Daga Emmanuel Onyango
Tsagaita wuta da dakatar da harbe-harbe a kan titunan Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ya sa rayuwa ta fara komawa daidai bayan da a baya 'yan tawaye suka yi ta samun iko da birnin.
Sai dai bayan samun wannan ɗan sukunin, har yanzu akwai fararen hula da ke cikin wahalar da rikicin ya jawo musu.
Babu ruwa da wutar lantarki, kuma an toshe duk hanyoyin da ke iya kai mutum cikin birnin, a cewar jami'an Congo.
Gadajen asibitoci sun cika da marasa lafiyar da suka ji raunuka sakamakon harbin bindiga. Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasta cewa kusan mutum 3,000 aka kashe sannan kusan 3,000 sun jikkata a cikin mako biyu da suka wuce. Akwai yiwuwar adadin ya ƙaru nan kusa.
MDD ta ce akwai ƙarancin kayayyakin asibiti, da man fetur da ma'aikata a matsayin babban ƙalubalen magancen matsalar.
![](https://images-cdn.trtworld.com/trtafricahau/21532341_0-0-6500-4429.jpeg)
Halin gararamba
An raba fiye da mutum 700,000 daga gidajensu a birnin a baki daya watan Janairu, in ji Hukumar Abinci ta Duniya.
Ga wadanda suka saura a garin kuwa, to birnin ya zame musu filin yaƙi. Motocin da aka ƙoƙƙona a kan tituna da gine-gine da aka lalata suna tuna musu da matsanancin tsoro da firgicin musayar wutar da aka sha fama da shi a baya bayan nan.
Ƙungiyar Agaji ta Red Cross tana ta taimaka wa hukumomi wajen tattara gawarwakin mutanen da aka kashe a lokacin yaƙin.
Babu na'urorin sanyi na adana gawarwaki a mutuware saboda rashin wuta. Myriam Favier, shugabar ƙungiyar Red Cross ta tawagar da aka tura Goma, ta kira hakan "aikin gaggawa" don gano gawarwaki.
An dakatar da muhimman ayyukan agaji a filin jirgin saman birnin, inda 'yan tawaye suka yi wa ƙawanya. Ofishin jinƙai na MDD ya ce rayuwar dubban mutane ta ta'allaƙa ne a kan filin jirgin saman da aka sake buɗe shi saboda gudun samun jinkiri.
"An ta'allaƙa a kan filin jirgin saman Goma don samun abubuwan rayuwa. Idan babu shi to ko kwashe wadanda suka samu munanan raunuka da isar da kayayyakin jinya, da karbar kayan agaji ba za su yiwuwa ba," in ji jami'in kula da ayyukan jinƙai na MDD a Congo, Bruno Lemarquis a cikin wata sanarwa.
![](https://images-cdn.trtworld.com/trtafricahau/21532391_0-0-5500-3665.jpeg)
Barazana ga fannin lafiya
Hukumomin lafiya sun yi gargadin karuwar barazanar barkewar cututtuka, da suka hada da kwalara da ƙyanda da kuma Mpox, saboda ƙaurar jama'a da rashin tsaftataccen ruwa.
A cewar kungiyar agaji ta duniya ActionAid, daruruwan mazauna yankin kuma suna fama da yunwa saboda tashin farashin kayan abinci.
Farashin kayan masarufi kamar fulawa da mai ya ninka fiye da sau biyu, kuma iyalai da yawa suna rayuwa ba tare da samun abinci ba.
“Komai ya yi tsada, a da muna sayen bokitin shinkafa a kan dala 20, yanzu ya kai akalla dala 23. Haka kuma farashin manyan kwalaben ruwan sha ya rubanya daga dala 1 zuwa dala 2 kowanne,” in ji wani dan agaji na kungiyar ActionAid a garin Goma.
Kungiyar agajin ta ce fadan ya katse hanyoyin zuwa yankunan da ke yankin wadanda ke samar da abinci ga Goma, lamarin da ya haifar da karanci da hauhawar farashin kayayyaki.
“Tashin farashin zai sa abinci a kasuwannin Goma ya sake fin ƙarfin iyalai da yawa, musamman waɗanda suka yi gudun hijira daga gidajensu kuma ba su da komai,” in ji Yakubu Mohammed Saani, Daraktan ActionAid na ƙasa.
![](https://images-cdn.trtworld.com/trtafricahau/21532393_0-0-6498-4368.jpeg)
Lamarin na yi wa mata tsanani
Shirin MDD na adawa da cin zarafi a lokutan yaƙi, wata cibiyar sadarwa ta kungiyoyi 26, ta ce cin zarafi ya zama ruwan dare a Goma.
A wajen birnin da aka yi wa kaca-kaca, fararen hula sun ba da rahoton cin zarafin mata da dama da wasu mutane dauke da makamai suke yi, a cewar Rediyo Okapi, tashar da ke karkashin tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya.
Goma has also seen a surge in other crimes, including carjackings and looting of warehouses belonging to humanitarian agencies.
Gamayyar kungiyoyin 'yan tawaye da ake kira Alliance Fleuve Congo sun karfafa ikon birnin bayan ayyana yarjejeniyar tsagaita wuta.
Yarjejeniyar tsagaita wuta ta bai daya da 'yan tawayen suka ayyana ta kasa tabbata, kuma tuni Kinshasa ta sha alwashin ƙwato birnin da ke da mutane sama da miliyan guda.
An shirya za a yi tattaunawar manyan jami'an tsaro a ranar 7-8 ga watan Fabrairu a birnin Dar es Salaam na gabar tekun Tanzaniya.
Ana sa ran shugaban kasar Congo Felix Tshisekedi da takwaransa na Rwanda Paul Kagame za su hallarci tattaunawar.
Masu lura da al'amura sun ce lokaci na ko-ta-kwana ya gabato, suna masu gargadin cewa karuwar tashe-tashen hankula na iya haifar da yaƙin yanki.