Jayayyar da ake yi dangane da abin da ya kamata a rinƙa tunawa dangane da tarihi ya ta'allaka ne sosai dangane da yadda za a koyar da shi kansa tarihin. . / Hoto: UNESCO

Daga Dayo Yussuf

Shi tarihi yana da wata hanya ta musamman na yin daidai da abubuwan da ke faruwa a yanzu, inda a wani lokacin yana sanyaya zukata.

Wannan tsohon tabon na ɗauke da alheri, duk da cewa bai warke ba amma duk da haka yana ƙarin haske domin fahimtar abin da ya faru a baya, da yanzu da kuma wanda zai faru a gaba.

Ƙasashen duniya da dama waɗanda suka gudanar da mulkin mallaka a baya a halin yanzu na ta ƙoƙarin shafe tarihi, ko dai ta hanyar rage wa lamarin ƙarfi ko kuma sake fasalta irin muguntar da suka yi a lokacin mulkin mallaka da cinikin bayi inda a halin yanzu suke son bayar da labarin ta yadda zai wanke su.

Sai dai sama da shekara ɗari biyu tun bayan da aka haramta cinikin bayi a faɗin duniya, aƙalla a kan takarda, irin raɗaɗi da jin zafi ta zaluncin da waɗanda suka rinƙa sayen bayin suka rinƙa yi kan bayin har yanzu na nan a cikin zukata.

A halin yanzu wane irin abu ne na ban tsoro game da cinikin bayi wanda ba za a iya mantawa da shi ba, ko kuma ma a cire shi daga littattafan tarihi ta hanyar wanke kansu a halin yanzu?

Masana tarihi na ƙoƙarin kallon wannan lamarin daga ɓangaren waɗanda suka haddasa da waɗanda suka wahala da kuma jama'ar da halin yanzu suke fama da matsalar da ta samo asali tun daga kakanninsu.

"Ra'ayi game da cinikin bayi na ɗaukar salo ya kuma danganta da waɗanda suka yi shi, da gwamnatocin da masu cinikin bayin ke wakilta, da masu saye da waɗanda ke amfana," in ji David Kyule, wanda ke koyar da tarihi da ilimin kimiyya na kayayyakin tarihi a Jami'ar Nairobi da ke Kenya a tattaunawarsa da TRT Afrika.

"Idan kuka yi tambaya game da haka a Birtaniya, Brazil da Amurka, sai yanayi ya sauya na jin daɗi da tausayi da sauransu."

A lokacin da aka yi cinikin bayi na Atlantika, daga 1526 zuwa 1867, an sayar da bayi kusan miliyan 12.5 maza da mata da yara a Amurka. / Hoto: Getty Images

Goyon bayan haramta cinikin bayi

Ana ta samun bambancin ra'ayi dangane da ranar 23 ga Agusta wadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin tunawa da cinikin bayi da haramta shi, a matsayin ranar tunawa da irin muggan laifukan da aka yi a baya ko kuma yadda aka lulluɓe cinikin bayin wanda ake yinsa da wani suna.

Kamar yadda Hukumar Kula da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO, ta ce a irin wannan ranar a shekarar 1791, an soma wata tarzoma a Jamhuriyar Haiti wadda ita ce ta taka muhimmiyar rawa dangane da cinikin bayi.

Tun daga farkon ƙarnin, ƙasashe kamar su Birtaniya sun soma fitar da dokoki domin haramta cinikin bayin.

"Wannan ranar ta ƙasa da ƙasa an ware ta ne domin tuna wa duniya bala'in cinikin bayi a cikin ƙwaƙwalen dukkan al'ummomi….akwai buƙatar samun damar yin la'akari game da abin da ya jawo haka a tarihi, hanyoyi da kuma sakamakon wannan bala'in," in ji wani bangare na sanarwar daraktan UNESCO a shafinta na intanet.

Kyule na kallon tunawa da batun cinikin bayi a matsayin fama da wani babban lamari da ke tafe da wani raɗadi da ake ji, musamman idan ana batun Afirka.

"Idan ana batun tunawa da cinikin bayi, akwai buƙatar ku tambayi kanku, me kuke so ku tuna, kuma iya wane lokaci za ku iya tunawa?" in ji shi.

"An yi maganar cinikin bayi a cikin littattafan addini, sai dai hakan ya sha bamban da irin wanda Faransawa da Birtaniya da Sifaniyawa suka yi.

