Daga Sylvia Chebet
Tsarin tausayawa masu rauni yana da faida sosai. Daga mutanen da ke fama da wata matsalar sabo zuwa ga wadanda suke neman sauki bayan sun fuskanci wani balain, fahimtar yanayin bambancin bukatuwa na da muhimmanci matuka wajen yin adalci a rabon tallafi.
Annobar Covid-19 da aka fuskanta ta kara tunatar da duniya cewa alakar da ke tsakanin mutane ta wuce maganar makwabtakar kasashe, ko ra'ayi. Sannan yadda annobar da girgiza duniya baki daya ya nuna cewa akwai bukatar hadin kai da aiki tare a gaba domin samun sauki idan wata annobar ta zo.
Amma kamar yadda taron Majalisar Kiwon Lafiya ta Duniya karo 77 da aka yi a Geneva ya gano, samun hadin kan yana da wahalar gaske.
Bayan daukar kusan shekara biyu ana tattaunawa a kan yarjejeniyar duniya a kan yadda za a fuskanci annoba a gaba, ana fargabar samun matsaya a kan yarjejeniya ya samu tsaiko saboda matsayar da majalisar ta Kiwon Lafiya ta fitar.
An fara tsarin ne tun a shekarar 2021, lokacin da aka ba Hukumar Lafiya ta Duniya nauyin jagorantar tattaunawa domin fitar da yadda ya kamata a raba kudaden kare aukuwar annoba a nan gaba, da kuma fitar da tsare-tsaren yadda kasashen za su iya kiyaye aukuwar matsalolin.
Taron Majalisar Kiwon Lafiya na karshe da aka yi, wanda ya samu halartar wakilan kasashe 194 mambobin WHO ne lokacin da aka ba Hukumar Lafiya ta Duniya domin fitar da sakamakon tattaunawar da yarjejeniyar da aka cimma da kuma shirye-shiryen kasashen duniya.
Sai dai bayan kammala taron, daya daga cikin shugabannin kwamitin tsara yarjejeniyar, Roland Driece ya tabbatar da cewa kasashe da dama ba su amince da daftarin yarjejeniyar ba.
"Ba mu samu nasarar da muka yi tunanin samu ba a lokacin da muka fara tattaunawar nan," in ji shi, sannan ya kara da cewa tattaunawar tana da matukar muhimmanci, saboda muhimmancinta ga yan Adam.
Mai rajin kula da kiwon lafiya, Maziko Matemba, dan kasar Malawi, wanda shi ma ya halarci taron, yana cikin wadanda suka yi tunanin za a samu nasara.
Kasar Malawi da ke Gabashin Afirka na cikin kasashen nahiyar Afirka da annobar Covid-19 ta illata sosai saboda wasu kalubale irin su rashin kwararrun maaikata kiwon lafiya da sauransu.
“A game da samar da yarjejeniyar annobar nan, ya kamata ne yi amfani da zahiri. Idan har ba a yi abin da ya dace ba, to lallai za a barar da asalin dalilin shirya tattaunawar, inji Matemba a tattaunawarsa da TRT Afirka.
Kyakkyawan fata
Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa ya yi amannar za a cimma matsaya a kan yarjejeniyar.
A jawabinsa a ranar karshe ta tattaunawar, ya nanata cewa, Ba wai mun gaza ba ne, za mu cigaba da yin duk mai yiwuwa-tare da yakinin cewa za mu samu nasara-domin ganin mun cimma nasarar domin lallai ana bukatar wannan yarjejeniyar a duniya.
Wata shugabar kwamitin tattaunawar, Precious Matsoso, ita ma nananta maganar Ghebreyesus ta yi, inda ta ce, Za mu tabbatar mun yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da wannan yarjejeniyar domin lokacin da wata annobar za ta barke, ba za ta bar mu ba, in ji ta.
Daftarin farko na yarjejeniyar ya maida hankali ne a kan yadda za a raba riga-kafin Covid-19 a tsakanin manyan kasashe da kasashe masu tasowa.
Sai dai sabani a kan yadda za a fitar da labarin sababbin kwayoyin cuta da kuma kimiyyar yaki da su ne ya kawo tsaiko wajen tattaunawar.
Sabon daftarin kuma ya bukaci WHO ta karbi kashi 20 na samar da abubuwan da suke da alaka da annobar kamar kayayyakin gwaji da magunguna da riga-kafi. An kuma bukaci kasashe su bayyana irin yarjejeniyar da suka shiga da kamfanoni.
Kasashe masu tasowa da dama suna tunanin ba a yi musu adalci, kasancewar su ake nema su kawo samfurin kwayar cutar domin hada riga-kafi da magani, amma kuma su kasa samunsu idan sun fito.
Matsalar daukar nauyi
Matemba ya ce akwai bukatar Karin zuba kudade domin fuskantar matsalar.
Daga ina za a samu kudaden da za a yi wannan aiki? inji shi, sannan ya kara da cewa, ta yaya za mu tabbatar da cewa bangaren kiwon lafiya na samun isassun kudaden gudanarwa? Sannan mu tabbatar an samu ingantaccen kiwon lafiyar?
Matemba, wanda ya tattauna a game da sauyin yanayi da kiwon lafiya a taron, ya yi amannar cewa kiwon lafiyar alumma shi ne kan gaba a cikin matsalolin duniya da suke shafar Afirka.
Misali a Malawi, yanzu ne fa muke watstsakewa daga goguwar teku ta Cyclone Freddy. Sannan mun fuskanci karancin kayayyakin agaji saboda rashin kudade, in ji shi.
Annobar goguwar teku ta Freddy ta fara ne a Maris na 2023, sannan an dauki kwana 36 ana yi, wadda ta yi sanadiyar raba akalla mutum 500,000 da muhallansu, sannan ta ɓarnata dukiyoyi da aka ƙiyasta ya kai biliyoyin dala.