Daga Murat Sofuoglu
A daidai lokacin da Turkiyya ke cika shekaru takwas da yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, Ankara na ci gaba da jiran Amurka ta miƙa mutanen da ke da alhakin harin da aka kai wa dimokradiyyar Turkiyya da al'ummarta a ranar 15 ga watan Yuli, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 253 tare da jikkata wasu da dama har fiye da 2,700.
Fetullah Gulen, shugaban kungiyar 'yan ta'adda ta Fetullah (FETO) yana kula da ayyukan ta'addanci daga gidansa da ke Pennsylvania tun shekarar 1999.
Duk da yawan buƙatun da Turkiyya ta miƙa na cewa Amurka ta ba da shi, Washington ba ta miƙa shi ga ƙawayen nata na NATO ba, abin da ya fusata Ankara tare da sanya jami'ai da dama suka nuna shakku kan ingancin ƙawancen siyasa da soja da aka shafe tsawon lokaci ana yi tsakanin kasashen biyu.
Duk da adawa ɓacin rai da Turkiyya ta sha nunawa, Amurka na ci gaba da bai wa ƙungiyar YPG reshen PKK ta Siriya kariya, wacce Washington da Ankara da NATO da EU suka ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta'addanci.
“FETO a matsayin kungiyar siyasa, ta zama wani ɓangare da Amurka ke amfani da ita don yaƙin sunƙuru da tashe-tashen hankula a faɗin duniya. Ma’ana, kungiya ce da ta iya yin tasiri a madadin Amurka a Turkiyya da ma duniya baki daya,” in ji Abdullah Agar, wani mai sharhi kan harkokin soji a Turkiyya.
Yayin da Gulen ya kasance mai wa'azi, kuma mabiyansa ke nuna kansu a matsayin wata ƙungiyar addini, a cewar Agar, ba wai addini suke yaɗawa ba, har ma da manufofin siyasa, kuma suna aiki a cikin al'umma daban-daban a duk faɗin duniya.
"A Turkiyya FETO ta faro, amma ta yi sojan gona a matsayin ƙungiyar Musulunci, tana kare muradun Ƙasashen Yamma da Amurka ba a Turkiyya kawai ba har ma da sauran ƙasashen duniya," Agar ya shaida wa TRT World.
'Kadara mai muhimmanci'
Idan har Amurka ta miƙa wa Turkiyya Gulen, zai iya nufin kawar da ko kuma gazawa wajen kare wanda take amfani da shi wajen yaƙin sunƙuru na duniya, wanda zai iya haifar da cece-kuce a cikin harkokin tsaro da siyasar kasar ta Arewacin Amurka da kuma yin illa ga amincin Washington.
A cewar Agar, hakan zai kuma iya yin tasiri a kan sauran ƙungiyoyin da ake amfani da su wajen yaƙin sunƙuru a irin su YPG/PKK a Siriya,
Daga wannan bayanin, za a iya fahimtar dalilin da ya sa Amurka ke ci gaba da bai wa FETO kariya.
"A ɗaya ɓangaren kuma, akwai haɗurra a yiwuwar Amurka ta miƙa wa Turkiyya Gulen, ta fannin bankaɗa munanan ayyukan FETO da alaƙrta da ƙasashen duniya. Bayan haka, idan har Gulen ya shiga hannun Ankara, to tasirin FETO da Turkiyya da ma sauran sassan duniya zai rushe," in ji Agar.
A hannu guda kuma, Agar ya ce ikirarin da FETO ke yi cewa su Musulmai ne masu sassaucin ra'ayi ƙarya ce tsagowanta da Amurka da Ƙasashen Yamma ke amfani da ita domin yaudarar al'ummomin Musulmai a fadin duniya, da kuma hana su tabbatar da nasu 'yancin na siyasa da tattalin arziki da manufofinsu.
