Daga Dayo Yussuf
Afirka ta dauki wasu matakai masu muhimmanci wadanda suka sanya ƙwararru ke kallon hakan a matsayin babban matakin samun cigaban tattalin arziki. Musamman Gabashin Afirka, tuni yankin ya fara habaka a kudu da Sahara.
Amma a tattare da yiwuwar samun ci gaba, akwai abubuwa da dama da ake tsammani.
Yawaitar kasashen Afirka da tattalin arzikinsu ke habaka ba makawa zai sauya fasali tare da kara yawan bukatar kayan masana'antu a nahiyar, inda makamashi yake da muhimmanci.
A saboda haka, daga ina wannan makamashi zai zo, kuma meye zai inganta hanyar kao shi?
"Wasu kasashen gabashin Afirka sun nuna sha'awar habaka makamashin nukiliya, musamman ma Kenya," in ji Amos Wemanya, babban mai bayar da shawara kan makamashi mai sabuntuwa a kamfanin 'Power Shift Africa' yayin da yake tattaunawa da TRT Afirka.
"Tuni Kenya ta dinga shiri don tabbatar da wannan abu tun da jiamawa. Muna da tsarin tallafin karatu ga dalbai a jami'o'in gwamnati inda suke koyon yadda ake sarrafa nukiliya, a yanzu muna da hukumar habaka nukiliya a Kenya wadda ke ayyukan samar da makamashin nukiliyar a yankin da ke gabar teku."
Kamar yadda yake a yankuna mafi yawa a duniya, bukatar kasashen Afirka ta makamashi mai sabuntuwa ta mayar da hankali kan makamashin geotermal, hydropower, iska ko hasken rana.
Amma Kenya da wasu kasashen nahiyar a baya-bayan nan sun nuna sha'awar habaka makamashin nukiliya, sauyin da yake kawo damuwa kan yiwuwar tabbatuwar lamarin.
"Idan har za mu habaka samar da lantarki a yankin, ba na tunanin nukiliya ce mafita," in ji Amos, wanda kungiyarsa da ke nazarin samar da alkaluma da mafita kan manufofin Afirka."
"Damuwarmu ita ce yadda samar da makamashin nukiliya yake daukan lokaci mai tsayi kafin a kaddamar da shi. Tun shekaru 15 Kenya ta ke tattaunawa kan samar da shi., kuma har yanzu bai samu ba. Yana jan kudi sosai, sannan ga batun tsaro da kariya."
Zage damtse
Injin 'Reactor' ne jigon cibiyar nukiliya, wand ake amfani da makamashin da yake fita a lokacin motsaway nukiliya - yanayi ne mai rikitarwa da 'neutron' suke karo da juna, tare da sinadarin zarra na uranium da ke mayar da su nukiliya.
Reactor na fitar da ruwan zafi, yana samar da tiririn da ke zafafa layukan da suke samar da lantarki.
Makamashin nukiliya ba ya fitar da gurbataccen hayaki zuwa duniya, ba kamar mai ba, wanda ke gurbata muhalli. Tabbas, wannan zabi na makamashi mai tsafta na zuwa da wahalhalu na sarrafa su da kuma batun kare al'umma.
Babban kalubalen shi ne yadda nukiliya ke iya yin zafin da ya wuce ka'ida d akuma iya fashewa. Mafi yawan kwararru sun fi damuwa game da yiwuwar samun kuskure daga mutane wanda zai janyo babbar musiba.
Amon ya yi bayanin cewa "Makamashin nukiliya ya hada da kayan da ka oiya bindiga su fashe, kuma dole ne a zubar da dattin wadannan kayayyaki a wani waje na daban."
"A nahiyar, muna da matsalar kula da bola. Ban san ta yaya za mu magance dattin wadannan kayan fashewar b, kenan muna da wani babban kalubale ga lafiyarmu."
Ana yawar bayar da misalin gargadi da hatsarin nukiliya na Fukushima da ya afku a Japan a 2011.
Ayyukan shimfida bututu
A farkon wannan shekarar, Uganda ta sanar da fara aikin makamashin nukiliya da zai dinga samar da megawatt 2,000 a yanki mai nisan kilomita 150 daga Kampala. Kasar na da manufar fara aiki da cibiyar da ke samar da megawatt 1,000 a 2031.
Rwanda ma, a baya-bayan nan ta sanya hannu kan yarjejeniyar gina cibiyar nukiliya. Kenya da Tanzania ne mambobin Kungiyar Kasashen Gabashin Afirka na baya-bayan nan da suka daura aniyar assasa cibiyar nukiliya.
A bangaren amfani mai kyau, cibiyar makamashin nukiliya na da karfin samar da lantarki ninki biyu sama da sauran hanyoyin samar da makamashi na zamani da ke aiki da fasaha.
Wata dama kuma ita ce, a kalla a karance, wannan cibiya za ta iya samar da lantarki ba tare da tsayawa ba saboda yanayi ko ruwan sama ko zafi ba.
Amos ya yi amanna da cewa makamashin nukiliya zai yiwu ne a wasu kasashe, amma zai zama matsala da kalubale ga wasu kasahen da suke bukatar kayan aiki sosai.
"Tuntuni muna da kalubale zuba jari a bangaren makamashi wanda kuma bangaren na bukatar zuba jari. Da a ce mun zuba wadannan kudade a tsarin samar da makamashi a babban tsarin habaka shi da ya fi.
A yanayi irin hakan, ba na tunanin muna yin adalci ga al'ummun da ba sa amfana da tsarin," ya fada wa TRT Afirka.
Domin samar da megawatt 1,000 na makamashin nukiliya ana bukatar dala biliyan $5, kenan idan Uganda na son samar da megawatt 2,000 na makamashin nukiliya, kasar za ta yi amfani da dukkan kudin da kasar ke samu a shekara guda.
Hakan na nufin irin wannan aikin zai dogara ne kan rancen kudade daga kasashen waje da ke da kudin ruwa sosai.
Jamus, Daya daga cikin kasashen duniya mafiya cigaba ta fuskar tattalin arziki, tana rufe cibioyin nukiliyarta mataki mataki. Sai dai kuma, wadanda suke daya bangaren muhawarar cewa kasashen da suka ci gaba na hakura da wadannan ayyukan bayan sun gaba cin moriyarsu.
Matukar ba a samar da wani zabi na musamman ba, Afirka kamar sauran kasashe masu taso wa, za ta iya daukar hanya sabanin wannan.