Gwamnatocin mulkin soji a Mali da Burkina Faso da Nijar sun ci gaba da aiwatar da shirinsu na sauya sunayen tituna a birane da dama a ƙoƙarinsu na kare asalinsu da kuma neman 'yanci. / Hoto: Reuters

Daga Firmain Eric Mbadinga

An ga yadda tarihi ke ciki da yadda ƙasashe ke sauya sunayen birane da tituna da wurare masu muhimmanci saboda dalilai da dama, a mafi yawan lokuta saboda dawo da martabar ƙasa ta fuskar al'ada da cin gashin kai.

Irin waɗannan sauye-sauye kan zo a lokacin da wasu muhimman al'amura ke faruwa kamar na siyasa da kawo ƙrshen mulkin mallaka da hamɓarar da mulki ko kuma haɗin kan wani yanki.

Gwamnatocin mulkin soji a Mali da Burkina Faso da Nijar sun ci gaba da aiwatar da shirinsu na sauya sunayen tituna a birane da dama a ƙoƙarinsu na kare asalinsu da kuma neman 'yanci.

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traoré, da takwarorinsa na Nijar Abdourahamane Tchiani, da Assimi Goita na Mali, dukkansu sun ɗauki matakin kawar da sunayen janar-janar da manyan 'yan siyasa na Faransa tun na zamanin mulkin mallaka daga jikin gine-gine da tituna.

Fitattun sunaye kamar su Louis Faidherbe da Michel de Montaigne na daga cikin sunayen da aka cire a wasu wurare a wadannan ƙasashe uku na Ƙungiyar Ƙawancen Sahel.

An jima ana fama da takun-saƙa tsakanin ƙasashen uku da Faransa. Suna zargin tsohuwar ƙasar da ta yi musu mulkin mallakar da jawo rashin zaman lafiya da son tayar da tarzoma.

Ƙaruwar fushi da tashin hankali

A shekarar 2022, Ministan Harkokin Wajen Mali Abdoulaye Diop ya sanar da Majalisar Dinkin Duniya cewa ƙsarsa za ta iya samar da "hujjojin da ke nuna yadda Faransa ke son tayar da tarzoma."

Abu na baya-bayan nan shi ne yadda ƙsashen uku suka yi irin waɗannan kalamai da ke zargin yadda Faransa ke amfani da Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin KAsashen Afirka ta Yamma, ECOWAS wajen rusa harkokin tattalin arzikinsu.

A yayin da shirin sauya suaneyn titunan ke ƙara samun karɓuwa, Burkina Faso ta bayyana cewa son kare martaba da tarihin Afirka ne ya sa take sauya sunayen daga na Faransawa.

A watan Oktoban 2023, an sauya sunan titin Boulevard Charles de Gaulle da ke babban birnin ƙasar Ouagadougou zuwa Boulevard Thomas Sankara, wato sunan tsohon Shugaban Ƙasar da aka kashe

Karuwar kyamar Faransa ce ta sa aka kori sojojin Faransa a yankin Sahel tare da ficewa daga kungiyar ECOWAS zuwa kawancen kasashen Sahel. /Hoto: Wasu

Shekara ɗaya bayan nan, Nijar ta sayua sunan titin Avenue Charles de Gaulle da ke Niamey zuwa sunan Djibo Bakary, wani muhimmin mutum da ya yi fafutukar samun 'yancin ƙasar.

Mali ta bi sahu a ranar 19 ga watan Disamba, inda ta sauya sunan titin Avenue de la Cedeao (wato sunan ƙungiyar ECOWAS da Faransanci) a Bamako zuwa sabuwar ƙungiyar AES.

Mabambantan ra'ayoyi

Fitaccen dandallin nan na Mali da ke gaban Majalisar Dokoki na nuna kasantuwar Mali a tarihi, inda yake ɗauke da alamu irin na zane-sane da addini kamar dai na fitaccen Masallacin Djenné.

Ginin L'obélisque des idéogrammes da ke Bamako na ɗauke da fitaccen rubutun Sundiata Keita na Nko, wato "Jirgin ruwa na Mali na iya girgiza, amma ba zai taba kifewa ba."

Tchanga Chérif Tchouloumbo, wani ɗalibi daga Niamey na ganin wannan matakin ba shi ne abin da ya dace ba.

A ganinsa, magance matsala irin wannan ta fi gaban a yi ta da sauya sunayen wurare kawai.

Tchouloumbo da Doumbia sun dage cewa sun fi damuwa da ganin shugabanninsu su mayar da hankali wajen inganta tsaro.

Shi kuwa Issa Ibrahim Alou daga Niamey ya yarda da muhimmancin sauya sunayen wuraren zuwa na tsantsar Afirka da ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso ke yi.

"Mu, Ƙungiyar Matansan Nijar mun daɗe muna son a ɗauki wannan matakin. A yanzu da hakan ke faruwa, muna ganinsa a matsayin abu mafi kyau. Mun yaba wa hukumomin mulkin sojan a wannan aiki na mayar da ƙasashen Afirka zalla a matsayin wani ƙoƙari na samun cikakken 'yanci," ya shaida wa TRT Afrika.

Kyaftin Ibrahim Traoré na Burkina Faso, Abdourahamane Tchiani na Nijar, da Janar Assimi Goita na Mali sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar kafa kawancen kasashen Sahel a shekarar 2023. Hoto: Others

Fiye da bambance-bambancen yanki

Dr Massamba Guèye, wani mai bincike, marubuci kuma wanda ya samar da gidan adana kayan tarihi na Maison de l'Oralité et du Patrimoine da ke birnin Dakar na based in Senegal, ya yi amanna cewa lamari ne da ya wuce batun mulki ko bambance-bambancen yanki.

Ya yi amanna cewa kamata ya yi a tunkari batun daga bangaren asali da al'ada "a ganina, bai kamata a ɗauki 'yan mulkin mallaka tamkar wasu gwaraza ba a Afirka."

Idan aka saka wa titi sunan wani abu, to haka al'ummomi masu tasowa za su ɗauke su a matsayin abu mai kyau.

Bai kamata a mutunta mutanen da suka yi mana mulkin mallaka a matsayin wasu gwaraza ba," in ji Dr Guèye.

"Idan ana so a dinga tuna wani aiki mai kyau, to fa sai an sauya sunayen tituna don al'umma su girmama abin. Sannan yana da kyau a sauya sunayen duk wani abu da ya shafi zamanin mulkin mallaka."

Lokaci na farko da aka fara ƙoƙarin mayar da sunayen abubuwa na Afirka shi ne shekarun 1970, inda tsohon Shugaba Mobutu Sese Seko na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ya daina amfani da sunansa na Faransanci, Joseph-Désiré.

Gidaje da wuraren taruwar jama'a ma na buƙatar a mayar da su sunayen Afirka zalla.

Fitaccen mai kishin Afirka Kyaftin Thomas Sankara ma ya yi irin wannan ƙoƙari na sauya sunan ƙasarsa daga Turanci Upper Volta, zuwa Burkina Faso.

Wani mai sharhi kan al'amuran siyasa da tsaro Mubarak Aliyu ya yi imanin cewa lamarin ya samo asali ne daga muhimman abubuwa guda biyu - kawancen tattalin arziki da ya fi amfanar bangare ɗaya tsakanin Faransa da kasashen da ta yi wa mulkin mallaka da kuma tasirin sojojin Faransa a wasu kasashe.

TRT Afrika