Daga Emmanuel Onyango
Mutuwar a kalla yara kanana 23 a Johannesburg a wata da ya gabata sakamakon cin abincin da ake zargin na dauke da guba ya janyo mayar da martani da ya sanya gwamnatin Afirka ta Kudu a makon nan ayyana cututtukan da abinci ke janyo wa "annobar kasa".
A tsakankani, ra'ayin mutane ya karkata ga rawar da kantinan cikin unguwanni ke taka wa - da ake kira shagunan spaza - wajen mutuwar da ke da alaka da gurbatattun abinci. an fi samun irin wadannan kantina da yawa a birane, da ke kasnacewa a dukkan unguwanni, kuma an fi zuwa shagunan sayayya saboda kusancinsu da gidaje, kusan koyaushe a bude suke sannan suna sayar da kaya daya-daya.
"Shagunan spaza na da dadin mu'amala a unguwanni, inda da tsakar dare ma za ka gan su a bude. Jama'a na da kakkarfar alaka da wadannan shagunan, ko da sukari gwangwani daya ne za su saya ko kwai kwaya daya," Rosheda Muller, shugabar Gamayyar Kungiyar Kananan 'Yan Tireda a Afirka ta shai da wa TRT Afrika.
Gwamnati na dora alhaki kan shagunan saboda yadda ba s aiya kula da kayan kwalam da makulashe da aka bayyana na janyo mutuwar da yawa/
Sakamakon fuskantar matsin lambar ya dauki mataki, Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a wannan watan ya sanar da daukan tsauraran matakai, ciki har da yin rejista ga dukkan shaguna da sauran wuraren da sayar da kayan abinci nan da kwanaki 21 a garuruwan da suke ayyuka. Ya kuma ce dole ne sai sun cika sharuddan kula da lafiya ko kuma a kulle su.
Hukumar kididdiga ta gwamnatin Afirka ta kudu ta bayyana cewa kantinan na da yawa kuma suna taimaka wa mutane miliyan uku da ayyukan yi.
Sai dai kuma, kwararrun kiwon lafiya na cewa matsalar ta fi karfin yadda gwamnatin ta dauke ta, bayan gargadi kan kula da magungunan kwari a fadin kasar da ingancin kayan abinci da yadda ake rarraba su.
Har yanzu akwai tambayoyi da ba a amsa ba game da alakanta mutuwar yara kanana da guba a cikin abinci, in ji Angelique Coetzee, shugabar KUngiyar Likitoci ta Afirka ta Kudu yayin tattauna wa da TRT Afrika.
"Idan har mace-macen na da alaka da shagunan spaza, me ya sa wasu yara kanana da ke tsakanin wasu shekaru ne ke mutuwa amma ban da manya? Dr Coetzee ta fada tana mai mamaki.
Wani bincike da aka gudanar a Afirka ta Kudu a 2023 ya gano cewa sama da kashi 50 na mutuwar yara a cikin shekaru 10 na da alaka da magungunan kwari da ake fesa wa; binciken ya alakanta mace-macen da magungunan masu karfi da ake sayarwa a kan tituna don amfani a gidaje.
Ta tambayi cewa "Gwamnati, ciki har da Sashen Kula da Lafiya na Kasa da larduna da yawa, na bukatar bayyana gaskiya da fada mana takamaiman meye muke gwagwarmaya da shi. Shin duk sun gan duk dalilan ko duk sun mayar da hankali ga shagunan spaza?"
Shagunan spaza sun zama babban batu. Mutuwar wasu yara a watan da ya gabata a Naledi, Soweto bayan sun sayi kayan kwalam da makulashe a wani kantin spaza- ya janyo hayaniya, inda jama'ar yankin suka kai hari kan shagon tare da sace kayan cikin sa wanda mallakin wani dan kasar waje ne.
A yayin da aka samu gurbatar kayan abinci a lokuta da dama a watanni ukun da suka gabata, ana ganin gwamnati ta makara a kokarinta na sanya dokoki kan kantina kanana.
Ka'idojin da ake bukata don yin rejista sun tanadi cewa dole ne mai kanti ya zama dan kasar Afirka ta Kudu kuma dole ne ya yi rejistar kasuwancin nasa da gwamnatin karamar hukuma.
Sai dai kuma, akwai damuwa kan ko mutanen za su iya yin rejista kafin wa'adin lokacin da aka tanada.
"Shagunan spaza ne zuciyar unguwanni, amma dole ne asaka musu dokoki - kuma a samar da tsarin gudanar da kasuwancin su. Amma ba zai yiwu a yi hakan a cikin kwanaki 21 ba. A matsayinmu na masu gwagwarmayar kasa, mun rubuta wasika ga shugaban kasa don neman karin lokaci, saboda ana daukar lokaci mai tsayin kafin rejista," in ji Muller.
Ta kara da cewa "ya zama dole su ba mu wa'adin shekara guda, saboda kananan hukumomi ba su da ikon yin rejistar kasuwanci a hukumance. Akwai miliyoyin 'yan tireda da ba su da rejista a Afirka ta Kudu, kuma da yawan su suna aiki a shagunan spaza kuma msuna sayar da kayan ciye-ciye."
Kwararrun kula da lafiya sun ce ka'idojin da aka ce za a kawo na iya zama marasa tasiri da gaza magance matsalar da ta addabi jama'a.
"A yanzu haka, an mayar da hankali kan shagunan spaza ne kawai, amma ina tunanin lamarin ya fi karfin batun shagunan spaza. Ina jami'an tabbatar da tsafta suke a shekarun da suka gabata? Shin sun yi aikinsu? Dukkan lamarin na bukatar a kalle shi," in ji Dr Coetzee.