Daga Firmain Eric Mbadinga
Sarah Boulungui mai shekara 38, ta kankame jakar hannunta, lebbanta na rawa inda idanuwanta suka cika da alamun nasara da damuwa a yayin da take sauraren a kira sunanta daga cikin mutane da dama da ke dakin jira na Cibiyar Kula da Lafiyar Jarirai da ke Libreville, babban birnin Gabon.
Tana daga cikin matan da suka yi tururuwa zuwa cibiyar, suna fatan smaun maganin kimiyya da zai taimaka musu wajen zama iyaye mata.
Shekaru 46 kenan da duniya ta mayar d amartani tare da rashin yarda da yadda aka haifi jaririn kwalba na farko, Loise Brown, a Oldham da ke arewa maso-yammacin Ingila.
Wannan tsari a fannin kula da lafiya mai tarihi a yanzu ya zama gaskiya a Afirka, kamar yadda yake a sauran sassan duniya, yana samar da farin ciki ga miliyoyin mata da ba sa iya daukar ciki a mahaifa saboda dalilai da dama.
Matsalar tsadar
Haihuwar jarirai a kwalba da a Turance ake kira 'In-vitro fertilisation (IVF)', kalmomin sun maye gurbin na farko da ake kira "test tube baby', jaririn kwalbar roba," ya zama mai kyakkyawar nasara har a lokuta masu tsauri, ciki har da ynayin shekaru da cututtuka.
Babban kalubale shi ne kudin d ake kashe wa wajen wannan tsari na haihuwa. IVF na da wahala kuma da yawan mutane a kasashen Afirka da dama ba sa iya biyan kudin da ake bukata.
Amma Gabon, kasar da ke Tsakiyar Afirka da ke da mutane sama da miliyan biyu, ta rungumi wannan juyin juya hali, tun daga horar da ma'aikatan lafiya, samar da gine-gine da sayen kayan aikin da ake bukata.
Ma'aurata a Gabon da ke gwagwarmayar samun haihuwa ba sa bukatar sai sun bar kasarsu a yau don samun amfana da tsarin IVF.
"Kafin zuwa CHU, na yi kokari ta hanyoyi daban-daban. Na ziyarci likitocin haihuwa da yawa kuma an same ni da ciwon cikewar mahaifa. Na karbi magani, kuma an fada min zan iya daukar ciki, amma har yanzu shiru," in ji Sarah a yayinda take tattaunawa da TRT Afirka.
Jure jarrabawa
Gwagwarmayar Sarah ta neman magani ta fuskanci kalubalen lafiya da zamantakewa.
"Ku yi tunani a ce aure babu haihuwa, abu ne mai wahalar gaske. Makotanka, abokai da 'yan uwa sun san kana da aure. Surukanka na zargin ka da cewar ka zubar da ciki sau da yawa a baya kafin ka yi auri dan su. Abu ne mai matukar wahala," in ji Sarah tana rawar baki da ban tauayi.
Kafin ta yi tunanin amfani da hanyar IVF, Sarah ta yi kokarin jan ra'ayin mijinta, wanda ya bayyana damuwarsa kan ko tsarin abin dogaro ne.
A yayin da mijin Sarah ya amince, sai ma'auratan suka mika kawunansu ga cibiyar kula da lafiya da ke CHU. Bayan daukar lokaci mai tsawo tare da kashe kudade a yawa, burinsu ya cika. Sarah ta zama uwa bayan 'yan watanni.
"Wannan ce babbar kyauta ga rayuwata. A lokacin da na kalli jaririn, sai na ce 'Nagode wa Ubangiji, d aya tuna da ni." in ji ta, tana zubar da hawayen jin dadi.
Juna biyu da aka samu nasarar haihuwa
CHU Mère-Enfant Jeanne Ebori ne asibiti na farko da ya fara aikin IVF. Tun 2022, a loakcin da aka kafa cibiyar, ta samu nasara da kashi 37.
Ya zuwa yau, a kalla ma'aurata 130 ne suka karbi kulawa kan tsarin IVF, inda kashi 70 suka kammala samun kulawar, kuma aka samu mata 30 da suka dauki ciki cikin nasara, inda suka haifi lafiyayyun jarirai.
"Mun yi hasashen kashi 20 zuwa 30 na ma'aurata a Gabon lafiyayyu ne ta fuskar haihuwa. Da zarar mace ta kai shekara 40, yiyuwar ta samu ciki na raguwa. Akwai kuma matsalar cututtuka da ka iya samun ta," in ji Dr Jean-François Meyé, daraktan CHU Mère-Enfant Jeanne Ebori.
Duk da kyara da kulabale daga jama'a, mata da dama irin su Urlette Etima, mai shekara 33, da Emarence Koumba, su zabi su jarraba IVF. "Akwai yaushe akwai fata mai kyau. Na yi amanna cewa a rayuwa, dole ka dauki matakan magance kalubalen da kake fuskanta," in ji Urletta, tsohon babban jami'in banki wanda ya koma dan kasuwa.
Shekara biyu kenan da yin aure, Emerance da mijinta Gauthier, sun mika kawunansu ga Dr Orphelia Makoyo da tawagarsa don ba su damar zama iyaye.
Hanyar da ake dabbaka IVF
A yayin da ake kula da lafiya kan tsarin IVF, matakin farko shi ne a dauki kwayoyin halittar mutumin da ya kas a haihuwa ko daukar ciki ta hanyar dabi'a da ake kira 'oocytes', sai a hada su da maniyyin namiji mahaifa ko wajen cikin mace, a dakin gwaje-gwaje.
"Idan rainon kwayoyin halittar da na maniyyin ma'auratan ya yi nasara, sai a dauke su a dasa su a cikin mahaifar mace," in ji Dr Makoyo.
Duk da IVF ya taimaki mutane da dama a Gabon da sauran kasashen Afirka su samu ciki duk da kalubale, har yanzu akwai wahala sosai.
"A wajen wasu 'yan Afirka, IVF wata mummunar al'ada ce da suka gaza fahimta. Sauyi ga tunanin mutane zai zo, amma za a dauki lokaci," in ji masanin zamantakewar dan adam dan kasar Chadi Felix Mbete yayinda yake tattaunawa da TRT Afirka.
Adadin masu son IVF na daduwa
A tsakanin al'ummar Gabon, wadanda suke riko da al'adun gargajiya, ana yawan zargin mata da matsalolin rashin haihuwar ma'aurata a lokacin da suke gwagwarmayar daukar ciki.
Domin yin riga-kafi ga hakan, Dr Aurelie Engangoye, kwararriya kan cututtuka masu yaduwa a Cibiyar Binciken Lafiya ta Kasa da Kasa da ke Franceville, ta bukaci mata da su kula da kawunansu kafin su fara tunanin samun haihuwa.
"A wasu lokutan, cututtuka na janyo matsaloli ga daukar ciki. A bangaren maza kuma, raguwar yawa da ingancin maniyyi na janyo gaza haihuwa," in ji ta yayin tattaunawa da TRT Afirka.
A sama da shekara biyu, Dr Meye na sanya idanu kan kaduwar ma'auratan da ke zuwa don samun waraka ta hanyar IVF, duk da cewar na da tsada sosai.
A yanzu haka a Gabon IVF na lashe kudi da ya kai dala dbu $3,318 - $5,792
Amma kuma duk da haka, A wajen mata irin su Sarah, duk da wahalar gwagwarmayar, amma tana kai mutum ga gaci, ba wai kawai zama uwa ba ne. Batu ne na karya lago da sauya tunani, jariri a lokaci guda.