Tun shekarar 2022 ne dai ake gwabza fada tsakanin Rasha da Ukraine, wanda a yanzu ke bayyana a yammacin Afirka ta hanyar diflomasiyya. Hoto: OTHERS

Daga Mazhun Idris

Yammacin Afirka da tuni ke fama da tashe-tashen hankula da sauyin yanayi da damalmalewar al'amuran siyasa da na zamantakewa, na iya fuskantar wata sabuwar matsalar, yayin da Rasha ke zargin abokiyar gabarta Ukraine, da bude wani "sabon babi a Afirka" a yaƙinsu na tsawon wata 30.

Yayin da kasar Rasha ke da dalilanta na ƙara taka tsan-tsan game da yadda Ukraine sauya dabaru fiye da abin da take yi a yaƙin, batun da ya fi daukar hankali a yanzu shi ne ko Yammacin Afirka na bari a shigar da shi cikin wannan rikici mai hadari.

Ukraine, wadda ke samun goyon bayan Amurka da Tarayyar Turai da NATO, ana hasashen tana aiki don neman ƙarin goyon baya daga wasu wuraren — ciki har da Afirka — don ta ƙara tunkarar wannan babban yaƙi na duniya.

A hannu guda kuma, ƙasashen Yammacin Afirka da dama, musamman waɗanda suke ƙarƙashin mulkin soja, suna juya wa Ƙasashen Yamma baya don cim ma muradunsu na ƙawancen soji da tattalin arziki da Rasha da China da sauran ƙasashe masu ƙarfin iko da suke son ƙawance da su.

Tuni dai Rasha ta zargi Ukraine da bude wani sabon ''gbabi'' a Afirka. Kasashen da ake kira da aka buɗe sabon babi da su a Afirka a yakin Rasha da Ukraine sun yi fice ne bayan takaddamar diflomasiyya tsakanin Ukraine da kasashen tsakiyar Sahel biyu na Mali da Nijar, kan taimakon da ake zargin Ukraine ta bai wa kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin.

Sergey Eledinov, manazarci mai zaman kansa kan harkokin tsaro na yankin Afirka, bai ga sha'awar da Ukraine ke da shi a nahiyar a matsayin wani sabon abu ko kuma abin mamaki ba.

"A baya dai Ukraine ta shiga ayyuka na musamman a Afirka," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Fito-na-fito

A ranar 25 ga watan Yuli ne 'yan awaren Abzinawa suka kai hari a wani sansanin soji da ke yankin Tinzaouatene a arewacin kasar Mali, wanda ya kai ga kwashe kwanaki uku ana gwabza fada, inda aka kashe sojojin Mali 47 da mayakan haya 84 na Rasha a Afirka, PMC Africa Corps (tsohuwar kungiyar Wagner).

Kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun kulla kawance tare da korar ƙasashen Yammacin Duniya. Hoto: Wasu

An yada bidiyoyin mutanen da aka kashe da na mayaan da aka kama a shafukan sada zumunta, wanda ke nuna yadda 'yan tawayen ke ikirarin samun nasara a kan sojojin gwamnati tare da rike tutocin Ukraine cikin murna.

"A bayyane yake cewa dakarun waje ne suka shiga wannan harin, inda suka yi sanadin salwantar da rayukan sojojin Rasha na Afirka," in ji Eledinov, wani jami'in sojan Rasha mai ritaya.

“An shirya aikin a tsanake, bisa ingantattun bayanai game da duk wani motsi na kungiyar,” in ji shi.

Kwanaki hudu bayan da aka fara kai harin, kafafen yada labarai na kasar sun rawaito kakakin hukumar leƙen asirin sojan Ukraine GUR, Andriy Yusov yana yin tsokacin da ake yi wa kallon tabbatar da goyon bayan kasarsa ga 'yan ta'adda a Mali duk da sanin cewa kasar da ke yammacin Afirka ƙawa ce ga Rasha.

Yusov ya shaida wa kafar yada labarai ta Suspilne cewa, 'yan awaren sun "karbi dukkan bayanan da suke bukata" domin kai wa sojojin Mali hari.

Ukraine wadda ke ke aika bayanai ga 'yan ta'adda domin kai farmaki kan abin da Kyiv ta kira "masu aikata laifukan yaki na Rasha" ana kallonta a matsayin mai bayyana aniyarta da gayya.

