Daga Firmain Eric Mbadinga
Kamar dai sauran iyaye mata, Jeanne tana da kyakyawan buri kan ɗanta na farko a duniya.
Ta sanya masa sunan Julien, tana da burin ganin ya girma cikin koshin lafiya da annashuwa da hankali da kuma wasa da wayon sanin abu.
Jeanne na kokarin koyar da shi abubuwa da su inganta masa kwakwalwa da zuciya don su iya taimakonshi a rayuwa.
Sai ga ƙaddarar ta zo a yanayin da ba ko wacce uwa za ta yi maraba da shi ba, Julien na fama da lalurar rashin samun rayuwa mai kyau kamar ko wanne ɗa.
Jeanne ta yi zargin cewa akwai wani abu da ɗanta ya rasa, don haka ta kai shin wurin likita.
Gano matsalar ne ya ƙara sanyaya mata gwiwa, wai a cewar likita, kyakyawan ɗanta na ɗauke da lalurar galahanga.
"Lokacin da na samu labarin cewa Julien na fama da lalurar PDD (Pervasive Developmental Disorder), na tsinci kaina cikin yanayi na baƙin ciki, ba tare da samun wanda zan yi wa magana akai ba, ga kuma karancin ilimi kan wannan lalura da ke damunsa a rayuwa," kamar yadda Jeanne ta shaida wa TRT Afrika.
''Na ƙi yarda da sakamakon cutar, balle har na iya sanin matakin da ya kamata na ɗauka, sai da ya dauke ni tsawon wasu lokuta na kokarin amincewa da wannan ƙaddarar.''
Yayin da suke ci gaba da rayuwa cikin ɗimbin ƙalubale na lalurar galahanga, ''autism'' har yanzu Jeanne da Julien wanda a yanzu shekararsa 15 suna fama da gwagwarmayar rayuwa.
A haka ne, uwa da ɗanta suka lalubo wata hanyar karfafawa kansu kana suka soma aikin taimaka wa wasu.
Kungiyar La Maison Bleue de Julien, makarantar Julien's Blue House da ke gundumar Nkoabang a Yaoundé, babban birnin kasar Kamaru, kyautar da mutane biyun suka samarwa masu fama da cutar galahanga da iyayensu.
An yi wa makarantar rajista a matsayin sadakatul jariya tun a watan Maris na 2020, kana wuri ne da aka assasa domin taimaka wa mutane masu fama da lalurar Autism hanyoyin da za su iya dogaro da kansu da kuma cuɗanya cikin mutane tare da horar da su ayyuka da suka shafi jinƙai da dabi'u ɗan'adam da haɗin kai.
A lokacin da ta yanke shawarar kafa cibiyar a shekarar 2020, Jeanne na sane da cewa akwai buƙatar ta ƙara jajircewa sosai a gwagwarmayarta kafin ta soma samun karbuwa daga farko.
"Ina yarda da lalurar da Julien ke fama da ita, sai na shaida wa kaina cewa dole na yi ƙoƙarin taimaka wa sauran iyaye, musamman ma iyaye mata, waɗanda sau tari da dama suke fama da yanayin kaɗaici da rashin ilimi kan lalurar, in ji Jeanne.
Ta kara da cewa ''ɗana da wata ƙawata ne suka mara min baya a wannan aiki da na soma."
Ba za a iya takaita tasirin da aka samu daga dukka ayyukan cibiyar ba, inda yaran da aka gano suna fama da lalurar Autism suka samu horo kan dabarun girke-girke da fasahar zamani.
Mafi muhimmaci ana koyar da su ayyukan da suka shafi zamnatakewa wadanda za su taimaka wajen ƙarfafa kwazo da fikirar waɗanda aka horar da su.
Wahalhalun lalurar
Jeanne, wadda a yanzu haka take cikin shekarunta na arba'in, tana ilimantarwa game da wahalhalun yanayin lalurar kalahanga wato ''Autism'' da aka fi sani da PDD.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana lalurar Autism a matsayin rukunin cuta da ke da alaƙa da ci gaban kwakwalwa, wanɗa ake samu ko dai ta hanyar muhalli ko kuma wasu abubuwan da ake gadonsu waɗanda ke shafar ɗabi'u da ilimi tare da dagula rayuwar masu lalurar.
