Sabuwar tattaunawar sulhu wadda Turkiyya ke jagoranta ta alamta alamun ɗinke ɓaraka a tsakanin Habasha da Somaliya bayan an shafe watanni ana takun sakar diflomasiyya kan yarjejeniyar tashar jiragen ruwa da Habasha ta rattaba hannu da yankin Somaliya na Somaliland wanda ya ɓalle.
Habasha da Somaliland sun sanar a ranar 1 ga watan Janairu cewa, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da za ta bai wa Habasha damar shiga tekun Bahar Maliya inda ita kuma a ɓangarenta ta amince da Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
Habasha ita ce kasa mafi yawan jama'a a duniya wadda ba ta da teku. Ta rasa hanyar shiga teku lokacin da Eritrea ta balle a 1993.
Kasar Habasha ta kasance tana amfani da tashar jiragen ruwa a makwabciyarta Djibouti wajen shigo da kaya da kuma fitar da su. Firaiminista Abiy Ahmed ya dage kan cewa samun damar mu'amala da teku na da matuƙar muhimmanci.
Somaliya, wadda ta dauki Somaliland a matsayin wani bangare na yankinta, ta yi Allah-wadai da yarjejeniyar a matsayin cin zarafi da cin mutuncin yankinta. Tana zargin Habasha da burin mamaye wani yanki na Somalia, abin da Addis Ababa ta musanta.
Kungiyar Tarayyar Afirka, makwabtan yankin da manyan kasashen duniya sun goyi bayan kiraye-kirayen a mutunta yankunan Somaliya. Sun bukaci shugabannin kasashen biyu da su warware takaddamar ta hanyar tattaunawa.
Kokarin da ake yi na sulhu tsakanin ƙasashen biyu na yankin Kusurwar Afirka ya ci tura.
A wani mataki na baya-bayan nan na kawo karshen takaddamar, Turkiyya ta shiga tsakani, inda ta taka rawa a matsayin mai jagorantar tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.
Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya karbi bakoncin takwarorinsa na Habasha da Somaliya a birnin Ankara a ranar Litinin, inda suka tattauna kan hanyoyin da za a bi don magance sabanin da ke tsakaninsu "ta hanyar da za a amince da juna."
Wannan mataki ne da ba a taba yin irinsa ba tun bayan da rikicin ya barke.
"Yunkurinmu na samar da zaman lafiya, diflomasiyya da kuma fatan alheri ya sa mu gudanar da tattaunawa da samun matsaya guda a duk inda zai yiwu,” kamar yadda Fidan ya shaida wa manema labarai a Ankara a gaban Ministocin Harkokin Wajen Habasha da Somaliya bayan tattaunawarsu.
Mai shiga tsakani
A baya dai gwamnatin Somaliyan ta ce za ta shiga tattaunawa kan yarjejeniyar tashar jiragen ruwa ne bayan Habasha ta yi fatali da yarjejeniyar da ta kulla da Somaliland tare da bai wa jama'a hakuri.
Dangantakar da Turkiyya ke da ita ta tsawon lokaci da ƙasashen biyu ana ganin tana da matukar muhimmanci wajen cimma duk wata nasara a tattaunawar.
Bangarorin sun amince su hadu a Ankara a watan Satumba domin tattaunawa zagaye na biyu.
Masu sharhi a yankin Kusurwar Afirka sun yaba da matakin diflomasiyya na Turkiyya.
"Ina ganin ya kamata mu yi maraba mu kuma yaba wa gwamnatocin Habasha da Somaliya bisa haɗin kan da suka nuna wurin magance matsalolinsu na diflomasiyya," in ji Nuur Mohamud Sheekh, tsohon kakakin babban darektan kungiyar IGAD.
"Godiya ga gwamnatin Turkiyya saboda irin gudunmawar da ta bayar don gudanar da wannan muhimmiyar tattaunawa," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Babu tabbaci kan hanyar da za a bi wurin dawo da dangantaka mai kyau tsakanin ƙasashen biyu kamar yadda take a baya, sai dai ana da yaƙinin cewa shiga tsakanin da Turkiyya ta yi zai bayar da mafita.
"Turkiyya tana da kyakkyawar dangantaka da gwamnatocin biyu da kuma (Firaiministan Habasha) Abiy da Shugaba Hassan (na Somalia), "in ji Mohamud.
Don haka, ya bayyana Turkiyya a matsayin ‘’aminctacciyar mai shiga tsakani".
Ƙawance mai muhimmaci
"Na yi imanin cewa ministocin harkokin wajen Habasha da Somaliya sun amince su sake haduwa a watan Satumba, wanda hakan ke nuni da cewa a shirye suke su warware matsalar da ke tsakaninsu, " kamar yadda ya ƙara da cewa.
Ana ganin yankin da Somaliya take yana da matuƙar muhimmanci sakamakon yadda yake da kusanci da Bahar Maliya da Mashigar Tekun Aden.
A watan da ya gabata ne ta samu kujera a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wadda ba ta dindindin ba.
Turkiyya na daga cikin manyan ƙawayen Somaliya tun bayan da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya kai ziyararsa ta farko a Mogadishu a 2011. Turkiyyar ta jima tana horar da dakarun tsaron Somaliya da kuma kai wa ƙasar kayayyakin ci gaba.
Turkiyya ta gina makarantu da asibitoci da ababen more rayuwa tare da ɗaukar nauyin karatun wasu 'yan Somaliya domin su yi karatu a Turkiyya.
'Muna kyautata zato'
Habasha na daya daga cikin kasashen Afirka da ke da alaka mai karfi ta fuskar tattalin arziki da diflomasiyya da Turkiyya.
Manazarta dai na ganin cewa, warware takaddamar da ke tsakanin Somaliya da Habasha na da matukar muhimmanci ga samun kwanciyar hankali da ci gaban Gabashin Afirka da ma wasu wuraren, idan aka yi la'akari da ɗumbin kalubalen tsaro da tattalin arziki da ake fuskanta a yankin.
Wasu ƙwararrun na ganin warware rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu abu ne mai wahala.
Shi ma Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya amince da '' irin sarƙaƙiyar da ke tattare da lamarin."
Duk da haka, ya yi kyakkyawan fata. Tattaunawar farko da aka yi ta "bayar da dama ga duka ɓangarorin su bayyana abin da ke zuciyarsu da kuma bayar da dama duka su fahimci juna," kamar yadda Fidan ya bayyana.
"Muna kyautata zato kan abin da zai zo nan gaba"