Daga Sylvia Chebet
“Cin abinci dole ne; amma amfani da hikima wajen cin abinci fasaha ne,” kamar yadda wani masanin falsafa François de La Rochefoucauld ya bayyana.
Sai dai alamu na nuna cewa wannan fasahar ta kwace wa mutane da dama. A fadin duniya, mutane masu yawan gaske suna yawan ta’ammuli da na’ukan maiƙon da ake kira trans fats, wato na’ukan maikon da ba na asali ba, wadanda shugaban bangaren cimaka na Hukumar Lafiya ta Duniya, Dokta Francesco Branca ya bayyana a matsayin makiya lafiya mai inganci.
Kusan mutum 300,000 zuwa 500,000 ne suke mutuwa a duniya a sanadiyar irin wadannan maikon masu illa ga lafiya, inji Dokta Branca a tattaunawarsa da TRT Afrika.
“Irin wadannan maikon ne suke jawo ciwon zuciya, don haka akwai bukatar a daina amfani da su a girki,” in ji shi.
Irin wadannan maikon ne suke cushe jijiya, wanda hakan ke kusanto da barazanar kamuwa da ciwon zuciya da ma mutuwa.
“Irin wadannan maikon ba su da wani sanannen alfanu,” inji Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, Dokta Ghebreyesus.
“A takaice ma dai sinadarai ne masu illa da suke kashe mutane, wadanda bai kamata a ce ana amfani da su wajen girki ba. Lallai akwai bukatar a yi fatali da su baki daya,” in ji shi.
Wadanne irin maiƙo ne haka?
Daga jin sunan za a sha ko wani abu ne daban, amma na’ukan maiko ne da muke ta’ammuli da su kusan kullum. Na’ukan maikon trans fats da ake kira trans-fattu acids (TFA) wasu kalan maiko ne wadanda ba na asali ba; wadanda ko dai aka sana’anta su, ko kuma suka taru da kansu.
“Yawanci ana samar da trans fats ne a lokacin da ake daskarar da man girki domin hada wani abu. Misali, idan za a hada man bota, ana kara sinadarin hydrogen ne a man girkin domin ya daskare.”
Bayan bota da man girki, yawancin cimakan da aka sana’antawa samar da irin wadannan maiko masu cutarwa, kamar irin cimakan da ake gasawa irin su kek da biskit da wasu cimakan da ake sarrafawa. Yawancinsu suna dauke da sukari da gishiri masu yawan gaske.
Haka kuma za a iya samun maikon nan mai cutarwa a cikin nama da madarar dabbobin gida kamar shanu da tunkiya da akuwa. Wani abun kuma shi ne da wanda aka samar ta hanyar sana’anta wasu abubuwan, da wanda ya taru da kan shi, duka suna da illa ga lafiya.
Masana sun bayyana cewa ana kara samun amfani da irin wadannan maikon a ’yan shekarun nan ne saboda saukin da suke da shi idan aka kwatanta da man girki masu kyau da inganci.
Haka kuma suna da wasu siffotin kuma, kamar daskarewa cikin sauki, wanda hakan ya sa suke da saukin aiki.
Amfani da man girki a kasashe da dama yana ta’allaka ne da samuwarsa, da tsadarsa.
A cewar Dokta Branca, zai iya yiwuwa a maye gurbin na’ukan maikon da masu inganci ba tare da tattalin arzikin kasa ya samu tangarda ba.
“Kasashe za su iya yin tsari. Za su iya cewa ba ma son ganin mai iri kaza, ko su ce kada kowane irin abinci ya dauki sama da kashi 1 na maiko mai illa ga lafiya, ko kuma ma su hana amfani da shi baki daya. Akwai hanyoyin sanya dokoki masu yawa, wadanda za su tilasta masu masana’anta su gyara.”
Sai dai dole akwai bukatar idan an sanya doka, a rika bibiya domin cimma nasara kamar yadda Dokta Branca ya bayyana.
