Daga Firmain Eric Mbadinga
Kwazon da matashiya Ny Aro Andriamiarosoa take nunawa a matsayinta na mai fafutuka kan sauyin yanayi ya zo daidai da girman aikin da ke gabanta.
A kasarta ta asali Madagascar, an fuskanci tasirin sauyin yanayi, inda aka dade ana fama da matsalar fari a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2022 a yankin kudancin kasar, yanayin da ya sanya wasu 'yan kasar neman abin da za su kai bakin salati.
Dubban iyalai na ci gaba da rayuwa a karkashin barazanar guguwa ta Batsirai, wadda ta kashe mutane kusan dari tare da raba kusan 30,800 da muhallansu a shekarar 2022.
Ana danganta tsawon lokacin da matsalar fari ta dauka a kudancin kasar da kuma karuwar wasu lamura na yanayi kamar mahaukaciyar guguwar da ke cikin iftil'in sauyin yanayi da kasar ke fuskanta.
A cewar kungiyar abinci da noma, kashi 95 cikin 100 na mutanen da ke fuskantar matsalar karancin abinci a kudancin Madagascar sun dogara ne kan noma da kiwon dabbobi da kuma kamun kifi.
A 'yan shekarun nan, yankin ya fuskanci karancin ruwan sama sakamakon matsalar sauyin yanayi, abin da ya sa aka samu raguwar hanyoyin samar da abinci, musamman shinkafa da rogo da kuma ragi da tabarbarewar ayyukan makiyaya.
Wadannan batutuwa na sauyin yanayi ne suka sanya Andriamiarosoa ba da himma wajen amfani da kwarewarta a matsayin injiniya a fannin aikin gona da kuma kwazo da hikimar hada mutane don gwagwarmayar ceton rai.
"Na yi imanin cewa ci-gaban wani yankin tsibiri kamar Madagascar ya dogara ne kan hada sauyin yanayi cikin kowane tsarin tattalin arziki," kamar yadda Andriamiarosoa ta shaida wa TRT Afrika.
Matashiyar mai sha'awar siyasa da jagoranci, Andriamiarosoa ta shiga Shirin Horar da matasa ayyukan Shugabancin a shekarar 2022 da kuma Shirin Shugabancin Matasan Afirka a 2023.
Kazalika Andriamiarosoa ita ce shugabar kungiyar CliMates Madagascar, da ke aikin tattara shawarwari da daukar matakai, inda ta hada masu aikin sa-kai da dalibai da kwararrun matasa wadanda ke tunkarar kalubalen sauyin yanayi.
Takan shirya horo na sanin makamar aikin a-kai-a-kai a tarurrukan matasa da sansanonin da aka tsara don mahalarta su ilimantar da kawunansu kan sauyin yanayi.
A watan Afrilun bara, Andriamiarosoa ta hada kusan matasa 50 a wani aikin kwanaki hudu da aka yi a tsakiyar dajin Madagascar da ke Antananarivo, taron da ya kai ga kafa kungiyar matasa ta kasa don muhalli da sanin halittu da sauyin yanayi.
Daya daga cikin manyan manufofin kungiyar shi ne bayar da tallafi don yaki da kwararowar hamada.
"A halin da ake ciki yanzu, na fi mayar da hankali wajen inganta rayuwa da wayar da kan matasan Malagasy game da kalubalen sauyin yanayi a wannan zamanin namu, ko ta hanyar siyasa ko taron wayar da kan jama'a a makarantu da jami'o'i.
Aikin da na yi kwanan baya na gudanar da CliMates shi ne shirin 'Climate Presidential," in ji Andriamiarosoa.
Matakin Gaba
A lokacin zaben Madagascar a shekarar 2023, kungiyar CliMates ta yi amfani da shafukan sadarwa na intanet wajen yada shirye-shiryen al'umma daga 'yan takarar zaben yayin da suke wayar da kan jama'a game da sauyin yanayi.
UNESCO ta shiga yakin
A watan Oktoba 2021, Agnès Callamard, sakatare-janar na kungiyar Amnesty International, ta fitar da wata sanarwa a gabanin taron COP26 a Glasgow.
"Madagascar na kan gaba wajen fuskantar matsalar sauyin yanayi. A sakamakon haka, mutane miliyan guda suna fuskantar iftila'i na fari da kuma take hakkinsu na rayuwa da kiwon lafiya da samun abinci da ruwa, hakan na haifar da yanayin yunwa," a cewar sanarwar.
''Wannan yana nufin hadarin yunwa. Wannan shi ne abin da ke faruwa a halin yanzu. Hasashen canjin yanayi ya nuna cewa fari zai ta'azzara kuma zai yi tasiri ga jama'a a kasashe masu tasowa," in ji ta.
Bayan taron Majalisar Dinkin Duniya, illar sauyin yanayi ta kara ta'azzara, lamarin da ke kara jefa rayuwar jama'ar Madagaska cikin hadari.
"Duk da cewa Madagaskar a kebe take, amma matsalolinmu ba a kebe suke ba, muna cikin nahiyar Afirka, kuma kalubalenmu da al'amuranmu iri daya ne," kamar yadda Andriamiarosoa, wacce ta halarci wata tattaunawa a taron COP28 na baya-bayan nan da aka gudanar a Dubai, ta shaida wa TRT Afrika.
Dauwamammiyar riba
A hanyar shirin "Climate Presidency, " aikin da damarmakinsa ya wuce iyakar lokacin zabe, Andriamiarosoa ta samu damar yin magana game da ka'idodin muhalli da UNESCO ta tsara tare da wayar da kan jama'a game da dangantakar da ke tsakanin siyasa da yanayi.
Baya ga wannan aiki, ayyukan hadin gwiwa tare da matasa daga wasu nahiyoyi sun kasance wani bangare na ayyukan CliMates Madagascar.
“Shirin matasa tare da gidauniyar Africa-Europe shi ma ya mayar da hankali kan hakan, burinmu tare da gidauniyar Africa-Europe shi ne samar da wata kafa da za ta bai wa matasa na nahiyoyin biyu damar yin mu’amala da kuma musayar ra'ayoyi, da nufin kara wa matasa hanyoyin daukar matakai da yanke shawara,” in ji Andriamiarosoa.
A taron COP28, wanda ya tattaro kimanin mahalarta 7,000 cikin kwanaki 11, muhimmiyar sanarwar da aka yi ta hada da "mafarin karshen" zamanin makamashin burbushin halittu da kuma sanar da hanyoyin yin juriya ga illar sauyin yanayi.
"Yankunan Madagascar da kuma yawan al'ummar duniya na cewa akida da al'adunmu a wasu lokutan suna watsi da muhimmancin yara da mata wajen yanke shawara," in ji Andriamiarosoa.
Jajircewarta ga Alliance Nationale de la Jeunesse Malagasy pour la Biodiversité, da le Climat et la Lutte Contre la Desertification ta kasance dauwamammiya
Sannan tana da kudirin shirya wata bita a yankin kan muhimman batutuwa da kuma shawarar da taron COP28 ya yanke, bisa ga la'akari da cewa "yakin zai soma ne a lokacin da taron ya zo karshe ".