Mutane da dama na ganin zai yi wahala matuƙa Shugaba William Ruto da babban abokin hamayyarsa Raila Odinga su haɗa kai a gwamnati, amma wasu manazarta siyasa na ganin ta zo.
A ƙoƙarin da yake yi na daidaita gwamnatinsa da ke fama da rikici, Ruto ya gabatar da wasu fitattun 'yan adawa hudu daga tawagar Odinga a cikin majalisar ministocinsa a ranar Larabar da ta gabata.
Sabbin ministocin da aka naɗa da suka haɗa da na ƙawancen ɓangaren adawa sun haɗa da John Mbadi (ministan kudi), James Opiyo Wandayi (ministan makamashi da man fetur), Hassan Ali Joho (ministan tattalin arzikin ma’adinai da teku) da Wycliffe Oparanya (kungiyoyin hadin gwiwa da kanana da matsakaitan masana’antu).
Farfesa Macharia Munene, malami mai koyar da tarihi a jami'ar ƙasa da ƙasa ta Amurka-Afirka, ya ce ƙawancen ba abin mamaki ba ne, amma ƙaimin matasa 'yan shekarun Gen-Z ne suka yi sanadin samar da iya.
“Dabarun siyasa ne da za su bai wa shugaban ƙasa damar shawo kan matsaloli da yawa kafin ya yanke shawarar abin da zai biyo baya.
Hakan zai danganta ne da abin da ‘yan majalisar dokoki za su yi cikin makwanni biyu ko fiye da haka, yayin da suke gudanar da aikinsu na tantance wadanda aka nada," kamar yadda Munene ya shaida wa TRT Afrika.
Abin da aka fara a matsayin zanga-zangar adawa da ƙarin haraji ta rikiɗe ta zama mummunan rikicin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 50 da kuma ɓarnata dukiya.
Munene ya ce "'Yan adawa za su so ƙwarai su zama wani ɓangare na fafutukar, amma a wannan karon ba ruwansu da harkar."
Ya yi amanna abubuwan da suka faru a Kenya a baya-bayan nan sun sa 'yan adawa a wani yanayi da aka kasa tantancewa.
"Za su so a ce su ne suka jagoranci zanga-zangar da ta yi nasara. A yanzu dole ne su nemi hanyoyin da za su yi uwa su yi makarɓiya a harkar ba waɗannan matasa 'yan Gen-Z ba."
An mallake 'yan adawa?
To a yanzu da gwamnati ta haɗa kai da mafiya yawan 'yan adawa, tambayar a nan ita ce wa zai dinga bin diddigin gwamnati?
Masu sharhi a siyasa sun yi amannar cewa bayan gama zanga-zangar baya-bayan nan, za a samu ɗan daidaito a tsarin siyasa da gwamnati a Kenya, ko da akwai ko babu jam'iyyar adawa.
"Matasa 'yan Gen-Z sun nuna wata hanya ta saka gwamnati a saiti," in ji Munene, yana mai cewa a yanzu ya zama wajibi a kan kowane ɗan ƙasa ya nuna damuwa da kuma jawo hankali idan har al'amura ba sa tafiya daidai.
Munene ya jaddada cewa, ‘yan majalisar wakilai, ko na adawa ne ko na jam’iyya mai mulki, an zabe su ne domin su wakilci jama’a, ba gwamnati ba.
"Don haka idan 'yan majalisar dokoki suka gaza gudanar da wakilcin mutane kamar yadda ya kamata, to 'yan ƙasa na iya amfani da damarsu kuma tuni an ga yadda matasan Gen-Z suke hakan, har ta kai matakin da 'yan siyasa suke damuwa saboda sun fara rasa iko da mutanen da ba zaɓarsu aka yi ba." in Munene.
Idan har suna so sukai labari a siyasance, to dolesu ɗinke ɓarakar da ke tsakaninsu. " Dole su nemo hanyar daƙile wannan fafutukar."
Yanzu da gwamnatin Kenya da wani babban bangaren 'yan adawa suka ɗinke, shin ko za a warware wa matasan matsalolin da suka gabatar?
