Daga Nuri Aden
Tafiya ci rani tamkar neman allura a cikin ruwa ne, ko dai ka yi nasara ko akasin haka.
Kimanin 'yan Somaliya miliyan biyu ne suka bar ƙasarsu ta haihuwa suke zama a ƙsashen waje, wanda hakan ya sanya suka zama 'yan ƙasar da suka fi kowa watsuwa a cikin kasashen duniya.
An fi samun al'ummomin Somaliya a Gabas ta Tsakiya da Amurka da Turai da Arewacin Amurka da Burtaniya, da kuma Gabashin Afirka.
Kamar yadda lamarin ya kasance game da ƙaura ta hanyar neman ingantacciyar dama ta rayuwa, da yawa daga cikin ƴan gudun hijirar Somaliya da ke tafiya ci rani sun sami ci gaba a wuraren da suka samu kansu.
Duk da haka, sun kasa daina tunanin ƙasarsu ta haihuwa da kewar dangi da abokan arziki da kuma al'adunsu.
Yayin da tashe-tashen hankulan da yakin basasa a shekarun 1990 ya haifar da yawaitar hijira, yawancin Somaliyawa sun ba da gudunmawar albarkatunsu da gogewarsu wajen zaburar da ci gaban al'umma.
Wadanda suke zaune a kasashen waje sun samu manyan nasarori. A Arewacin Amurka da Turai, 'yan asalin Somaliya suna zama 'yan majalisa, ministoci da ƙwararru a fannoni daban-daban na ƙoƙarin ɗan'adam.
Jawaahir Daahir MBE, shugabar kungiyar Global Somali Diaspora (GSD), ta shaida wa TRT Afrika cewa, "Lokacin da na ga 'yan gudun hijirar Somaliya na komawa gida don bayar da gudunmawarsu ga ci gaban tattalin arzikin kasar, musamman ta hanyar kungiyoyi masu zaman kansu da kuma kungiyoyin fararen hula a lokacin rikici, hakan ya sa na cika da alfahari."
"Akwai fatan cewa rayuwar gaba za ta yi haske, tare da matasa masu ilimi - inda malamai, ma'aikatan jin dadin jama'a, lauyoyi, likitoci, da ma'aikatan jinya - suke ba da gudunmawa ga al'ummominsu, ko a cikin Turkiyya da Turai, Arewacin Amurka ko Afirka."
Tururuwar masu dawowa
Wasu daga cikin mazauna kasashen waje sun koma Somaliya don daukar nauyin jagoranci, da karfafa muhimman sassa kamar kiwon lafiya, ilimi, noma da fasaha.
Kudade, zuba jari da canja wurin sana’o’i su ma suna ba da gudunmawa sosai ga tattalin arzikin kasa da al’umma.
Majalisar Dinkin Duniya da cibiyoyin hada-hadar kudi daban-daban sun yi kiyasin cewa kudaden da ake turawa za su kasance tsakanin dalar Amurka biliyan 1.4 zuwa dala biliyan biyu a duk shekara, wanda ke tallafa wa kusan rabin gidajen Somaliya a cikin kasa mai sama da mutum miliyan 18.
GSD, wata kungiya ce mai zaman kanta wacce aka kafa don hada kan al'ummar Somaliya a duk duniya, ta karfafa wannan alaka sosai tsakanin 'yan kasashen waje da kasarsu ta haihuwa.
"Na tuna sosai lokacin da ɗaruruwanmu suka taru daga sassa daban-daban na Turkiyya, Turai, Arewacin Amurka, Asiya, Australia da Afirka a watan Yunin 2014.
Mun gane wani sarari - mun bazu ko ina cikin duniya amma ba mu da hanyar ganawa da juna," in ji Jawaahir, wacce ke zaune a Burtaniya.
"Daga waɗancan tattaunawar ta farko ta fito da manufar samar da wani dandali da zai haɗa kan al'ummar Somaliya da ke zama a ƙasashen waje baki ɗaya.
Bayan shekaru goma, muna bikin zagayowar ranar kafa wata cibiyar da ta sami ƙarfi da tasiri."
Haɗin kai don wani dalili
GSD ta karbi bakuncin taron kasa da kasa karo na 10 a ranakun 28-29 ga watan Satumba a Istanbul, inda aka ƙirƙiri ƙungiyar shekaru goma da suka gabata.