Harin martani na diflomasiyya

Ko da yake bayyana hakan bai yi karin haske ba kan yadda da kuma lokacin da aka kafa irin wannan hadin gwiwa ta soji tsakanin Ukraine da 'yan awaren Mali, kalaman na Yusov ya janyo ce-ce-ku-ce a fagen diflomasiyya.

A ranar 3 ga watan Agusta, maƙwabciyar kasar Mali, Senegal ta gayyaci jakadan Ukraine a birnin Dakar, Yurii Pyvovarov kan wani bidiyo da aka wallafa a Facebook, inda aka ji jakadan na cewa Kyiv ta bayar da "goyon baya ga harin ta'addanci" a Mali.

Ofishin jakadancin Ukraine da ke Senegal, wanda ya hada da Guinea da Guinea-Bissau da Cote d'Ivoire da kuma Laberiya ne ya wallafa bidiyon.

"Idan har ana son a yarda da bayanan da Ukraine ta fitar, za a iya daukar matakin da Ukraine ta dauka a matsayin wani shiri na yaki da Rasha (a nahiyar Afirka)," Eledinov ya shaida wa TRT Afrika.

A baya dai Kyiv ta zargi Rasha da daukar fursunoni daga gidajen yarinta domin tallafa wa yakin da take da Ukraine.

A baya-bayan nan dai jami'an kasar Rasha sun kai ziyara a kasashen yammacin Afirka da suka hada da kasar Mali domin bunkasa alaka. Hoto: @PresidenceMali

Sai dai kuma kasashen Nijar da Mali da ma wasu kasashen Yammacin Afirka sun bayyana matakin na Ukraine a matsayin cin zarafi ga kasar Mali da tsaronta.

A ranar 4 ga watan Agusta ne kasar Mali ta katse huldar diflomasiyya da Ukraine, inda ta zarge ta da taimaka wa 'yan ta'adda, wadanda sojojin Mali ke fafatawa da su don kakkabe kan iyakokinsu.

Kakakin gwamnatin Mali Amadou Abdramane, ya sanar a cikin wata sanarwa ta gidan talabijin cewa kasarsa za ta nemi kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi muhawara game da "kutsen Ukraine".

Ma'aikatar Harkokin Wajen Ukraine ta ce Mali ta yanke huldar da ke tsakaninsu "ba tare da gudanar da cikakken bincike na gaskiya kan al'amura ba...kuma ba tare da bayar da wata shaida da ke nuna da hannun Ukraine ba."

Kyiv ta soki matakin na Mali a matsayin na "gajeren tunanin da kuma yin gaggawa".

A ranar 6 ga watan Agusta, Nijar ta kuma sanar da yanke huldar diflomasiyya da Ukraine "nan take", ta kuma zargi Kyiv da "taimaka wa kungiyoyin ta'addanci" a Mali.

Kwanaki biyu bayan haka, wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Ukraine ta yi tir da zarge-zargen na Nijar, inda ta kira su da "marasa tushe kuma ba gaskiya ba". Har ila yau, ta yi watsi da zargin "tallafa wa ta'addancin kasa da kasa" da "ƙetare ƙa'idojin MDD da dokokin kasa da kasa".

Yaƙin cacar baka na sake dawowa

Gaskiya mai ban tsoro game da tsoma baki na kasashen waje a Yammacin Afirka, duk da sunan siyasar ƙasashen da ke adawa da juna kishiyoyin a can yankin Turai nesa da nahiyar, ya kawo mummunan yanayi ga rikice-rikicen Afirka.

Da alama abin da kowa ke tunani a Kyiv shi ne cewa Ukraine na buƙatar samar da wani babi na adawa da Rasha.

Masu sharhi dai na ganin shigar sojojin Ukraine da Rasha cikin yankin Sahel babu makawa zai haifar da ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a yankin da kuma ci gaba da zullumi ga al'ummar yankin.

Eledinov na kallon inuwar Amurka da Faransa a matsayin wata babbar giwa a cikin lamarin, inda ya yi wa "rawar da Ukraine ke takawa wajen yaƙi da mamayar Rasha" laƙabi da zamowa maslaha ga Ƙasashen Yamma biyu.

"Kada ku manta cewa yakin Rasha da Ukraine shi ma fada ne na aƘida a cikin tsarin karkatar da siyasa," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

TRT Afrika