"Wani zai ce tashin hankali zai ragu kaɗan, amma zai zama kuskure a yi tsammanin cewa komai ya wuce, saboda idan har ba a magance matsalolin ba, to babu wani dalili da zai sa mutane su ci gaba da fafutukar," in ji Munenne.
Ido akan 'yan majalisa
A wannan karon dai ‘yan majalisar za su gudanar da tsatsauran bincike yayin da suke tantance sabbin ministocin da aka zaba.
Bayan rikicin da ya barke a ranar 25 ga watan Yuni, inda 'yan adawa suka mamaye majalisar jim kadan bayan ta zartar da wani kudurin doka mai cike da cece-kuce kan batun amincewa da karin haraji, masu sharhi na ganin a yanzu 'yan majalisar za su yi kokarin tabbatar da cewa sai an dogara da su.
"Za a sake gwada 'yan majalisar," a cewar Macharia, yana mai cewa: '' Idan ('yan majalisar) suka nuna cewa suna da hurumin yanke hukunci, to hakan zai zama hujja mai kyau na cewa 'a'a wannan ba zai yiwu ba.''
Makonni biyu masu zuwa, in ji shi, na iya zama lokaci mafi mahimmanci ga abubuwan da za su faru nan gaba.
'Yan siyasa dake zaman ɗoya da manja
Dangantakar da ke tsakanin shugaba Ruto da madugun 'yan adawa Odinga ita ce cikakkiyar ma'anar ɗaci da zaƙi.
Sun kasance aboƙan siyasa na kut-da-kut tsawon shekaru da Ruto wanda ya kasance mai goyon bayan Odinga a yayin da yake neman zama shugaban Kenya a zaben 2007.
Bayan zaben, ɗan takarar jam'iyyar adawa a lokacin Odinga ya yi watsi da sakamakon zaben ƙasar da ya baiwa shugaba mai ci a lokacin Mwai Kibaki nasara.
Kazalika rikici ya barke bayan zaben wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,000.
Tattaunarwar zaman lafiya da ƙasashen duniya suka yi, ta kai ga kafa gwamnatin haɗin kan kasa, wadda William Ruto da Raila Odinga suka shiga inda Odinga ya zama firaminista.
Sai dai alakar 'yan siyasar biyu ta fara yin tsami ne bayan da a shekarar 2011, kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta gurfanar da William Ruto tare da wasu 'yan siyasar Kenya da dama kan rikicin da ya haddasa asarar rayuka.
Odinga dai baya cikin wadanda aka gurfanar.
A shekarar 2013, Ruto ya haɗa kai da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar adawa ta Uhuru Kenyatta wanda shi ma yake ta fafatawa da kotun ICC.
Daga baya kotun ta ICC ta yi watsi da tuhumar da ake wa Ruto da Uhuru.
Uhuru ya zabi Ruto a matsayin abokin takaransa inda daga ƙarshe ya doke Odinga a Zaben.
Daga baya ne Kenyatta ya gayyaci Odinga cikin gwamnatinsa, lamarin da ya ƙara harzuka mataimakin shugaban kasar Ruto.
Ruto dai ya tsaya takara a zaben shugaban ƙasa na shekarar 2022 ba tare da son ran ubangidansa Uhuru wanda ke marawa Odinga baya.
Ruto, wanda ya fito daga dangin da ba su da wani tarihi na siyasar ƙasa, ya sha alwashin kawo ƙarshen ''siyasa gado'' a Kenya, yana mai kwatance da iyalan Uhuru da Odinga, waɗanda zuriyarsu ke da tushen siyasa.
Ruto ya doke Odinga da rata marar yawa a zaben shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 9 ga watan Agustan 2022.
Tun daga lokacin suka zama abokan gaba na siyasa.
Sai dai zaman ɗoya da manja da 'yan siyasar ke yi ya sake ɗaukar wani salo bayan matakin baya-bayan nan da Shugaba Ruto ya ɗauka na bai wa na hannun damar Odinga mukami a majalisar ministocinsa.