Donald Trump / Hoto: Getty Images

Daga Sylvia Chebet

Taken 'MAGA' da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya tashi daga matsayin taken yakin neman zabe d aya ja hankalin Amurkawa masu jefa kuri'a, zuwa matsayin jagorar shugabantar kasar mafi karfin tattalin arziki, wanda daya daga manyan magoya bayansa Elon Musk ya kira "alade a kan hanya".

Tafiyar Trump zuwa ga bayar da kariya ga Amurka tare da daukar zafafan matakai, ciki har da matakin zartarwa na dakatar da tallafi ga kasashen waje na kwanaki 90, an samu mayar da martani sosai ga wannan sauyi na manufa da tunanin me zai je ya komo a duniya.

Sai dai kuma, ba kowa ne ke bayyana damuwa da sukar sabon tsarin sauya gudanarwar Amurka kan manufofin kasashen waje da tattalin arziki ba.

Tsohon Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bukaci Afirka da ta kalli matakin na Trump a matsayin "kiran a farka", yana mai bayyana yiwuwar matakin na kariya ga Amurka da Trump ke yi zai bar nahiyar cikin zaman ɗar-ɗar.

"Na ga wasu mutane na kuka, 'Wayyo! ban sani ba... Trump ya ce ba zai sake ba mu wasu kudade ba.' Me ya sa kuke kuka? ba gwamnatinku ba ce.

"Ba kasarku ba ce," in ji Kenyatta a wajen Taron Kula da Lafiya na Gabashin Afirka da aka gudanar a Mombasa a ranar 28 ga Janairu.

"Trump ba shi da wani dalili na ba ku komai. Ina nufin, ba kwa biyan haraji ga Amurka....Wannan kiran a farka ne gare ku, 'To, me za mu yi don taimakawa kawunanmu? Ba shi da dalilin ba ku komai...yana tausaya wa jama'arsa ne; hakan ba shi da kyau gare ku."

Tsarin dogaro da kai

Afirka na da dimbin albarkatun kasa da za a iya amfani da su don samun dogaro da kai da rage dogaro kan taimakon kasashen waje.

A 2019 wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya a intanet na https://www.unep.org/regions/africa/our-work-africa ya bayyana cewa Afirka waje ne da ke dauke da kusan kashi 30 na albarkatun kasar da ake da su a duniya, kashi 12 na albarkatun mai da kashi 8 na alarkatun iskar gas.

Haka zalika nahiyar na dauke da kimanin kashi 40 na zinaren da ake da shi a duniya, da kusan kashi 90 na albarkatun 'chromium da platinum'.

Rahoton ya ambaci man fetur da gawayi a matsayin albarkatun kasar da suka yawa a kasashe 22 daga cikin 54 da ke Afirka.

A 2019, Nijeriya ta samar da kashei 25 na man da aka fitar daga nahiyar, sai Angola da ta fitar da kashi 17, inda Aljeriya kuma ta fitar da kashi 16.

Bangaren noma kuma, wanda ke samar da ayyukan yi ga jama'a da dama, na da makoma mai muhimmanci.

Tuntuni kwararru ke cewa shugabanci mai dorea da ciro albarkatun kasar Afirka na iya tiamakawa kasashen Afirka samun kudaden shiga, samar da ayyukan yi, da habaka tattalin arziki.

Dabarun amfana da kudaden cikin gida na iya tallafawa wadannan manufofi na samar da cigaba da kuma taimaka wa kasashe magance kangin basussuka da rashin cigaba.

Bankin Duniya ya ce Yarjejeniyar kasuwanci Mara Tsaiko ta AfCFTA na gabatar da damarmaki masu muhimmanci ga kasashen nahiyar "su fitar da mutum miliyan 30 daga tsananin talauci a kuma kara yawan kudaden da mutum miliyan 68 ke samu wadanda suke rayuwa da kasa da dala 5.5 kowacce rana".

