Gana na karbar tufafi gwanjo sama da miliyan 15 daga kasashen arewacin duniya a kowanne mako, in ji kungiyar Greenpeace Africa. / Hoto: AFP

Daga Sylvia Chebet

Muhalli da yanayi a Ghana na fama da illolin abin da Yammacin duniya ke kira 'tsaftar bazara" a fannin tufafi.

A kowanne mako, tufafi gwanjo guda miliyan 15 da aka zuba a manyan kwantenoni kusan dari na isa kasar ta Yammacin Afirka da Arewacin Duniya, mafi yawanci ta tashar jiragen ruwa ta Tema.

A 2022, Gana ta shigar da tan 121,934 na kayan gwanjo da a kasar ake kira da sunan "obroni wawu".

Ma'anar wannan suna a yaren kasar shi ne "Tufafin wanda ya mutu", kuma hakan ba shi da illa kamar ta tasirin kayan ga muhalli da lafiya.

Wani bincike da Greenpeace Africa suka gudanar ya ce Ghana ce kasa ta biyu a duniya da ta fi kowace shigar da kayan gwanjo bayan Pakistan, inda take da kashi 5.1 na kasuwannin duniya a wannan fanni.

Kayan gwanjo na iya zama darasi wajen ci gaba da amfani da kaya da al'adu a gidaje a duniya baki daya, amma abinda Ghana ke shigarwa kasar daga Birtaniya kowace shekara ya wuce batun kayan sa wa tsaffi ko gwanjo.

A duniya, manyan kasashen da suka fi fitar da tufafi zuwa kasashen waje a tsakanin 2010 da 202 su ne AMurka, China, Jamus da Birtaniya.

Mafi yawancin kayan gwanjon da ke zuwa Ghana na shiga kasuwar Kantamanto da ke babbn birnin Accra, kasuwa ta biyu mafi girma a kasar da ke da rumfuna kuan 5,000 kuma sama da mutum 30,000 ke cinikayya a lokaci guda a ciki.

Kasuwanci mai wahala

A kowacce rana, masu sayar da kayan na gwagwarmaya a layukan kasuwar kanana tare da daurin kayan gwanjo, wadanda kusan a a iya cewa sun gama lalacewa ba za su amfanar ba.

"Wadanda suka lalace gaba daya sun fi masu dan kyau din yawa sosai," Greenpeace suka rawaito wata dattijuwa na fadin hakan.

Binciken kungiyar ya bayyana cewa kusan rabin kayan da aka shigo da su ba sa samun masu saya inda suke kare wa a shara tare da lalata muhalli.

A kowace shekara ana tattara tufafi kwaya dubu dari biyar da ba a sayar da su a kasuwar Kantamanto, ana zubar da su a bola da sauran wuraren zubar da shara a Accra.

Wani rahoton Greenpeace Africa mai taken "Tufafin gaggawa, guba a hankali: Rikicin Tufafi gwanjo a Gana", ya bayyana cewa ruwa, gabar tekuna, da gonaki na illatuwa daga tufafin da ake zubarwa.

Tsaunukan robobi

None of these has any resale value. Masu bincike na Greenpeace sun kuma bayyana cewa kusan rabin kayan gwanjon da ake kawo wa ana samar da su ne daga sinadaran 'synthetic fibres'.

Masu binciken sun kuma gano cewa ana amfani da dattin kayan tufafi a matsayin mai a wajen wankan jama'a kamar tsohuwar Fadama, wata unguwar marasa galihu da ke Accra.

A rashin masu aikin, bakin hayakin da ke fita daga wadannan wajen wanka na illata iska da sinadarin da ake kira noxious da yake fitarwa, wanda ba shi da ingan, kamar yadda ka'idojin kasa da kasa suka tanada.

Mafi muni ma shi ne yadda wasu daga cikin wadannan wurare suke dauke da gurbatacciyar iskar carbon da phenol, wadanda suke janyo cututtuka.

Masu bincike sun gano cewa, sinadarin styrene wanda ke kashe kwayoyin halitta na haihuwa.

Wani gwajin fasaha infrared da aka gudanar kan bolar kayan gwanjo da aka tattara a kasuwar Kantamanto da sauran bololi ya nuna kusan dukkan kayan ba sa iya narkewa su zama kasa.

