Dalilan da suka sa gwamnatin Nijar ta yanke huldar soji da Amurka sun kasance batutuwan da masu sharhi suka fi tattaunawa a tsakaninsu: Photo/Facebook/Shugaban Jamhuriyar Nijar  

Daga Abdulwasiu Hassan

A wani gagarumin sauyin tsari, gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yanke huldar hadin gwiwa da sojojin Amurka.

Yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu a shekarar 2012 ta bai wa sojojin Amurka da ma'aikatan farar hula damar yin aiki a Nijar.

Sojojin Amurka sun dade suna gudanar da ayyukansu a wani babban sansanin sojin sama a birnin Agadez mai tazarar kilomita 920 daga Yamai babban birnin kasa, inda suke amfani da wajen ta hanyar zirga-zirgar jiragen marasa matuka da ayyukan leken asiri da dai sauran su.

Wannan wuri da ake aije jiragen yaki mara matukan ya kai kimanin kudin Amurka dala miliyan 100, sannan yana dauke da sojojin Amurka 1000, sai dai sannu a hankali Nijar na ci gaba da nisanta kanta daga kasashen yamma ciki har da Faransa wacce ta mata mulkin mallaka tun bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi mata a watan Yulin bara.

Babu alamar da ke nuna cewa, kasancewar sojojin Amurka a Nijar yana taimaka wa kasar wajen shawo kan matsalolin tsaron da ta ke fama da shi, a cewar wani mai sharhi kan harkokin siyasa Malam Salissou Sa'adou da ke zama a birnin Yamai.

“Amurkawa a Nijar suna zaune ne a Agadez. Kuma Agadez na da tazara mai yawa daga Tilleberi da Diffa inda ake gwabza fada da 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi. Don haka, ban ga wata matsala ba wajen neman su fice daga kasar,” kamar Sa’adou ya shaida wa TRT Afrika.

Sanarwar da Nijar ta fitar kan yanke huldar sojojinta da na Amurka na zuwa ne bayan da tawagar sojojin Amurka da ta diflomasiyya suka bar kasar bayan wata ziyarar kwanaki uku da suka kai ba tare da ganin shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tiani ba.

Mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka a Afirka, Molly Phee da kwamandan rundunar Amurka a Afirka, Janar Michael Langley na daga cikin tawagar.

Kakakin gwamnatin mulkin sojin Nijar Kanar Amadou Abdramane ne ya sanar da kawo karshen yarjejeniyar sojin Nijar da Amurka ta gidan talabijin din kasar.

Ya ce kasancewar jami'an Amurka a Nijar ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar, kamar yadda ya ce an sanya shi ne ba tare da izini ba a shekarar 2012.

Ya kuma kara da cewa tawagar Amurka ba ta bi ka'idojin diflomasiyya ba a ziyarar da ta kai kasar, kasancewar ba a sanar da Nijar wadanda za su zo ba da kuma ranar zuwansu da ajandarsu ba.

Mai magana da yawun gwamnatin mulkin sojin Nijar, Kanar Ahmadou Abdramen ne ya sanar da hakan ta gidan talbijin din kasar ta Nijar: Photo/Facebook/RTN

"Gwamnatin Nijar ta yi soki matakin tare da yin Allah wadai kan halin rashin da'a da kuma barazanar daukar fansa da shugaban tawagar Amurkar ya yi kan gwamnati da al'ummar Nijar," in ji Kanar Abdramane, yana mai karanta sanarwar a hukumance ta gidan talebijin din kasar.

Dangantaka tsakanin kasashen ya yi tsami ne tun bayan da gwamnatin Amurka ta bayyana karbe ikon mulki a kasar a matsayin matakin juyin mulki a watan Oktoban 2023.

Duk da wannan matakin da Nijar ta dauka, Molly Phee ta ce Amurka za ta iya ci gaba da baiwa kasar tallafin soji. Sai dai kuma Amurkan ta nuna damuwarta kan yadda Nijar ke kara kulla alaka da Rasha.

Kara nuna kyama ga kasashen yammacin duniya

Ana dai kallon wannan sabon ci gaba da aka samu a Nijar a matsayin wata alama ta nuna kyama ga kasashen yammacin duniya da ke kara ruruwa a yankin Sahel na Afirka biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasashe da dama da suka hada da Nijar da Mali da Burkina Faso.

Rundunar sojin Nijar ta fatattaki sojojin Faransa daga kasar a bara, bayan shekaru biyu da Mali ta fitar da su ita daga kasar.

Kimanin sojojin Faransa 1,500 ne suka janye aikinsu daga kasar a watan Janairu, bayan zanga-zangar tsawon wasu makonni da ƴan Nijar suka kwashe suna yi.

'Yanci

Dakatar da alakar soji da Amurka ba wai yana nufin ci gaba da nisantar kasashen yamma ba ne, amma ayyana samun 'yancin kai da iko, in ji Sa'adou.

Gwamnatin mulkin sojin kasar ta yanke huldar soji da Amurkawa a wani yunƙuri na "guje wa ɗabi'ar ra'ayin mazan jiya", in ji shi, yana mai kari da cewa ƙasar na ƙoƙarin gujewa manyan ƙasashen duniya ne da ke amfani da albarkatunta.

Tiani "ya yi ikirarin an tsara juyin mulkin ne tun da farko" kuma masu yunkurin "sun yi kokarin ta da barazana da za ta shafi Najeriya da Nijar," in ji sanarwar.

Mai sharhin ya yi imanin cewa matakin na Nijar ta dauka ba zai yi wani tasiri babba ba kan yanayin tsaro a yankin sahel inda kungiyoyi daban-daban masu dauke da makamai ke kai munanan hare-hare a 'yan shekarun nan.

"Wannan ci gaban zai karfafa kudurin kasashen Sahel na hadin gwiwa don tabbatar da cewa sun fuskanci matsalar rashin tsaro." in ji shi.

Sai dai Sa'adou ya ce dole ne gwamnatin mulkin sojin Nijar ta kara zage damtse wajen tabbatar da tsaron lafiyar 'yan kasar domin tabbatar irin goyon bayan da jama'ar suka bayar ga matakin da ta dauka na inganta 'yancin kasar.

TRT Afrika