Kowa na da labarinsa

Jayayyar da ake yi dangane da abin da ya kamata a rinƙa tunawa dangane da tarihi ya ta'allaka ne sosai dangane da yadda za a koyar da shi kansa tarihin.

Ranar 23 ga watan Agusta ce ranar tunawa da cinikin bayi da haramta shi. / Hoto: UNESCO

Ana yawan kokawa dangane da ƙin "bayyana wasu abubuwa" da kuma "juya gaskiya" da ƙasashen Yamma ke yi a littattafansu na tarihinsu domin guje wa jin kunya ko kuma kama su da laifin aikata cinikin bayi.

"Waɗanda suka rinƙa cinikin bayin suna da labarinsu, haka su ma waɗanda aka bautar da su na da nasu labarin. Waɗanda ke da hannu kamar su Cocin Katolika sun taka muhimmiyar rawa wurin cinikin bayi a Congo, suna da abin da za su ce game da hakan. Da dama suna sauya tarihi domin cimma wata manufa tasu ko kuma ta gwamnati," in ji Kyule.

Irin nauyin da ya rataya a kan masu kallon tarihin cinikin bayi a yadda ya kamata ta'allaƙa ne da waɗanda aka bautar da kuma ƙasashe da jama'ar da suka aikata hakan.

"Ba wai batun sauya labarin bane; batu ne na sauya ainahin yadda lamarin yake. Domin samun yadda abubuwa suke a zahiri game da cinikin bayi, akwai buƙatar mu yi la'akari da irin rawar da hakan ta taka a wasu ƙasashen da suka ci gaba," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"Akwai buƙatar mu yi magana kan bankuna irin su Barclays waɗanda kai tsaye aka kafa su ta hanyar cinikin bayi. Akwai buƙatar mu yi magana a kan ƙasashen da suka yi cinikin bayai da tattalin arziƙinsu."

Ana ci gaba da cinikin bayi

Wata fahimta da ake da ita ita ce an sauya fasalin cinikin bayi sannan an sayar da shi ga ƙasashen duniya, inda yake a ɓoye.

An shafe shekaru shekaru masu yawa ana cinikin bayi a duniya kafin aka daina. / Hoto: Getty Images

"An shaida mana cewa mun samu 'yanci, amma shi mun same shi?" kamar yadda Kyule ya bayyana.

"Cinikin bayin ba daina shi aka yi ba. Waɗanda suke yinsa sun yi saurin gano cewa a matsayinsa na kasuwanci, ba zai ɗore ba, wanda hakan ke nufin akwai buƙatar sauya salo."

Kamar yadda wasu masana suka bayyana, kamar yadda aka sauya wa mulkin mallaka fasali da kuma miƙa shi ga 'yan korensu waɗanda suke son yi wa iyayen gidansu biyayya ta hanyar amfai da ƙasashensu, har yanzu kuwa akwai mulkin cinikin bayin ta ƙarƙashin ƙasa.

Yadda suke yin aikin su, ya zo daidai da yadda masu mulkin mallaka suke. Turawan Birtaniya da na Faransa sun bar tsarin karatu wanda za a ci gaba da koyarwa da matasa 'yan Afirka, da tsarin gwamnati da addini. Ta hanyar yin haka, sai suka ci gaba da dawwamar da zaluncin da suke yi a ɓoye.

"Ban ga bambanci tsakanin mulkin mallaka da sauya fasalin cinikin bayi ba," kamar yadda Kyule ya shaida wa TRT Afrika. "Safarar bil'adama ita ma wata kalma ce da ake amfani da ita wurin 'cinikin bayi'. Har yanzu ana tursasa wa wasu yin ayyuka a wurare da dama, daga ciki har da gidajen da ake mayar da 'yan aiki tamkar wasu bayi."

Ci gaba da fitar da ma'aikata zuwa ƙasashe domin gudanar da aikatau inda a lokuta da dama ake samun labaran cin zarafi, da take haƙƙin ma'aikata da ƙwace fasfo ɗinsu da hana su biyan haƙƙoƙinsu da hana su hutunsu da kuma umartarsu kan yadda za su gudanar hutunsu duka hanyoyi ne da ke nuna cewa har yanzu akwai bauta.

TRT Afrika