Sake samar da kaya daga tsofaffi

Polyester da ake sake sarrafawa a samar da wasu kayayyakin, ana samar da shi ne daga bolar kwalaben 'polyethene terephthalate', wanda ke nufin zuwan robobin cikin muhalli jinkiri kawai yake samu maimakon kare zuwan sa baki daya.

A cikin Accra da kewaye, ana kai tufafin da ba a sayar da su ba zuwa wuraren zubar da shara, ciki har da wuraren da ake kira tsaunukan bola a ke kusa da kogin Odaw a yankin Tsohuwar Fadama.

A gefen tekuna ana ganin tasirin datti da bolar tufafi da aka tattara tsawon shekaru, inda suke kewaye a gabar tekun Accra da garuruwan kasar da dama.

A wasu wuraren, dattin na bayyana tarihin zubar da shara.

"A tsawon lokaci, darttin kayan na nutsewa a gabar teku ta yadda suke hadewa da kasa, suna samar da gubar lalatattec tufafi wanda ke tafiya can kasan ruwa, inda suke yaduwa su illata da cutar da halittun cikin tekun," in ji nazarin na Greenpeace.

Nazarin ya ambaci tan 0.5 na sinadaran kananan robobi da ake saki a cikin tekun kowace shekara daga wanke bolar tufafi da ake yi, wanda ya kasance kashi 35 na kananan robobin d aake fitarwa a duniya.

Kungiyar Kare Muhalli ta WWF, ta ce bangaren samar da tufafi na bayar da gudunmowar tan miliyan 92 na bola a duk duniya kowace shekara.

Tufafi masu amfani

"Wannan rahoton kiran a farka ne," in ji jagorar yaki da robobi a Afirka ta Kunfiyar Greenpeace, Hellen Dena.

"Dattin da ake zubarwa a China ba wai batun muhalli ba ne kawai; babban misali ne na rashin adalcin muhalli da rashin kulawar da Arewacin Duniya ke yi."

Masanan kare muhalli a nahiyar na da ra'ayin cewa matsalar ta samo asali ne daga sabon salon mulkin mallaka, inda Ƙasashen Yamma suke kallon Gana da sauran kasashen Afirka - ciki har da Kenya, Tanzania da Tunisia - a matsayin bolarsu.

"Dole ne kamfabnonin samar da tufafi da gwamnatoci su dauki mataki cikin gaggawa na magance illar da bolar ke janyo wa a kasashe irin su Gana," in ji Dena.

Gana na bukatar karin kasa a yayin da ba ta da isassun wuraren kula da bola.

Greenpeace sun yi kira da a hana fitar da tufafin da suka lalace a Arewacin Duniya, samar da ka'idajojin fito, da tsarin bayar da izini kafin a dakko kayan zuwa kasashen Afirka, kuma dole ne a shigar da mahukuntan yankunan cikin lamarin.

Tsarin mai lalata wa ya gyara

Domin ganin an ankarar da mahukunta da kamfanonin Arewacin Duniya su fahimci irin tasiri da illar kayan gwanjo a Gana da ma wasu wuraren, Greenpeace sun zaburar da jama'ar yankunan kewayen Kasuwar Kantamanto da su tattara wasu daga kayayyakin da aka yi amfani da su aka jefar.

A mako guda, sun loda tan 4.6 a karamar kwantena, wadda aka mayar da ita da kayan zuwa Jamus.

A wajen Makon Tufafi na Berlin a watan Fabrairu, 2024, an ajje kwantenar a wajen inda a jikin ta aka rubuta sakon "Dawowa ga Wanda Ya Aika".

Ko wannan sakon na karara zai sanya masana'antun samar da tiufafi da mahukunta su dauki alhakin magance matsalolin da suka janyo tare da samar da yanayi mai kyau? Wannan abu ne da ake jiran gani.

WWF a nata bangaren, ta ce dole ne a koma ga tsarin "ingantaccen tufafi" don bayar da kariya ga duniya da ma masana'antun tufafin.

Kungiyar ta bayyana cewa "A tsarin ingantaccen tufafi, dukkan tufafi zai zama mai karko, an samar da shi da inganci sosai kuma daga abubuwan da ake iya sake sarrafa su ko sabunta su.

Sannan ana iya juya su ta hanyoyi da dama a sake amfani da su idan bukatar hakan ta taso, ake iya gyara su idan ana so, sannan a karshen rayuwarsu a mayar da su wani sabon abu."

TRT Afrika