“Wannan abu ne mai sauki, kuma ko kwanan nan mun karrama wasu kasashen saboda yadda suka kafa wasu dokoki, kuma suka dabbaka su. Yanzu haka mutanen da suke wadannan kasashen ba sa amfani da irin wadannan maikon, wanda hakan ya sa suke kare kansu daga kamuwa da ciwon zuciya.”
A watan Janairun 2024, WHO ta karrama kasashen Denmark da Lithuania da Poland da Saudiya Arabiya da Thailand saboda kokarinsu na yaki da ta’ammuli da maiko masu illa.
Wadannan kasashen, “su ne kan gaba a duniya wajen tabbatar daina amfani da irin wadannan na’ukan maikon. Muna kira ga sauran kasashe da su yi koyi da su,” inji Darakta Janar na WHO.
Tsari mai kyau
A shekarar 2018, WHO ta daura damarar kawar da irin wadannan na’ukan maikon zuwa karshen shekarar 2023. Sai dai rashin cimma wannan nasarar na nufin kimanin mutum biliyan biyar suna cigaba da fuskantar barazanar kamuwa da ciwon zuciya da mutuwa.
“Mun yi zaton za mu iya kammala yaki da amfani da irin wadannan maikon a shekarar 2023,” inji Dokta Branca, jagoran bangaren cimaka na WHO.
Hukumar ta lafiya ta assasa wani shiri mai suna REPLACE domin karfafa gwamnatin kasashe wajen shirya dokoki da dabbaka su domin samun nasarar daina amfani da irin wadannan maikon baki daya.
Duk da cewa har yanzu ba a fara amfani da tsarin ba, Dokta Branca ya ce ana samun cigaba matuka a fadin duniya.
A shekarar 2023 kawai, an samu nasarar tsarin a kasashe bakwai, (Masar da Mexico da Moldova da Nijeriya da Macedonia ta Arewa da Philippines da Ukraine) kamar yadda jami’in na WHO ya bayyana.
“Tsarin zai karade duniya. Kamfanonin abinci na duniya da masu sarrafa man girki duk sun fahimci manufar tsarin. Kamfanonin man girki da dama sun fara canja tsarin aikinsu. Don haka, lallai akwai alamar nasara, kuma nan da dan lokaci kadan za a iya cin wannan nasara,” in ji Dokta Branca.
“Daina amfani da na’ukan maikon trans fat ba wani abu ne mai wahala. Za a iya yinsa ba tare da samun tangardar siyasa da tattalin arziki ba, saboda za a iya dabbaka shi, a samu nasara ba tare da kashe makudan kudade ba.
Ba a bukatar wadannan sinadaran masu ili, kuma babu wanda zai yi kewarsa idan aka daina amfani da shi,” inji Dokta Tom Frieden, Shugaba, kuma babban jami’in gudanarwa na Resolve to Save Lives ya bayyana.
“Muna samun nasara, amma kasashen da ba sa amfani da dokokin ba suna cikin barazana, domin za su iya zama kasashen da za a rika kai irin wadannan maikon. Akwai bukatar gwamnati da sauran kamfanonin abinci su tabbatar hakan bai faru ba,” in ji shi.
Yadda za a rage amfani da maiƙon trans fat
Masana sun ba da shawarar amfani da man da ke dauke da sinadarin polyunsaturated fatty, kamar wadanda ake samu daga masara da waken suya da gyadar Yarbawa, sai kuma man girkin da suke dauke da sinadarin monounsaturated fatty-acids irin wadanda ake samu daga zaitun da gyada da fiya da sauransu.
Duk da cewa nauyin kare al’umma daga amfani da irin wadannan na’ukan maikon ya rataya ne a kan gwamnati, suma daidaikun mutane akwai rawar da za su taka.
Daga cikin rawar da mutane za su iya takawa akwai rage amfani da abincin da ake gasawa, da rage cin nama da madarar shanu da tumaki da awaki.