Koriya ta Kudu ta karbi bakuncin tawagar kasashen Afirka 48, wadanda kusan 25 daga cikinsu shugabannin kasashe da gwamnatoci ne. Hoto: Gidan Gwamnati Nairobi.  

Daga Sylvia Chebet

Masanin tattalin arzikin Kenya XN Iraq yana kallon ka'idar jan hankali ta duniya ta fuskar ilimin karatunsa.

"Afirka kamar wata kyakkyawar mace ce; kowane namiji yana sonta da aure," in ji shi, yana mai kwatance da taron farko na Koriya ta Kudu da Afirka da aka kammala a shekarar 2024 wanda ya hada shugabannin kasashe da gwamnatoci kusan 25 daga nahiyar a babban birnin Seoul.

Taron na ranar 4 da 5 ga watan Yuni shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin makamantan manyan tarurrukan A firka da kasashen Rasha da Italiya da China da kuma Faransa suka gudanar.

Kamar sauran maneman Afirka, Seoul ta yi alkawarin zuba jari na biliyoyin daloli ga nahiyar.

"Don ƙarfafa haɗin-gwiwa da Afirka, Koriya ta Kudu za ta fadada shirin ba da Taimako kan Ci Gaban (ODA) da kusan dalar Amurka biliyan 10 daga yanzu zuwa shekarar 2030," kamar yadda shugaban kasar Yoon Suk Yeol ya sanar a wurin taron.

"Kazalika Koriya ta Kudu za ta saka dala biliyan 14 a cikin kudaden fitar da kayayyaki zuwa ketare," in ji shi.

Ga Iraki, farfesa a jami'ar kasuwanci na Nairobi, duk wanda ya musanta tashin hankalin da ke gaban Afirka ''yana barci ko kuma yana jin barci ne.''

Magagin barci da asara

Da alama Amurka ta shiga magagin barci bayan taronta na Afirka a shekarar 2014, inda ta bar China ta sha gabanta a fannin tattalin arziki da kuma Rasha a fannin tsaro.

Shugaba Joe Biden da William Ruto sun yi tattaki tare da matansu zuwa fadar White House don liyafar cin abinci a ranar 24 ga Mayu, 2024. HOTO: Fadar gwamnatin Nairobi

A watan Mayu ne, Washington ta baza jan kafet wa shugaban Kenya William Ruto. inda aka haɗa liyafar cin abincin a fadar White House a ziyarar da ke zama ta farko da wani shugaban Afirka ya taba kaiwa cikin shekaru 15.

"Za mu kaddamar da abin da mu ka kira hangen nesa na Nairobi da Washington," in ji Shugaba Joe Biden yayin wani taron manema labarai na haɗin-gwiwa da Ruto a fadar White House.

''Wannan shiri zai hada cibiyoyin haɗa-haɗar kudi na kasashen duniya don tara albarkatu ga kasashen da ke fama da basussuka,da kuma buɗe wasu damammaki na samar da kudade ga kamfanoni masu zaman kansu tare da samar da hanyoyi ba da lamuni masu inganci da dorewa da kuma sauki.''

A nasa bangaren, shugaba Ruto ya bayyana ƙarara cewa kasarsa wadda ke yankin gabashin Afirka ba ta kallon gabas ko yamma kanta a "gaba take." yana mai kari da cewa Amurka na da damar sake farfado da tasirinta a Afirka.

"Amurka na buƙatar ta tashi tsaye," in ji Ruto. "A matsayinta na mai bin tsarin dimokuradiyya, kuma kasa wadda ta yi imani da bin doka, dole ne a yi la'akari da wannan sannan dole dimokuradiyya ta fita daban."

Masana na ganin hakan a matsayin amincewa da cewa an bar Amurka a baya kana tana buƙatar ta yi sauyin tashi tsaye.

A wani gagarumin mataki, Biden ya sanarwa majalisar dokokin Amurka kudurinsa na ayyana Kenya a matsayin babbar kawar ƙungiyar NATO.

Ƙungiyar NATO

An kafa ƙungiyar ta NATO ne shekaru 75 kawo yanzu don adawa da takwaranta tsohuwar Tarayyar Soviet da kawayenta.