Sami al Arian, daraktan Cibiyar Nazarin Musulunci da Al'amuran Duniya a Jami'ar Sabahattin Zaim da ke Istanbul, wanda ya yi bincike game da kungiyar tsawon shekaru, ya ce Washington "na kallon kungiyar a matsayin wani makami da za ta yi amfani da shi wajen cusgunawa Turkiyya."
A yayin da Amurka ba ta son ta fito ƙarara ta bayyana goyon bayanta ga kungiyar da ta kitsa yunkurin juyin mulki a shekarun da suka wuce a Turkiyya, kasa ta biyu mafi karfin soji a NATO, Amurkan na da damuwa game da manufofin Turkiyya, waɗanda ke yin tirjiya ga manufofin manyan ƙasashen duniya, in ji Arian.
A 2019, Turkiyya ta sayi garkuwar makamai masu linzami samfurin S-400 daga wajen Rasha, bayan Amurka ta ƙi biyan bukatar garkuwar Patriot da Ankara ta nema.
Wannan ya janyo tsama a tsakanin kasashen biyu ƙawaye a NATO. Haka zalika Amurka ta ki baiwa Turkiyya jiragen yki samfurin F-35, ta cire Turkiyya daga aikin samar da jiragen, wanda ya janyo matsaloli.
Turkiyya ta kuma dauki matsayi na daban a rikicin Ukraine, domin ganin an kawo karshe zubar da jinin, ta karfafa alakarta da Rasha, maimakon sauran kasashen Yamma.
A baya-bayan nan Turkiyya ta bayyana niyyarta na shiga Kungiyar BRICS, kawancen da babu wata kasar Yamma a ciki da aka kulla bayan yakin cacar baki. BRICS ta hada da Rasha da China da India.
Ba kamar sauran kasashen Yamma ba, Ankara ta goyi bayan kungiyar gwagwarmaya ta Falasdinawa da ke kalubalantar masu rajin kafa kasar Yahudawa a Gaza, Turkiyya ta dinga karbar bakuncin shugabancin Hamas, tana kuma kira ga Amurka da ke goyon bayan Isra'ila kan ta nemi Tel Aviv ta zuana da a teburin sulhu da Falasdinawa.
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da shugaban siyasar Hamas Ismail Haniyeh a Istanbul a watan Afrilu don tattauna yadda za a kai kayan agaji zuwa Gaza.
"Sun yi kokarin sauya manufofin Turkiyya sabod Ankara, a shekarun da suka gabata, na ta kokarin dabbaka manufofinta na kanta, tana kokarin tsaya wa da kafafuwanta wajen yanke hukunci d akarfin ikonta a yankin, tana kokarin taka babbar rawa a dukkan al'amuran yankin da suka shafi Amurka, wanda suna zama kalubale da cikas ga ayyukan Amurka a yankin." in ji Arian.
Tabbas Gulen an yi amfani da Gulen "watakila ta bangaren tattara bayanan siri da leken asiri, CIA da wasun su" a batun matsayin Turkiyya a siyasance, in ji Arian.
"A ko yaushe za su iya amfani da su wajen batutuwan da suka shafi sabani tsakanin Turkiyya da Amurka."
Matthew Bryza, tsohon jami'in diplomasiyyar Amurka, na da ra'ayin cewa dalilan da suka hana a mika Gulen sun shafi "tsaurara" dokokin shari'a na Amurka, ba wai batutun yanke hukuncin 'yan siyasa ba.
Amma Bryza ya kuma shaida wa TRT World cewa "akwai kyakkyawar fahimta a cikin gwamnatin Amurka kan cewa Fethullah Gulen na da hannu a yunkurin juyin mulkin da aka yi a Turkiyya."
A wata tattaunawa da TRT World a baya, Richard Falk, farfesan dokokin kasa da kasa ya yi nuni yiwuwar hannun Amurka a yunkuri n juyin mulkin yana mai cewa "bayanai na karara" sun nuna cewar masu shirya juyin mulkin sun samu umarnin su ci gaba da aikinsu daga Washington.
