Ramaphosa Davos

Daga Charles Mgbolu

Idan ka kalle shi a karon farko, garin Davos na hutawa ne da ake wasan dusar ƙanƙara da daɗin ɗaukar hoto, wanda yake a tsaunin Graubunden na Switherland, wurin da ya zama kamar ba wajen gudanar da kasuwanci ba.

Amma ba hakan ne ya sanya Davos ke fitowa a shafukan farko na jaridu a kowace shekara ba. Tun 1971, wajen gudanar da Babban Taron Tattalin Arziki na Duniya ya zama cibiyar tattaunawa kan batutuwa da fannonin duniya, manufofin masana'antu da yankuna.

Taron WEF na 2025 mai taken "Haɗin-Kai Don Zamani Mai Basira", na karɓar baƙuncin shugabannin tattalin arziki da siyasa na duniya, ciki har da mutane na musamman daga Afirka.

Taron da ake gudanarwa a tsakanin 20 da 24 ga Janairu na da mahalarta kusan 3,000, ciki har da shugabannin gwamnati 350 da jagorori 60 daga ƙasashe kusan 130.

Waɗanda ke wakiltar Afirka a wajen taron sun haɗa da Shugaban Ƙasar Afirka ta Kudu; Cyril Ramaphosa, takwaransa na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Felix Tshisekedi, da Shugaban Ƙasar Somalia, Sheikh Mohamud.

Shugaba Hassan Sheikh Mohamud na Somalia ya bayyana cigaban da ƙasarsa ta samu a ɓangarori da dama. Hoto: Villa Somalia

Masar ta samu wakilcin Firaminista Mostafa Madbouli, haka ma Nijeriya ta samu wakilcin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima.

Tambayoyi game da muhimman buƙatu

Ɗaya daga cikin tantamar da ake da ita game da taron na Davos na bana shi ne wane alfanu yake da shi ga tattalin arzikin ƙasashe, musamman ma na Afirka?

Babbar tambayar da aka fi ji game da taron ita ce; Ko tattaunawar da ake yi a wajen Taron na Davos na taɓo batutuwan da suka shafi halin da tattalin arzikin ƙasashen Afirka da wasu wuraren ke ciki?

A yayin da tattaunawa a bana ta mayar da hankali ga tasirin ƙirƙirarriyar basira, wani tunani shi ne yadda batun ba lallai ya zama damuwar gaggawa ga ƙasashen Afirka ba.

Waɗannan masu nazari na cewa dole ne shugabannin Afirka su faɗaɗa tunaninsu a wajen taron na manyan mutane kuma kada su zama "masu asara".

"Davos na da amfani ne kawai a lokacin da shugabannin Afirka za su samu labarin za a yi mu'amala da su sosai da kuma ɗora Afirka a turbar haɓakar tattalin arziki," in ji wani ƙwararre a fannin tattalin arziki da kasuwanci a Nijeriya, Jide Pratt, a hirarsa da TRT Afrika.

"Idan, a matsayin shugaban Afirka, zan iya ƙulla yarjejeniya a Davos saboda ɗaiɗaikun mutanen da ke son tattaunawa da su za su je wajen, to amfanin babban taron na da yawa."

Pratt ya jaddada babbar buƙatar shugabannin Afirka kan su haɗa kawunansu wajen cim ma muradun nahiyar a fagen ƙasa da ƙasa.

"Dole ne su koyi shirya kansu da haɗa shiri da buƙatunsu waje guda. Misali, tunanin me ya sa ma aka kafa ƙungiyar G12. Kallon yadda ƙasashe suke haɗewa waje guda tare da neman biyan buƙatunsu a haɗe." in ji shi.

Wannan son-kai ne ke sanya wa ake kiran da a samu babban haɗin-kan ƙasashen Afirka a tarurrukan ƙasa da ƙasa.

Aiki yadda ya kamata

Duk da wadannan kiraye-kiraye da ake ta maimaitawa, sakon na bata a yayin fassara da isar da shi. Pratt ya yi gargadin cewa WEF na wannan shekarar ba zai yi wani amfani sosai ga kasashen Afirka ba matukar kasashen za su dinga neman biyan bukatunsa daya-daya.

Ramaphosa na Afirka ta Kudu, misali, ya ce zai yi amfani da wannan dama wajen tura bukatar kasarsa ta shugabancin G20, da kuma batun sarrafa ma'adanai a cikin kasarsa maimakon fita da su kasashen waje.

"A matsayin mambobin G20, muna bukatar kokarin bai daya na mayar da hankali kan habaka duba da irin karbin arziki, kasuwanci, zuba jari da talaucin kasashe tare da tabatar da adalci wajen samun damarmaki musamman ga mata da matasa."

A nasa bangaren, Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya gayyaci masu zuba jari da su "amfana da damar da Nijeriya ke da ita wajen zuba jari don ribata da kasar da ma Afirka baki daya".

Pratt ya sake jaddada cewa manufofin daidaikun kasashe na raunata manufofin kowacce nahiya.

"Batu ne na niyya. A matsayin shugaban Afirka, zan je wajen taron da zuciya mai karfi. Mene ne karfin a cikin zuciya? Ina son na ga cigaban nahiyar da habakar masana'antu. Zan tabbatar cewa aikin cimma wadannan manufofi ya fara kafin kammala taron." in ji shi.

Shugaba Ramaphosa, a jawabinsa a Davos, ya tabo muhimmancin hadin kan kasashen duniya a matsayin "gadar wayewar dan adam da cigaba".

Sai dai kuma, gaba mai muhimmanci da masu nazari suna bayyana ita ce; Ba tare da hadin kan cikin gida da zama waje daya tsakanin shugabannin Afirka ba, inda za su fitar da manufofin bai daya don baje su a wurare irin su Davos, to tarukan za su zama kamar na "shan shayi kawai".

TRT Afrika