“Muna matukar godiya da irin kyakkyawar tarba da gwamnati da al’ummar Turkiyya suka yi mana, wanda ya ƙara haɓaka ƙoƙarin da muke yi na samar da ƙwarewa ga matasa.
Taimakon da suke bai wa gwamnatin Somaliya, wanda ya hada da horar da 'yan sanda da sojoji da karfafa kiwon lafiya, yana da matukar amfani," in ji Jawaahir.
“Wannan ƙawance mai ɗorewa yana ci gaba da ƙarfafa, kuma muna matukar godiya da irin goyon bayan da al’ummar Turkiyya suka ba mu, wadanda suka tsaya mana a lokacin da muke bukata.
Yunkurinsu ya kawo sauyi mai ma’ana a tafiyarmu ta samun ci gaba da kwanciyar hankali”.
Taron da aka yi a watan da ya gabata ya kasance wani muhimmi ga wakilan Somaliya don yin aiki tare da fahimtar juna, da kuma karfafa matsayinsu na masu kawo ci gaba a kasarsu ta haihuwa.
Firaminista Hamza Abdi Barre na Somalia na daga cikin manyan baƙi a taron.
"Muna kammala taron Ba da Agajin Gaggawa na 'Yan Somaliyan, wanda zai hada dukkan kungiyoyin Somaliya da ke aiki a wannan bangare.
Idan muka duba gaba, muna da niyyar kafa irin wannan tarukan ga malamai da likitoci da injiniyoyi na Somaliya,” in ji Jawaahir.
Hanƙoron ci gaba
Tasirin ’yan kasashen waje ya zarce kudaden da ake turawa; ana kallon su a matsayin masu muhimmai ga tsarin zamantakewa da tattalin arzikin Somaliya.
Masu zuba jari na kasashen waje suna da kashi 80% na jarin fara kasuwancin kanana da matsakaitan masana'antu. Tattalin Arziki na yau da kullun yana bunƙasa akan gudunmawarsu.
Yayin da Somaliya ke ci gaba da sake gina kasar, gwamnati ta amince da muhimmiyar rawar da 'yan kasashen waje ke takawa wajen ci gaban kasa.
Dukkanin shugabannin Somaliya karkashin jagorancin Shugaba Hassan Sheikh Mohamud, a ko da yaushe sun amince da rawar da al'ummar Somaliya ke takawa, tare da karfafa musu gwiwa da su ci gaba da saka hannun jari wajen sake gina kasar Somaliya.
A yayin tafiye-tafiyen da yake yi a hukumance, kamar dai yadda magabatansa, Shugaba Hassan Sheikh yakan gudanar da taruka da kasashen waje yayin da yake jaddada kiran goyon bayansu a yaki da ta'addanci tare da ayyukan gina kasa.
A nata bangaren, Mogadishu na yin kokarin saukaka wa 'yan kasashen waje da ke dawowa cikin al'amuran yau da kullum.
Ɗaya daga cikin ƙalubalen shi ne rarrabuwar ƙwararru da ta tattalin arziki. Mazauna ƙasashen waje suna da ilimi da ƙwarewa da gogewa waɗanda ba a samun irin su a cikin ƙasar.
“Lokacin da ’yan gudun hijirar Somaliya suka koma kasarsu, galibi ana kallonsu ta wani nau’i na daban.
Al'ummomin yankin na kiran su 'Qurbajoog', tare da amincewa da abubuwan da suka faru a kasashen waje. Wannan kalmar tana nuna sha'awa da ma'anar rabuwa," Jawaahir ta shaida wa TRT Afrika.
Moalim Abdallah, kwararre a fannin IT da ya yi karatu kuma ya samu horo a Landan, shi ne ya kafa GlobalNet, wadda ta himmatu wajen karfafa al’ummar Somaliya ta hanyar ba da horo da ƙwarin gwiwa na shiga harkar fasaha.
"Gwamnatinmu na buƙatar saka hannun jari don yin amfani da fasahar dijital ga matasanmu na Somaliya," in ji Moalim.
Dr Maryan Qasim, wacce tsohuwar minista ce a gwamnatin tarayya, ta yi imanin cewa ’yan ci-ranin Somaliya da mutanensu da ke gida za su iya tsara hanyar samun ci gaba tare idan suka guje wa kabilanci.