A daren 15 ga Yuli, a loakcinda John Kerry, Ministan Harkokin Waje na lokacin, na ziyara a Moscow inda ya fitar da sanarwar kira da dakatar da duk wata tarzoma, wanda hakan ke nuni da Amurka ta san za a yi juyin mulkin, in ji Arian.
"Tunda dai sun san da wannan yunkuri na juyin mulki. kenan suna da hannu a cikinsa." in ji shi
Alaƙa da Yahudawan Zionist
Arian ya kuma ja hankali da wata gaɓa mai muhimmanci, babbar alaƙar Gulen da Yahudawa masu rajin kafa kasar Yahudu a Birnin Kudus, wanda hakan na da tasiri ga 'yan siyasar Republican da Democrat. Ya ce "Gulen a Amurka na ta ƙara kusantar Yahudawa da ra'ayoyinsu."
Ya ci gaba da cewa FETO na shirya ayyuka da taruka a Amurka don faɗaɗa ƙawance da alaƙarsu da Yahudawa.
Duk da cewar a karkashin mulkin jam'iyyar Democrat aka fara kokarin ganin an dawo da Gulen zuwa Turkiyya da Amurka, duk da tsauri da rikita-rikitar tsarin shari'ar Amurkan, Republican ma sun yi adawa da wannan bukata saboda a koyaushe FETO na neman wani da ke goyon bayansu a daya bangaren, in ji Arian.
"Za su taimaka musu. Masu rokon Yahudawa za su fara sauya wa wadannan mutane wajen aiki, a kusa ko a nesa, dama ko hagu, 'yan Democrat ko Republican, suna amfani da wannan hanya, suna ma amfani da damrmakin siyasar daya bangaren," in ji farfesan.
A baya, Gulen ya sha fitar da sanarwar goyon bayan Isra'ila. Misali, a loakcin da Isra'ila ta kai wa jirgin ruwan Mavi Marmara hari, wanda na daga kayan taimakon da ake kaiwa Gaza na kasa da kasa da manufar bude hanyar shiga Gaza da sojojin Isra'ila suka rufe, ya yi watsi da cewar kayan taimako ne za a kai.
Harin na Isra'ila ya janyo mutuwar 'yan kasar Turkiyya 10.
A tataunawarsa ta farko a Amurka a 2010 ya fada wa jaridar Wall Street Journal cewar ya kamata a ce masu shirya tafiyar su nemi izinin Isra'ila, yana bayyana aikinsu a matsayin "alamar bijirewa mahukunta".
Arian na da ra'ayin cewa ra'ayin Gulen game da Isra'ila na da amfani ga manufofin masu son kafa kasar Yahudawa a Kudus da ma yakin da suke yi da Falasdinawa.
"Gwamnatin Isra'ila da 'yan Zionist na son amfani da Gulen a matsayin wani makami na kalubalantar Turkiyya kan ta janye hannayenta daga al'amuran Falasdinu sannan kar ta goyi bayan Falasdin kamar yadda gwmanatin Turkiyyan ke yi tsawon shekaru." in ji shi.
Mece ce manufar Gulen?
A wajen kasar Turkiyya, yunkurin juyin mulkin 15 ga Yuli alama ce karara ta manufar shugaban FETO na son kifar da gwamnati.
"Idan ka yi zuzzurfan kallo ga wadannan manufofi, za ka samu cewa bai damu sosai game da shugabancin dimokuradiyya ba ko aiki da doka da oda ta hanyar wakiltar mutane," in ji Arian.
"A saboda haka, ko ma menene manufarsa, wani abu ne da ya yi na neman kwace mulki ta hanyar karfin soji sannan ya zo ya kawo wasu ka'idoji nasa, akidunsa, ra'ayinsa da yake ta ɗaɓɓakawa da kira gare su tsawon shekaru," in ji farfesan.