ECOWAS ta kakaba wa Mali da Burkina Faso da Nijar takunkumi bayan da sojoji suka hambarar da zababbun gwamnatocin farar hula a kasashen: Hoto/ Others

Daga Abdulwasiu Hassan

Wani hasashe da aka yi game da kungiyar ECOWAS mai wakilan kasashe yankin yammacin Afirka 15 na rasa ikonta a kan wasu mambobinta uku sakamakon rudanin da suka fada ya tabbata.

A ranar 28 ga watan Janairu ne gwamnatocin mulkin soji na Mali da Burkina Faso da kuma Nijar suka sanar da ficewar kasashensu daga kungiyar ECOWAS na yankin.

Kyaftin Ibrahim Traoré na Burkina Faso da Kanar Assimi Goita na Mali da kuma Janar Abdourahamane Tiani na Nijar, wadanda dukkansu uku suka kwace mulki daga hannun gwamnatocin farar hula ta hanyar juyin mulki, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka zargi kungiyar ECOWAS da nuna rashin adalci ga kasashensu.

A martanin da ta mayar cikin gaggawa, ECOWAS ta ce ba ta samu wata sanarwa a hukumance daga kasashen ba game da ficewarsu daga kungiyar.

Kazalika, ta jaddada cewa kasar Burkina Faso da Mali da kuma Nijar na ci gaba da zama wani bangare na kungiyar, kuma ana aiki tare domin kawo karshen wannan matsalar da ta kunno kai.

Kungiyar ECOWAS wadda ta kakaba wa kasashen takunkumi bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatocin da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya, ta ce tana aiki tare da sabbin gwamnatocin domin mayar da tsarin mulkin kasashen.

Ra'ayoyi game da hanyoyin warware matsalar sun bambanta kamar yadda ake da mabambantar ra'ayoyi game da abubuwan da suke faruwa a yanzu.

Tasirin abubuwan da suka faru

Abin da akasarin mutane suka fi la'akari a kai shi ne ficewar Mali da Burkina Faso da Nijar daga kungiyar ECOWAS na da matukar tasiri ga yankin musamman Nijeriya.

"A matsayinta na kungiyar yankin, ECOWAS na bukatar ta samar da hadin kai tare da bunkasa tattalin arzikin yankin, a yayin da wadannan kasashe uku su ka fice, kungiyar za ta rabe tare da gurguncewa," kamar yadda Farfesa Kamilu Fagge na sashen nazarin kimiyyar siyasa a Jami'ar Bayero da ke jihar Kano a Najeriya ya shaida wa TRT Afrika.

Akwai rarrabuwar kawuna tsakanin Jama'ar yankin game da batun ballewa daga kungiyar:/ Hoto: Reuters

"Mafi muni kuma, idan ba a magance rikicin da kyau ba, lamarin zai iya tura wadannan kasashe zuwa Rasha, ta yadda za a farfado da yakin cacar baka a yankin."

Farfesa Fagge ya kara da cewa ficewar kasashen uku za ta takaita kasashe kamar Nijeriya yaki da laifukan da suka shafi kan iyaka da safarar makamai ba tare da hadin kan makwabciyarta ta yankin arewa wato Nijar ba.

"Baya ga haka, ficewar kasashen zai gurgunta dangantakar zamantakewa da tattalin arziki, Muna da kusanci ta fuskar al'adu da zamantakewa da makwabtanmu, kuma idan babu hakan ba za mu iya cimma komai ba, kamar yadda masu iya magana kan ce samun tsaron ku yana tattare da makwabcin ku,'' inji shi.

Har yanzu kasar Nijeriya da Benin da Cape Verde da Cote d'Ivoire da Gambia da Ghana da Guinea da Guinea-Bissau da Liberiya da Senegal da Saliyo da kuma Togo mambobin kungiyar ECOWAS ne.

Tsarin ficewa

Sashi na 91 na Yarjejeniyar ECOWAS da aka sabunta ya bukaci duk wata kasa da ke son ficewa daga kungiyar ta ba da sanarwa shekara daya kafin lokacin.

Ayyukan tsaro na hadin gwiwa na daga cikin batun farko da suka janyo ficewar kasashen daga ECOWAS: Hoto/Reuters

Sashen dokar ya ce kasar da ta dauki wannan mataki za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar tun daga lokacin da ta ba da sanarwar har zuwa shekarar gaba, bayan cika wannan sharruda kasar za ta iya ficewa daga kungiyar idan har ba ta canja ra'ayi ba.

