Tarayyar Afirka ta gudanar da taro a karo na 44 don duba matsalolin zaman lafiya da tsaro da nahiyar ke fuskanta. / Hoto: Reuters

Daga Coletta Wanjohi

Shugabannin kasashe da na gwamnotoci daga kasashe mambobin Tarayyar Afirka (AU) na taro a Addis Ababa babban birnin Ethiopia don taronsu na shekara-shekara, a yayin da rashin tabbas ke jarraba karfin kungiyoyin yankin.

Moussa Faki Mahamat, shugaban Tarayyar Afirka, ya kawo irin kalubalen da ake fuskanta a bayanin da ya yi ga mambobin majalisar zartarwar a ranar 14 ga Fabrairu da aka bude taron.

"Akwai wani sabon salo da ya zo na raunata shugabancin yankuna da nahiyarmu," ya fada wa majalisar zartarwar da ta hada da ministocin harkokin wajen da aka dora wa alhakin tsara manufofin taron shugabannin kasashen Tarayyar Afirka da z aa yi a a ranakun 17-18 ga Fabrairu.

A Yammacin Afirka, kungiyar ECOWAS da ke da mambobi 15 na fama da matsalar matakin da kasashe uku suka dauka - Mali, Burkina Faso da Nijar - na za su fice daga kungiyar. Dukkan kasashen na karkashin mulkin soja a yanzu haka, sun ki yarda da aiki da wa'adin bayar da sanarwa shekara guda kafin wata kasa ta bar kungiyar.

Mali, Burkina Faso da Nija sun zargi ECOWAS da 'gaza bayar da cikakken goyon baya wajen yaki da ta'addanci" da "kaucewa daga tubalan da aka kafa ta a kai" da ma sauran zarge-zarge.

Kasashen uku sun gana a Burkina Faso don tattaunawa kan kirkirar tasu kungiyar wadda ba ta da alaka da ECOWAS. Tuni d ama suka sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro da tattalin arziki, an sanya hannu kan yarjejeniya a watan Disamban bara inda aka kafa Kawancen Kasashen Sahel.

Mabambantan ra'ayoyi

An samu rabuwar ra'ayi kan gaskiyar korafin da Burkina Faso, Mali da Nijar suka yi game da ECOWAS.

"Idan ka kalli batun ta fuskar yadda Tarayyar Afirka, musamman ma kwamitin Tsaro da Zaman Lafiya ya magance matsalolin irin su na sauye-sauye a gwamnati da suka saba wa kundin tsarin mulki, za a iya cewa abinda kasashen nan suka yi zargi kan ECOWAS na da dalilai," in ji Tsion Hagos, daraktan shirye-shirye na wata kungiya mai zaman kanta da ke bincike kan manufofin shugabanci a dukkan Afirka, yayin tattaunawa da TRT Afirka.

Chadi ta kasance karkashin shugabancin soji, kuma ba a taba dakatar da ita daga Tarayyar Afirka ba. Chadi da ke shimfide a Arewaci da Tsakiyar Afirka, na karkashin mulkin soja tun bayan rasuwar shugaba Idris Deby Itno a 2021.

Gabon da sauran kasashe uku da suka fice daga ECOWAS na cigaba da zama a dakace a AU saboda zaman su a karkashin mulkin soja.

Tambayar ikon mulki

Ba ECOWAS ce kawai kungiyar yanki da aka girgiza tushenta ba.

A Gabashin Afirka, Sudan ta sanar a watan Janairu cewa ta dakatar da zaman ta mamba a Kungiyar Cigaban Gwamnatoci ta (IGAD), wadda AU ta dora wa alhakin taimaka wa wajen kawo karshen rikici tsakanin sojojin Sudan da mayakan RSF da aka fara tun watan Afrilun 2022.

A gefe guda, Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, ta ki sabunta yarjejeniyar zama mamban Kungiyar kasashen gabashin Afirka bayan 8 ga Disamba. Ta zargi dakarun da aka kai kasar a watan Yuli, 2022 don kawar da barazanar da kungiyoyin 'yan bindiga ke kawo wa, da zama "mara tasiri da ke hada kai da 'yan tawaye".

Gwamnatin DRC ta bayyana cewa ta gwammace Kungiyar Cigagan Kudancin Afirka ta fara aika dakarunta kasar.

"Na tambayi kaina wannan tambayar kuma ina tambayar ku. Tun yaushe kuma zuwa yaushe wannan kawance zai tsaya tare da kauce wa rushewa daga kan tubalansa?" Shugaban AU ya tambayi ministocin harkokin waje da suka taru a Addis Ababa.

AU ta amince da 'yancin mulkar kai na kasashe mambobinta. Kundin tsarinmulkin Tarayyar ya bayyana cewa kowacce kasa na da 'yancin kare kanta da iyakokinta.

Wannan na bayar da dama ga kasashe mambobin AU su ki aiki da wasu matakai da AU ta dauka a yankunansu.

"Wannan daya daga cikin lokutan da za ka tambayi kanka ne, 'shin AU wata kungiya ce mai tabuka abin kirki?' da a ce babu wasu mambobi da sadaukar da wani bangare na ikonsu ga kungiyar ba, to da AU na ci gaba da fuskantar kalubale." in ji Hagos a tattaunawar sa da TRT Afirka.

Kwararru sun zargi kasashe mambobin Tarayyar da kin bin aiki da matakan da AU ke dauka, a lokacin da babu dakarun nahiya da ke shiga tsakani.

"Har yanzu AU ba ta aiki dakarun ta na kar ta kwana. Wannan wani bangare ne na matsalolin."

Aikin dakarun kar ta kwana na Afirka shi ne wanzar da zaman lafiya a nahiyar a yayin da aka samu rikici a wata kasa. A 2003 aka dakatar da wannan aiki, amma har yanzu za a iya amfani da shi.

"Tabbas, wanzuwar wadannan dakaru ba ya nuna ana karya mutunci da darajar mulkin kasa. Amma idan akwai hanya mai kyau sosai ta aikewa da dakaru, to hakan zai hana afkuwar rikici a yanki, kamar yadda muka gani a DRC." in ji Hagos.

Kwararrun sun kuma bayyana akwai bukatar yin tattaunawa kan iyakance rawar da kungiyoyin yankuna za su taka.

An dora wa Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro na Tarayyar Afirka laifin amincewa da dukkan matakan da kungiyoyin shiyya suka yanke, maimakon ya tsaya ya kalli ko matakin ya dace ko akasin haka.

Lokacin nazari da waiwaye

Tarayyar Afirka ta amince da Kungiyoyin Shiyya guda takwas, da suka hada da Kungiyar Larabawan Maghreb, Kungiyar Gabashi da Kudancin Afirka, Kungiyar Kasashen Afirka na Sahel, KUngiyar Gabashin Afirka, Kungiyar Cigaban Tattaln Arzikin Yammacin Afirka, IGAD da SADC.

An kafa duk wadannan kungiyoyi kafin a kafa AU, kuma suna da ayyuka da tsare-tsare mabambanta.

Hagos ya yi amanna da cewa lokacin hisabi ya yi ga AU.

Ya ce "Wannan ce gabar da ya kamata a dauki darasi daga abinda ya faru a baya. Idan ka dawo yin abinda ka saba yi, ko abinda tsarin da kake kai ya kawo, to za ka zama abin misali ga wasu. Muna neman hadin kai mai dore wa ne."

TRT Afrika