Manufar ƙungiyar ita ce tabbatar da tsaro da yanci ga kasashen Turai da Arewacin Amurka a fadin iyakar Tekun Atlantika ta hanyar albarkatunta na siyasa da na soji.

''Don haka a takaice, zama babbar kawar NATO na nufin za ka iya samun damar amfani da wasu kayayyakin aikin soji da fasahar zamani na software da kuma bayanan sirri,'' Iraki ya shaida wa TRT Afirka, Yana mai kari da cewa "Amma ba za ka iya samun kariya mai yawa ba kamar yadda za a samarwa ainihin memba na NATO,misali a kariyar hari."

Yana mai nufi da cewa, tun bayan samun matsayin manyan kawayen NATO, kasashen uku na Afirka- Maroko da Tunisia da Masar- sun ci gajiyar kayan aikin soji, sannan a yanzu ana daukarsu a matsayin kasashen mafi karfin dakaru a yankin gabas ta tsakiya da arewancin Afirka.

Kenya za ta kasance kasa ta farko da ke yankin kudu da hamadar Sahara, kuma kasa ta 19 da za a nada a matsayin babbar kawar NATO. Hoto: Gidan Gwamnati Nairobi

Da zarar majalisar dokokin Amurka ta amince da hakan, Kenya za ta zama kasa ta 19 da ta samu matsayi na babbar kawar ƙungiyar tsaro ta NATO, kuma ta farko a yankin kudu da hamadar Sahara.

Sai dai duk da haka akwai wata sarƙarƙiya da ke ƙasa, '' ina tsoron cewa, ta hanyar nuna alaƙar mu (Kenya) da Amurka, za mu samar wa kanmu sabbin abokan gaba. Babban abin tambaya anan ita ce ko ribar za ta wuce kasadar yawa,'' in ji Iraki.

Kazalika masanin tattalin arziki kuma mai sharhi ya dada jadadda wannan batu, yana cewa ''watakila Kenya ta datse matsayinta na babbar kawar ƙungiyar (NAM) ta hanyar kulla kawance da NATO."

Ko da yake, masu sharhi da dama sun yi imanin cewa tasirin NAM yana raguwa yayin da duniya ke ƙara samun wasu hanyoyi. A halin yanzu, kasashe suna kulla kawance ne bisa muradun kansu.

Ba a samun komai a kyauta

Amurka ta sanya Kenya a cikin jerin amintattun kawayenta na dimokuradiyya a nahiyar, tana mai daraja gudummawar da take bayarwa a kokarin samar da zaman lafiya da tsaro a kasashe da ke fama da rikici kamar Somaliya da Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo da Sudan s da kuma Haiti.

Yayin da wannan dabarun haɗin-gwiwar ta dauki tsawon shekaru 16, masana sun ƙara jan hankali kan jinjinar da Amurka ta yi wa Nairobi.

Tsawon shekaru 50 kawo yanzu, tasirin Amurka a Afirka ya dusashe, kuma har yanzu damar sake dawowarsa yana sama-ya-na- dabo.

"Ina ganin Amurka ma ita ta ce ba za ta iya brain albarkatun nahiyar Afirka ga China ita kadai ba, tana son samun babban rabo.'' in ji Iraki.

Shugaba Ruto ya dawo gida daga ziyarar aikinsa ta kwanaki uku da ya kai Amurka tare da wasu nasarori da suka hada da samun kudin aikin hanyar Nairobi zuwa Mombasa na dala biliyan 3.5 da kuma yarjejeniyar tsaro ta dala biliyan 7.

Kazalika, Amurka za ta aika da jirage masu saukar ungulu 16 da kuma motocin sulke kusan 150 don inganta shigar Kenya cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Wani sashe na hasashen masanan ya yi nuni da cewa akwai yiwuwar kasashen yankin Gabas su mayar wa Amurka martani wajen tayin ƙarin kasuwanci da zuba zari.

"Muna fatan za mu amfana daga yankunan Gabas da Yamma a nan gaba. Kamar yadda suke faɗa a harshen Swahili, tutapita kati kati yao (za mu bi su sannu a hankali )," in ji Iraki.

TRT Afrika