamar aikin yadda za ta kula da yaran.
"Muna kokarin sauya tunanin yaran, wanda daga cikin dabarunmu akwai nuna musu muhimmancin hutawa da wasanni," in ji Amal.
Masana sun ce wasanni ne magani da yaran suka fi bukata a yanzu.
"Wasanni na da matukar muhimmanci ga yaran da suka fuskanci matsalolin rayuwa kamar rikici ko suka rasa wani na kusa da su," inji Anne Filorizzo Pla, masaniya a fannin lafiyar kwakwalwa da ke aiki da Gidauniyar Save the Children.
"Ta hanyar wasa ne yaran za su dawo da farin cikinsu, har su dawo daidai."
A kasar Dimokuradiyyar Jamhuriyar Congo kuwa, dagulewar rikici a Kudancin kasar ta sa dole akalla yara 78,000 suka tsere daga gidajensu. Kasar, wadda take yankin Afirka ta Tsakiya tana kuma cikin kasashen da suka fi yawan yara da suke fama da karancin abinci mai gina jiki.
A Myanmar, Majalisar Dinkin Duniya ta ce Yakin Basasar kasar ya jawo karuwar tauye hakkin kananan yara da kashi 120%. Wannan ya kunshi jefe bam a wurare mai yawan mutane, zaban inda za a kai harin da gangan da matsanancin bukatar agajin gaggawa.
Haka kuma wasu yaran da dama ba sa samun damar wasan duk da cewa ba su taso a garuruwan da ake yaki ba, sai dai saboda ana tilasta musu zuwa aiki domin samun kudi.
Asusun UNICEF ya kiyasta cewa yara miliyan 160 ne suke fita aiki maimakon su mayar da hankali wajen karatu da wasanni.
Kamar yadda Save the Children suka bayyana, su kuma yara mata suna fama da aikace-aikacen gida ne wanda hakan ke hana subdamun lokacin wasanni da sauran ayyukan kirkira da fasaha , wanda hakan ke takaita musu damar amincewa da kansu da kuma cika burinsu a rayuwa.
Bayan wasanni da jin dadi
Masana halayyar dan Adam sun bayyana cewa wasanni na taimakon yara wajen koyon karatu, inganta lafiyarsu da cigabansu. Ta hanyar wasanni ne yara za su koyi natsuwa da mayar da hankali da juriya da kara karfin hadda da harshe.
Haka kuma wasanni na kara bude idon yara su san duniya da abubuwan da ke faruwa. Hakan na kara bude kwakwalwarsu da taimakonsu wajen burin zama wani abu a gaba.
"Ko da komai ya tabarbare musu ne, za su iya samun damar koma hayyacinsu da lafiyarsu ta hanyar wasanni saboda wasanni ba wai wasannin ba ne kadai, yana da matukar muhimmanci musamman wajen gano fasahar yara da ba su karfin gwiwa da waraka da bude musu kofofin cika burukansu na rayuwa," inji rahoton Save the Children.
Sai dai duk da haka, kusan kashi 70 na manya ba su san muhimmancin wasanni a rayuwar yara ba, don haka sai ya kasance ba sa ba wasannin muhimmanci.
"Yara a ko'ina suke suna da 'yancin wasanni. Yana da matukar muhimmanci ga cigabansu da lafiyarsu da karatunsu. Amma duk da haka, ba a ba wasannin muhimmanci sosai," in ji Pla.
Wasanni wani 'yanci ne da yara suke da shi kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tanada bayan taronta na Hakkin Yara a shekarar 1989.
Masana suna ganin kaddamar da ranar 11 ga Yuni a matsayin Ranar Wasanni a matsayin tabbatar da muhimmancin wasanni wajen samun ilimi da inganta lafiyarsu.