Ko da an gano cutar da wuri ko a makare, waɗanda ke fama da lalurar Autism suna buƙatar taimako na musamman don fuskantar ƙalubalen da yanayin ke zuwa da shi.
A cewar ƙwararru a fannin halaiyar ɗan'adam, muhimman kalaman da ake buƙata sune na soyayya da haƙuri da kuma wasu dabarun hanyoyi.
Tun bayan kafa cibiyar La Maison Bleue de Julien a lokacin bullar cutar Covid-19, Jeanne ta gaza ɗaukar kowa in ban da ɗanta bayan an buɗe cibiyar.
Daga nan ne ita da danginta suka bude shafin Facebook inda suka fara wallafa labarin rayuwar Julien na yau da kullum don ƙarfafawa sauran iyaye da kuma taimaka musu su fahimci yadda za a iya taikaita wahalhalun da ke tafe da lalurar.
Saƙon kafofin intanet din sun yi tasiri sosai. Bayan ganin hotunan Jeanne da ɗanta, wasu iyaye da ƙwararrun masu aikin sa kai suka shiga ayyukan cibiyar da ƙungiyar.
Bayan shekaru huɗu na aiki tuƙuru, Julien ba shi kaɗai bane, a yanzu haka kungiyar La Maison Bleue de Julien ya tara dalibai 20.
Ana ba da horo kan zane-zane da girke-girke da iya maƙwalashe da kuma horo kan fasahar zamani, iyaye masu aikin sa kai da ƙwararru suna koyar da yaran masu shekaru tsakanin 5 zuwa 15.
A lokacin hutu, ƙungiyar na shirya darussa tsakanin yara da malamai da suka ƙware wajen ba da horo kan hanyoyin iya magana da kuma dabarun sanin dabi'u.
Jeanne, wadda ke taka matsayi biyu na Uwa da kuma mai ba da horo, ta yi imanin cewa haɗin kai daga iyali da tausayawa da haƙuri da kuma ƙautatawa daga ƴan'uwa da samun goyon bayan al'umma suna da matukar muhimmaci wajen inganta rayuwar mutanen da ke fama da lalurar Autism.
Hukumar WHO ta ba da shawara kan dabi'un da za su taimaka wajen inganta hanyoyin sadarwa da zamantakewa da duk za su taimaka wajen iinganta rayuwar mutanen da ke fama da lalurar Autism da masu kula da su,
Ƙalubalen Amincewa da lalurar
Duk da cewa an samu ci gaba sosai a ayyukan da kungiyar La Maison Bleue de Julien ta sa a gaba, Jeanne ta ce akwai buƙatar a ƙara kaimi kan wasu fannoni da dama don haɓaka dabi'un tallafawa mutanen da ke fama da lalurar galahanga.
"A bangaren iyaye, kyawawan dabi'u suna somawa ne daga wurinsu ,idan har suka amince da lalurar kana suka dauki nauyin kula da ɗansu da ke fama da cutar.'' in ji Jeanne
Ta kara da cewa ''Akwai buƙatar iyaye su taka rawa a karatun ƴa'yansu da ayyukansu da kuma yanayin wassaninsu, tare da taimakon ƙwararru da ware lokaci na musamman ga masu fama irin wannan lalura,'' kamar yadda ta shaida wa TRT Afirka.
Kazalika Jeanne ta jaddada cewa babu wata nasara karama sannan babu wata ci gaba da ya yi kaɗan.
Ƙusan Jeanne ce ke ɗaukar nauyin ƙungiyar La Maison Bleue de Julien tare da wasu rukunin iyayen ƙadan wadanda suka miƙa mata yardarsu.
Kamar yadda yake a sauran ƙasashen Afirka, Kamaru tana da cibiyoyi ƴan kalilan na musamman ga masu fama da lalurar Autism.
Kasar Maroko, wacce kundin tsarin mulkinta ya ba da damar samun ilimi ga kowa, a hukumance ta haramta duk wani wariya game da masu fama lalura ta musamman.
Masu bincike sun ba da shawarar samar da yanayi mai kyau na koyo ga yara masu fama da lalurar kalahanga don inganta rayuwarsu.
Ga Jeanne, ganin walwalar fuskar ɗanta Julien a kowane ɗan ƙaramin ci gaba da ya ya ke samu shine mafi nutsuwa da farin cikin rayuwarta.