Tare da aiwatar da Yarjejeniyar AfCFTA, matakan saukaka kasuwanci da suke saukaka fito za su samar da dala biliyan 292 daga cikin dala biliyan 450 da ake sa ran za a samu.

'Kyakkyawan kula da harajin daloli'

To, me wannan ra'ayin rikau na Trump game da bayar da kudade ke nufi har zuwa lokacin da Afirka da sauran duniya za su koti rayuwa ba tare da kudaden ba?

A taron 'yan jarida na farko, sakatariyar hulda da 'yan jaridu ta Fadar White House, karoline Leavitt ta ce shirin Trump na dakatar da bayar da taimakon kudaden na d amanufar "kyautata amfani da dalolin kasar".

Matakin zai dakatar da kashe biliyoyin daloli na taimakon kubutar da rayuka a duniya.

A 2023, Amurka ta zama kasa mafi girma a duniya da ke bayar da taimako a duniya, inda ta bayar da tallafin dala biliyan 72.

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a baya-bayan nan ya kira ga "A samu karin togaciya don tabbatar da ci gaba da bayar da taimako ga masu rauni da ke bukatar tallafin jinkai a duniya".

"Rayuka da rayuwar wasu jama'a sun dogara ne kan wannan taimako", in ji Stephen Dujarric, mai magana da yawun Guterres.

Sai dai kuma, tsohon Shugaban Kasar Kenya, Kenyatta na da ra'ayin cewa Trump na da gaskiya wajen daukar matakin kare muradun Amurka.

"Babu wanda zai ci gaba da bude hannu a can yana ta ba ku. Lokaci ya yi da za mu yi amfani da albarkatu da arzikinmu don yin abubuwan da suka kamata," in ji Kenyatta.

Kalubalen shari'a

Wasu daga matakan zartarwa da Trump ya dauka sun fada rikita-rikitar shari'a. Wani alkali a Amurka ya dakatar da matakin tallafin kudade ga ayyukan tarayya da dama, mintuna kadan kafin matakin ya fara aiki.

Sai dai kuma, mahukunta a sabuwar gwamnatin na cewa dakatar da bayar da tallafin ya zama wajibi don trump ya tabbatar da tallafin ya yi daidai da bukatun Amurka.

Kwararru sun lura da cewa Trump na daukar matakai irin wadanda ya dauka a lokacin mulkinsa na farko - sai dai cewa a yanzu yana da damar kwarewa sannan yana kewaye da mutanen da suka dade suna shiri do ya dawo Fadar White House.

Babu mamaki, aboda haka, cewa Trump na amfani da karfin ikon shugaban kasa.

"Mutumin ya dawo," in ji David Monyae, mataimakin farfesa a Jami'ar Johannesburg yayin tattaunawa a TRT Afrika.

"Wannan na bukatar duniya ta zama mai sanya idanu kan muhimman bangarori."

Mai jin ra'ayin jama'a dan jam'iyyar Republican, Whit Ayres ya gamsu da cewa "wannan gwamnatin ta Trump ta fi zama mai zafi sama da wadda ya jagoranta a wa'adin farko."

Dan kishin Afirka Momodou Taal, wanda ya rubuta 'The Malcolm Effect Revisited', ya ce ya wajaba shugabannin Afirka su fara dabbaka manufofi irin na "Afirka Kawai", yana mai bayar da karin haske kan inda Amurka ta dosa.

"Shugabannin Afirka za su iya koyo daga wannan. Wadannan manufofi na bayar da kariya da muke gani a tarihi na da alaka ta kai tsaye ga cigaba," Taal ya fada wa TRT Afrika.

"Za ku fahimci cewa jari hujjar kowa ya yi kasuwnacinsa ba tsaiko ba zai samu nasara ba ba tare da tsoma hannun kasashe ba.

"Saboda haka, ana bukatar manufofin bayar da kariya ga kasa don ciyar da nahiyar gaba."

TRT Afrika