“Kowa zai iya yanke shawarar tafiya. Amma idan suka take sharruda, kamar sashi na 21, me zai faru da su? Babu komai,” a cewar Farfesa Fagge.

Idan aka yi la’akari da yadda wasu shugabannin yankin Afirka ta Yamma ke yin watsi da hukuncin kotun ECOWAS, zai yi matukar wahala a iya bi ko aiwatar da wata doka a yanzu.

''Kasashe da dama ciki har da Nijeriya a lokuta daban-daban sun sha bijirewa ka'idoji da dokokin kungiyar ECOWAS, kuma ba zai yiwu ka take doka ka sa ran wasu za su bi ba.'' in ji Farfesa Fagge.

Takaita damammaki

Yarjejeniyar tsarin dokar ECOWAS ta bai wa 'yan Afirka ta Yamma damar shiga da fita yankin ta hanyar samun biza idan sun isa. Masana dai na ganin wannan na daya daga cikin tasirin ficewar kasashe uku mambobin kungiyar suka janyo.

A gefe guda kuma manazarta na ganin matakin ficewa daga ECOWAS a matsayin wata dama ga kasashen yamma su iya kutsa kai yankin cikin sauki.

"A halin yanzu kasashen ukun da suka dauki wannan mataki za su fi jin jiki domin yankunansu baki daya a kasa yake, babban tushen kasuwanci da dangantakarsu sun ta'allaka ne kan kasashe da ke makwabtaka da su, kuma yanke alaka da su zai haifar da wahala." A cewar Farfesa Fagge wa TRT Afirka.

A daya bangaren kuma, kasa kamar Nijeriya, wadda ayyukan samar da wutar lantarkinta ya dogara kan ruwan da ke ratsawa ta makwabciyarta Nijar, za ta ji radadin wannan ficewa idan har kasar ta datse kogin.''

Farfesa Issoufu Yahaya na Jami’ar Abdou Moumouni da ke Yamai ya dora alhakin rikicin da ake fama da shi a yanzu kan kungiyar ECOWAS, yana cewa kungiyar ta zama ta siyasa, duk da cewa an kafa ta ne domin kare tattalin arzikin kasashe mambobinta.

"Akwai yiwuwar wasu shugabannin ECOWAS na kara kaimin muradun kasashen Yamma," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

“Ya kamata shugabancin ya kasance yana dauke da diflomasiyya wajen warware batutuwa, amma babu tsarin diflomasiyya a cikin kungiyar a yanzu, ba mu da wata yarjejeniyar dokar ECOWAS da ke goyon bayan duk wani takunkumi, hakan na nufin abin da kungiyar ta yi (wajen sanya takunkumi kan mambobin kungiyar) ya sabawa doka. ."

Ballewa daga kungiyar yankin ECOWAS zai haifar da mummunan tasiri kan kasuwanci: Hoto/Reuter

Mataki na gaba

Kungiyar ECOWAS dai ta ce ta kakaba wa kasashen uku takunkumi ne domin kare ‘yancin zaben al'umma. A dayan bangaren kuma, gwamnatin sojojin da ke neman ballewa daga kungiyar sun kafa hujjar cewa sun dauki matakin ne don al'ummarsu.

Wasu na ganin ya kamata kungiyar ECOWAS ta shiga tattaunawar diflomasiyya da kasashen da suka balle, wasu kuma na ba da shawarar a bi hankali har sai wutar rikicin ya lafa.

Farfesa Fagge ya ce kowanne bangare biyu na da ra'ayinsa - su daidaita bambance-bambancen da ke tsakanin su tare da neman mafita ga matsolin da suka shafi Afirka za ta magance matsalar Afirka don amfanin 'yan kasarsu.

Farfesa Yahaya ya ba da shawarar barin ECOWAS, yana mai cewa ba gudu ba ja da baya kan abin da ya riga ya faru. "Ina ganin abin da ya fi dacewa shi ne kowa ya bi hanyarsa domin babu wata alama da ta nuna cewa kungiyar ba ta da wata makoma ga yankin."

To sai dai ga al'ummar yammacin Afirka da ke sa rai wajen ganin ranar da yankin zai koma wata kasuwa mai dauke da jama'a da kayayyaki da ayyuka da za su iya fita da shiga ko ina a yankin cikin sauki, ficewar kasashen uku daga kungiyar ECOWAS wani koma baya ne da zai matukar shafarsu.

TRT Afrika