Shugabanin kasashen Burkina Faso, Mali, Sanagal, Mali da Chadi wadanda na daga cikin wadanda suka kawo karshen alakar soji da Faransa.

Daga Emmanuel Onyango and Susan Mwongeli

Ga dukkan alamu mamayar Faransa a kasashen da ta yi wa mulkin mallaka ya kare, a yayin da ake ci gaba da watsi da Paris a yankin.

A cikin 'yan watanni, guguwar adawa da Faransa a Yammaci da Tsakiyar Afirka ta sanya manyan kawayen Faransa a fannin tattalin arziki da ayyukan soji sun juya mata baya.

Na baya-bayan nan su ne Chadi da Senagal, wadanda suka soke yarjejeniyar ayyukan soji da Paris a makon da ya gabata.

A manyan garuruwan yankin an bayyana bacin rai game da Faransa, inda dandazon masu zanga-zanga suka dinga ɗaga tutocin kasashensu suna kira ga Faransa da ta bar yankin baki daya.

A Nijar, kwanaki kadan bayan sojoji sun karbe mulki, wani dandazon jama'a da ke adawa da Faransa ya taru a gaban Ofishin Jakadancinta a babban birnin Niamey, tare da yin kira ga ma'aikatansa su bar kasar. Wannan ne lokacin da aka yi sakin da babu kome.

Ƙarfin mullkin mallaka

Ƙwararru sun bayyana cewa yadda Faransa a shekarun nan ta ƙi yarda ta ƙyale kasashen da ta yi wa mulkin mallaka su sakata su wala - abin da ake kira FaransAfrika- ne babban dalilin d aya sanya ta ci gaba da aiki da karfin mulkin mallaka a tsakanin kasashen.

Misali, Har yanzu a Faransa ake buga kudin Saifa (CFA), wanda ake amfani da shi a kasashen Afirka 14. Har zuwa baya-bayan nan, sama da sojojin Faransa 6,000 ne ke barbaje a kasashen Afirka daban-daban da nufin za su taimaka wajen yaki da ta'addanci.

Dadin daɗawa, ƙarfin ikon tattalin arzikin Faransa, musamman wajen hakar ma'adanai, da kuma yadda take juya shugabannin siyasa ta kowacce hanya, sun zama manyan abubuwan d aake alantawa da tabarbarewar tattalin arzikin yankin.

"(Guguwar adawa da Faransa) ta faru a tarihi sakamakon abubuwa da al'amura daban-daban da suka faru.

"Alakar ta ƙara sakwarkwacewa ne, musamman kan batun karfin ikon juya kai, inda kasashen Afirka da dama suke gwagwarmayar samun cikakken karfin iko da yin mulki yadda suke so tare da samar damnaufofin tsaro da cigabansu da kan su," in ji Tighisi Amare, Mataimakiyar Daraktan Shirye-Shiryen Afirka a Chatham House, ta fada wa TRT Afrika.

Kawo karshen hadin kai

A makon da ya gabata ne Chadi ta bi sahun da sauran kasashen yankin Sahel, ciki har da Nijar da Mali wajen kawo karshen yarjejniyar ayyukan soji da Faransa da ta y musu mulkin mallaka.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Chadi ta ce lokaci ne da kasar ya kamata ta "ta samu cikakken karfin mulkin kanta da tsara manufofi d akawance duba ga muhimman abubuwan da kasar ke bukata."

Senegal ta biyo baya kwana guda, inda Shugaban Kasar Bassirou Diomaye Faye ya yi kira ga Faransa da ta rufe sansanonin sojinta da ke kasarsa.

A jawabin da ya yi a Fadar Shugaban Ƙasa ya ce "Senegal kasa ce mai 'yancin kai, kasa ce mai cikakken iko, kuma karfin mulki bai yadda da wanzuwar sojojin wata kasa a iyakokinta ba."

Karfin fada a jin Faransa a Yammaci da Tsakiyar Afirka na raguwa, kuma kasashe irin su Turkiyya, da ke kulla dangantaka mai kyau da kasashen Afirka ke maye gurbin ta.

"Tun 2009 Turkiyya ta yi gaggawa wajen zama babbar mai fada a ji a Afirka. Irin dabarun da ta bi na da farkarwa sosai," in ji Amare.

"Ta fara amfani da karfafa diplomasiyya, wanda ya sanya ta ninka ofisoshin jakadancinta da ke nahiyar har sau hudu, sannan manyan shugabanninta suka dinga ziyartar kasashen Afirka.

sannan matakin ya ƙara ƙarfi a 2011, lokacin da ta mayar da Somaliya kan taswira bayan ware ta da aka yi na tsawon shekaru saboda rashin tsaro da ke kasar."

Amfanar juna

Dabarar ita ce ta a dauki matakan da kowane bangare zai amfana a bangarorin tsaro, kasuwanci da gina kasa.

"Kasashen Afirka na neman manyan kasashen duniya da z asu yi aiki tare. Ba sa son su zama suna alaka da kasa daya kawai, ko a tsakanin kasashe kadan.

Suna neman fadada hanyoyin da za su dinga sabun abubuwa daban-daban ta wadannan alakoki," a cewar Amare.

"Idan aka kalli yanayin Turkiyya, za a ga akwai damar samun kai fasahar kere-kere da za ta mayar da hankali ga hadin kai na tsawon lokaci - da kuma bayar a horo tare da kara girman masnaa'antunsu da ma zama kasashen da suka ci gaba, wanda fifiko ne ga kasashen Afirka."

Hakan ya sanya adadin kasuwanci da Turkiyya da Afirka karuwa zuwa ninki takwas a 'yan shekarun nan, inda ya haura Yuro biliyan 40, kamar yadda alkaluman kamfabin dillancin labarai na Anadolu suka bayyana.

TRT Afrika